Chapter 47

1.3K 52 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

*page 46~47*

――――Kai tsaye site d'inshi ya nufa, bai wata wata ba, ya shige bathroom yana sakar ma kanshi shower, niko kam lokacin ina kitchen ina fama da girki, don haka bansan ya dawo ba, ya jima kafun ya futo ya shirya cikin wani white shirt da black trouser, bisa gado ya lullube kanshi cikin blanket, lokacin da ko ina na jikinsa ke amsa mishi da ciwo, yana sauke wani numfashi mai cike da wahala.


――Bakaramin tsorata mahaifin basma yayie ba, lokacin da yaga d'iyarsa, mamaki sosai yayie, yarinyan da yasan tana india tana fama da karatun ta, mai ya dawo da ita kasan nan, sai daya ga sakon da yake jakan ma, kallon matar nashi kawai yake, wanda sai ayau yake ganin gaskiyanta, da ake rigima da ita, kan al-adar daya tsara ma yeyen nashi, na ganin karshen boko, kafun ya aurad da yeyen nashi, itama tasan yanxu za'a yarda da ita, musamman mahaifiyar su basman dake fafa da boko, sukai sallama da police d'in tana basu address d'in gidan, koda zasu kwaso mata sauran kayanta da suka rage, ya rasa tunanin dazai yie game da lamarin, idan har zata iya bude baki ta roki saurayi yai sex da ita, to tabbas aure take so.

   Neekam 2pm shine lokacin dana futo don zuwa makaranta, sanda naga motocin wajen sunmin yawa a gun, sai da nayi d'an mamaki, kafun na d'an basar, don nasan yau ranane da yake dad'ewa a wajen a'iki, naja motana ina tafiya makaranta.

    Na rika kaiwa ina dawowa a tsakar falon, tun sanda na idda sallan isha'i, ko abinci na kasa ci, ganin har 9pm yau be shigo ba, tare dasa kunni ko zanji horn d'in mota, amman shiru, kona jie sai inji gate d'in makota aka bud'e, wani tunanin ya fad'o mun arai, kodai ya dawo ne ban saniba, da sauri na nufi site d'inshi ina nufa bedroom, na d'aga cotton d'in tare da sallama, hangoshi nayi gaba d'aya ya rufe kanshi da blanket, na karisa da sauri ina mamakin sanda ya shigo gidan,,,,

    yaye blanket d'in nayi, na zaro ido sanda nakai hannuna saman kanshi, wani hucin zafi na tashi, a hankali nake furta kalman,,,,,

    ya salam, na zauna kusa dashi, ina dad'a kai hannuna saman wuyanshi, ya d'an motsa yana bude idonshi a hankali, tare da bina da kallo, cike da damuwa, nake fad'in,,,,

    yaya majeed baka da lfy sosai haka, yunkurawa yayi yana mikewa zaune, cikin wani walallan murya yake fad'in,,,,,,

   am fine, ya fad'i,hakan yana ture blanket d'in,daga jikinsa, nai saurin fad'in,,,,

   no yhu are not, kaji jikinka da zafi sosai, wani murmushin yake yayi, yana kuma fad'in,,,,,

   karki damu, anyi sallah magrib, cike da tausayawa nake fad'in,,,,,

   eh tun d'azu, yanxu kusan 9pm ne, da sauri naga ya kuma yunkurawa yana mike tsaye da fad'in,,,,

   oh my god, ya wuce bayi cikin sauri, sauke wani ajiyar zuciya nayi, tare da shiga damuwa, ganin yanayin jikin nasa, dagani, yana jin jikin sosai,,,,,

  na mike tare da shimfd'a dadduma, anan wajen sallah, sannan na futa zuwan site d'ina, abinci na d'ibo tare da dauko mai drink, na dawo site d'inshi,,,,,,

   sallah na sameshi yana yie, na ije kayan abincin ina zama, tare da zuba uban tagumi, har ya idar  ban saniba,,,,,

   ya jima bisa dadduman yana gode ma Allah daya kubutar dashi daga shari irin na basma, tare da kara neman tsari  akan duk wani abin sharri, bashi kad'ai ba, har iyalansa, da sauran al-umman musulmai baki d'aya,,,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now