🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 73*
――――Na futo wanka sanye da wata tattausar rigan wanka, wanda na kulle ta gaba da design belt dinshi, rigan kuma ta tsaya mun dai dai gwiwa, gaba daya set din kayan wankan a saudiya na siyosu, inajin dadin sasu, musamman karamin towel din da nakan yie turban dashi, wanda ke sauri tsane mun ruwan gashina,,,
sai dai yau tun a bayi na nema na rasa, don haka na futo ina bincika trolley dina, tunanina yaya majeed ya manta bai dakko mun dashi ba, sosai nake dubawa ban ganshi ba, muryansa naji daga falo yana fadin,,,
soyayya nah, kina neman wani abu ne, shiru na danyi, kafun in magana ya rigani da fadin,,,
kixo kie amsa a nan, da dan mamaki na futa zuwa falon,,,
daga bakin kofan bedroom din na tsaya ina binsa da kallo, shima nie yake kallo da wani smiling yake daga mun towel din sama, yana fadin,,,
zoki amsa, karisowa nayi ina mika hannu zan ansa, kawai saiji nayi ya jawo hannun nawa, yana mun masauki kan jikinsa, lokacin da yake zagayo da hannayensa ta saman cikina, na zaro ido ina kallonsa, tare da fadin,,,
yaya majeed plss ka bani, yai yer murmushi mai sauti, yana daga towel din a hannunsa can sama, da fadin,,,
kie amsa in kina so, ganin zai bata mum lokaci, yasa na fara kokarin kamowa, yana dada sama dashi, tare da wala wala da hannun, niko sai mika hannu nakeyi, inaso in mike amman ya matseni da dayan hannunsa a jikinsa, dariya abin ya soma bani, lokacin da dukkan mu muka soma dan dariya, inason in kamo, shi kuma yana kaudawa, muka maida abin wasa, inyayi nan da hannun ni kuma nayi nan, ina faman fadin,,,
yaya majeed plsss ka ban, dai dai nan suka iso wajen, tana tafe itace gaba gaba, dama ita already ta shirya, anci gayu, da wani classy pencil shoe mai tsinin gaske, cokal cokal, take hawa stairs din wajen, rike da wani katon flask na ruwan zafi, lokacin da sister kausar ke tafe a bayanta da wani dan basket mai dauke da kayan breakfast din,,,
ita ta fara kutso kai ciki ko sallama babu, dama kofan a bude yake, mutuwar tsaye tayi, dai dai sanda ni kuma nake dada mannewa a jikinsa, da gashina dake yarfan ruwa, kwance a bayana, ina kai hannuna zan amsa towel din, shi ya fara lura da shigowan ta, tun sanda ta daga cotton, niko sai da naji karan tsinin takalmi, nayi saurin kai dubana wajen, dai dai sanda sister kausar ta shigo da sallama, da sauri ta juya ita zata futa, ya dan sassauta rikon da yayi mun, yana fadin,,,sisters ku shigo mana, ke kausar dawo, ba musu kai a kasa ta juyo, tana tafiya cikin sanyi, sanda ta iso inda Amal ke tsaye ta zuba mana idanu, dan bangajanta tayi, wanda ya dan dawo da ita hayyacinta suna samun waje suka zauna, tana bin jikina, tun daga kan kafafuna har zuwa gashin kaina da yake a jike, sister kausar na ije kayan dake hannunta, take gaishesa, nima muka gaisa inata kokarin kwace kaina, kawai sai gani nayi ya kuma rukoni, yana kama gashina tare da fara goge mun da towel din, yana fadin,,,
soyayya nah ki tsaya mana, kinsan wannan duty nane, kunyace ta kamani, ina dan turesa, sanda sister kausar ke dada yin kasa da kanta, tana satan kallon inda Amal take, ta kafemu da ido ko kiftawa, da tunanin mafarki takeyi ko mene, ita dai sister kausar sai yanxu ta gane plan din, hmmm lallai brothern su sai a barshi, cigaba nayi da janye jikina, ya rukoni da kyau sanda yake sauke towel din daga kaina da kallona so serious yake fadin,,,