Chapter 83

2.6K 118 19
                                    

 
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W @H@L@H?~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕


*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*



_*mamansadiq, mrs Dawud and mom khadeeja:Baxan kare rubutu ba, ba tare dana kira sunan kuba, hakika a duk sanda naga comment dinku, nakan jie kaman thousand peoples ne sukai mun, bani kadai ba, nasan writers da dama suna jin dadin comment dinku, don haka muna godiya.....taku meemartjj*_

   _*members na so ko wahala, ku,sani bani da bakin magana, a gaskiya ina yinku over and over, baku kadai ba harda sauran groups  din, ina yinku irin much luv din nan , kuma nagode da wannan tafiya da kuka bini mu kayi a book din so ko wahala, fatan alkhairi.*_

   _lashminzy:ina tayaki murnan kammala novel dinki, *Rudani* tare da_
  _hafnan: *fatalwan mijina* Allah ka bamu iko rubuta alkhairi, Amin, much congrats._

  _*bari namiko gaisuwa nah wajen boss dina kafun na wuce wato.....*_
_*jamila umar Janaf, keta daban dince, saboda kina da sunan ta daban din a rayuwa nah.*_

     ~*Limahbell tawan ta kaina, ina yinki kawatah*~




_LAST PAGE_ *83*

  ――――Sister Amal ina wuni, ta zuba mun ido, kaman ba xata amsa ba, gandirebance ta daka mata tsawa da fadin, ta karisa ta zauna mana, ba shiri taxo tana zama a kujeran da yake facing dina da fadin,,,

lfylau, ina mummy take?jiki a sanyaye nake fadin,,,

  ammm sunje umara da daddy, amman tace ince miki tana dawowa zata xo, na mika mata jakar ina fadin,,,

  gashi tace akawo miki, amsa tayi sanda take budewa, ta zaro wani packet din chocolate da murmushi a fuskanta, kafun kwalla su cika idanunta tana fadin,,,

  Allah sarki mummy na, my favorite chocolate, ta numfasa, sanda tayi kokarin maida kwallanta da fadin,,,

  nagode, nasan ba duka kayan bane mummy ta bada akawo mun, thank u sist, ta fadi hakan tana wani mammaxewa, amman maganan gaskiya daurewa kawai takeyi, hawaye nah suka kasa boyuwa, sanda nake binta da kallo da tunanin rayuwa kenan, classy Amal din nan ne a cikin wannan suturar da muhalli, ta dukar da kanta tana dan wasa da hannun paper bag din dana zubo kayan, tana fadin,,,

  zan tafi, nagode da ziyara, da hawaye da suka wanke mun fuska nake fadin,,,

  kin wuce haka a wajena, nayi kewarki yer uwatah, sister Amal nasan cewa ni ba best sister dinki bane, amman kie sani nie meenal ina sonki, matsayin ki na yaya tah da muka tashi gida daya, a dan razane ta dago da mamaki tana kallona, kafun murya na rawa take fadin,,,

  nie Amal kike so, bayan nie ban taba miki wani abu na kirki ba, ina kuka da tausayin halin da take ciki a yanxun, nake cigaba da fadin,,,

  yess sister Amal, kinsan menene, lokacin da muke gida, bani da farin cikin daya wuce in kalli site din bed dinki a bedroom dinmu, in ganki kwance, ko kina danna waya, duk da baxa muyi magana ba, amman indai baki a dakin sai inji wani iri, inason kallonki kina shiryawa cikin classy dresing dinki, kuma ina enjoying a duk lokacin daxan ce miki kinyi kyau ki amsa mun da murmushi, ina sonki saboda ke yer uwa tace, plsss kie dawo gida muyi rayuwan farin ciki, bana son ina ganinki cikin wannan rayuwan, runtse idanu kawai tayi tana saka sabon kuka, kuka kawai takeyi, mai cike da nadaman rayuwa, da raya,,,

  tabbas haka ne, zata hantareta, zata mata tsawa, amman magana daya na kirki daxai hadasu ta rika blushing tana murna kenan, za'a siya mata kaya, ita ba'a siya mata ba, amman a duk lokacin da zata saka kayan tana fara'a zata rika zuzuta kyaun da tayi, indai tayi sabon dinki, to meenal ce ke fara fadin kayan sun mata kyau, to meye dalilin daxai sa ta kyareta, tasa hassada da kyashi a rayuwar yer uwa irin wannan, kaiconta, wani irin nadama da kunya suka lullubeta, tana kuka cike daban tausayi, kanta a kasa, nima kukan nakeyi, gandireban na tsaye kawai tana kallon mu, kafun na mike ina share hawayena, da saba maamaa a kafada nake fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora