Chapter 67

2.8K 92 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W @H@L@H?~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 67*

―――― Haka ya cigaba da takawa cikin dakin cike da natsuwa, yana cigaba da bin dakin da kallo, ba abun da yake furtawa face kalman,,,


masha Allah, ya isa wajen side drower, yan bin wani dan design frame mai kyau da kallo, wanda yake dauke da hotan mu, mu biyu, yayi kyau sosai, ya tsuguna yana shafa frame din, tare da dan murmushi, wanda har saida yayi sanadiyar futowan kyawawan hakoransa,,,

mikewa yayi sanda yaga wani yer red flower rose, mai dauke da green din stick, kasanshi kuma wani littafine kaman album kaman magazine, ya nisa lokacin daya daga flower rose din, tare da dago littafin, dake dauke da hardcover, zanen wasu flowers ne masu matukar kyau, da heart, a jikin front cover din, milk ne sai akayi rubutun da red, an rubuta,,,


_once upon a time_ budewa ya fara yie cikin natsuwa, sanda ya fara karo da ratsatstsun kalaman soyayya, sunan meenal da A/majeed kawai kike gani, abin ya burgeshi sosai, don wani dan medium magazine ne na musamman, ya bude next page, inda ya rika ganin hotun nan mu, nacan da, ko wanne a kasa sai ayi dan summary na labarin rayuwan mu,,,


haka ya cigaba da budewa, har yaxo wajen hotunan su na yanxu, dana bikin su, ko ina da dan short labari, ya bude last page, inda page din farko nashine shi daya, hotan da nike matukar so ne, sanye cikin kayan yen sandan, hotan dana fara karo da fuskansa, da wayauna, sai dayan page din, hotana nane sanye cikin hijjab din hadda a motan, wanda shine yayi mun, randa ya bani kyautar motan, ya zuba ma hotan idanu, wanda yayi kyau kaman ba a waya akai hoton ba, ya rufe magazine yana zuba ma cover din baya idanu, wanda ke daukr da hoton mu ni dashi, ina sanye cikin lafaya ranan da za'a kawoni gidan nan, a kasa an kara rubuta sunan mu, da wasu kalamai masu sanyaya zuciya,,,


yai dan murmushi lokacin da yakai magazine din wajen kirjisa yana mannewa, tare da sakin ajiyar zuciya, jin soyayya na yake yana ratsa ko ina na jikinsa, ya dago flower rose din tare da kaiwa bakinsa yai kissing, maidawa yayi ya ijiye, lokacin daya juyo inda nake tsaye, ya tako cikin takun sanyi har inda nake,,,,

da sauri na juya mishi baya, lokacin da nake jin bugun zuciyana kaman zai fasa kirjina ya futo, jikin sanyi naji ya daura hannayensa saman kafaduna, wanda suke bayyane a waje, na kuma runtse idanu, sanda yake jiyowa dani na fuskan ceshi,,,

ya salam, tsarki ya tabbata ga Allah, shine kalman da yake maimaitawa cikim zuciyarsa, yasa hannunsa yana sauke nawan hannun dana kare kijina dashi, tare da zuba ma wajen idanu,,,

ina sanye da wata slim pich night wear, hannun ta dan karamine, amman up shoulder ne, don haka hannayen na bisa damtsen hannuna, ya tafi tare da wuyan rigan, inda ya sauka kasa, rigan yaji breastpad, wanda ya taimaka wajen dago kirjin sama, rigan taji shape daga wajen kirji, sai kuma dai dai cibiya ta bude, inda ta tsaya zuwa sama cinya, spackling rigan kawai keyi,,,

yabi gashina da kallo wanda na murmude da wani kalan style, a farkon gashin, dai dai tsakiya kuma saina hada gashin, nayi cumbing dinshi, tare sa kamawa da wani pich din band, na saki gashin, fuskana ba komai, so fresh, sai romantic wetlips din dana sa,,,

na shafe jikina lungu da sako da mayuka da turarukan masu dadin kamshi, ya saki ajiyar zuciya lokacin da yakain hannunsa kaman zai shafa mun kai, kawai sai naga ya fasa, yana sauke gwiwansa daya kasa, ya sauke dayan ma, ya zube gwiwowinsa bisa kasa, kanshi a sama, idanunsa cikin nawa, don nima dago kai nayi lokacin da naji yasa gwiwansa bisa floor, ina binsa da kallo, tafin hannunsa ya miko mun sanda ya fara magana da dan rawa rawan murya, yana fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang