🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 69*
――――tayi kuka harta gaji, haka ta yini ta kara kwana a wajen, ko abinci taki cie, sai da taga ba dama, sannan taci wani, hankalinta a tashe yake, tare da tunanin dalilin wannan wulakancin da aka mata,,,
――safiyar ranan ko office bai wuce ba, ya biyo ta station din su sagent Nura, sanda driver ke packing, wanda ke zaune kusa da driver ya futo da sauri yana bude mishi kofa, sanye yake da army green din suit, wanda suka daukesa suka mishi kyau, masu tsadan gaske, kafanasa sanye da classy black cover, sanda indanuwasa ke sanye cikin wani black goggle,,,
ya ziro da kafansa daya, kafun ya sako dayan yana futowa daga motan, ya kara kyau iya kyau, tare da yer kiba, sumar kan nan, a kwance baki sidif, har wani haske ya kara irin na kwanciyar hankali, jin dadi da samun natsuwa, ya wuce ciki yana tafiya da takun jarumta, lokacin da wasu ke tsayuwa suna faman kamewa tare da sara mishi, shidai da hannu kawai yake amsa musu, ya wuce ciki, inda sagent Nura ya tare shi cikin saurin, suka gaisa, yana yaba masa akan a'ikin daya bashi, tare da amsan file din, da yake mika mishi, wanda ya tanadi duk wani laifin na jalila,,,
wani dan daki ya nufa, inda tun isowarshi madam dora ta iza keyar jalilah, dakine wanda haske be wadata sosai, daga wani table a tsakiyan dakin, sai kujeru guda biyu, ta both side, tana zaune duk tayi zuru zuru, ya shigo shida sagent Nura wanda ya maida kofa ya rufe ya tsaya can bakin kofan, shi kuma ya cigaba da takawa zuwa wajen table din da take zaune, bisa daya daga cikin kujerun,,,
sai da gabanta ya fadi, a zuciya tana raya, wow wannan wani irim mutum ne, gayen nan ya hadufa, sai kuma ta kauda kai don yayi mata kwarjinin da bazata iya cigaba da kallon shiba, da wani kallon harara yake binta da ido, ya dan jefa file din saman table din, kafun ya bude baki da ker yana fadin,,,
meye sunan ki?da dan yanga take fadin Jalila yola, ya zabga mata harara, sanda ya bude wayansa yana budo hotan, ya ije mata wayan gabanta da fadin,,,
kinsan wannan?gabanta ne ya wani irin fadi, lokacin da tsoro ya kamata, ko a bacci aka tasheta zata fada ko wacece, da dan in ina take fadin,,,
e,,,,eh na santa course mate dinane, kuma mun zauna daki daya, ya dauki wayansa yana kashewa tare da maidawa aljihu yake fadin,,,
good daga haka kuma sai mene, cike da dan barinkanci take fadin,,,
nothing, mun dai zauna tare, kafun daga baya tabar dakin, wani kallo yake mata, rayuwanshi ya tsani karya, ya kada kai da fadin,,,
ke zan miki mugun rashin mutunci, idan bakiyi magana ba, ya dan daga file din daya ije gabanta yana fadin,,,
wannan file din da yake dauke da dukkan laifin kine, so ki fada mun gaskiya, ko insa yarana su farfasa miki jiki da duka kafun nan, ya dan dafa table din da duka hannayensa, yana facing fuskanta so silent yake fadin,,,
tell me, har daloli nawa ya baki, da kika kaimai ita, zaro ido tayi, sai kuma tai saurin yin kasa da kanta, lokacin da kirjinta ke duka kama zai futo, kaman ta fada mishi, wata zuciyar na zugata, ke jalila in yasan wani abu kan maganan, ba zaki sha da kyau ba, don haka ta gwada barinkan cinta, maybe ta samu sa'a su dai daita, don haka ba ba bata lokaci, kai a kasa take wani lankwasa murya, tare da dan turo kirji, tana dada nanata bata san komai game da lamarin ba,,,
![](https://img.wattpad.com/cover/169954186-288-k358612.jpg)