🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 58*
――――Na sauke wani ajiya zuciya, sanda hawaye ke cigaba da zuba a idanuna, da tunani kala kala, murya can ciki nake fadin,,,
yaya majeed, me yasa za kamun haka, me yasa sai dana saba da kai, na shaku da soyayyan ka, meye laifina da baxa ka so niba, wani shashekar kukan na cigaba dayi, banda hawaye ba abun dake zuba a fuska na, kafun naja wani dogon ajiyan zuciyar, ina runtse ido tare da budewa, lokacin dana tsaya da kukan, hawaye na cigaba da kwarara mun,,,
ba abun da nake tuna sai happy moments dinmun, ina tuna lokutan da zai dawo office, bazai wuto ko ina ba, sai kitchen, wata lokacin sai dai iji ya rugumoni ta baya, yana manna mun kiss a gefen kumatu, na tuno randa zaya bani kyautan mota, nie yayi ma abin arziki, amman shi yafi farin ciki da nuna annashuwa, kawai sai,na sami kaina da sakin murmushi, har lokacin da raguwan hawayen dake zuba mini, a hankali ina kuma furta,,,
ina sonka A/majeed, plss nima ka soni mana mijina, sabon kuka kuma na saka sanda wani sashin na zuciyana ke tuna mini, son maso wani nakeyi, shine ko babban wahala,,,
na jima a wajen kafun in yanke shawaran mikewa in koma gidan mijina, wani zuciyar na raya mun, komai zafi maganinsa Allah, in sha Allah bazan yi dana sani ba, hasken motane ya kashe mun ido, dama akwai hasken farin wata gana kofan gidan da nake zaune, nasa hannu, ina rufe fuskana tare da mikewa,,,
motace mai tsada, yana tafe cikin tintet glass, banda sauti ba abun sake tashi, Nurien kenan, dan makwabcinmu, yaron ya sagarce da yawa, kullum dama sai dare yake dawowa, wani abinma don ana tsawatar mishi, bayanshi wata henesi ce, itama mai kyaun gaske take binshi a sannu, sukai hanyar street dinmu, nima na fara tafiya inda nai hanyar gida, cikin sanyin tafiya, janye da trolley dina, har motocin suka kule ma ganina.
ya kusa karisawa wajen gidan mu, dama daga namu sai nasu gidan, henesi tasha gaban motan Nurien din, ba shiri ya taka birki, don yau beyi shaye shayen nashi ba, yana cikin hankalinshi, sunyi su hudu suka futo cikin motan, cikin shiga irin ta yen ta'adda,,,
ba bata lokaci suka daka mishi tsawa ya bude mota, yana budewa suka jawoshi, wata mace itace gaba gaba, wani abu suka shaka mai, nan ya fadi kasa sumamme,,,
sauri sauri suke kokarin sakashi a mota, don cika kudirin su, na kidnaping dinshi da suka shirya, sai dai kash, mission din nasu ya tarwatse, lokacin da securities din kofan gidan mu suka, kawo mishi dauki, karan bullet kawai su kaji a kansu, nan da nan suka sakeshi nan kasa, suna komawa cikin mota tare da juya kan steery zasu koma inda suka futo,,,
daya cikin security din yabi matan da gudu, yana sakin ma tayan mota bullet, yayin da dayan kuma ya tsaya wajen Nurien din don taimaka masa,,,
lokacine karnuka suka fara barking, ga karan bullet, masu gida kowa ciki ya kulle, gogan dake zaune a falo, ya daga kanshi sama ido rufe, lokaci daya ya bude ido, yana nazarin karan bullet din, da haushin karnukan, da sauri ya mike, har yayi kofan futa, sai kuma ya dawo, bedroom ya koma, can saman drower ya jawo pistol dinshi, ya makale yana maida riga ya rufe, ya futa cikin sauri,,,
gudu suke sosai lokacin daya samu sa'an sakar ma tayan motan bullet, nan suka wani ja suna tsayawa kaman zasu kife, dai dai sanda nake karisowa wajen, naja na tsaya da wani fargaba, dukansu suka futo, hannu a sama alaman surrender, lokacin da yake nuna su da bindiga cikin tsawa yana fadin,,,
![](https://img.wattpad.com/cover/169954186-288-k358612.jpg)