🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Jinjina tah gareki mrs sambo💕mama a wajen sultan da khalil💕Allah yai ma rayuwa albarka dake da zuri'arki da yen uwa musulmai baki daya💕Amin.*
*🌸dafatan readers zasu cigaba da kasancewa dani meemaaaah,,ina muku fatan alkhari,,,har wayau plss ina fada a rika ije karatu tym din ibada da a'iyyuka masu muhimmanci,Allah kasa mu dace🌸*
*page 6*
――――A haka muka karisa kan steps din ya ciro wayansa yana mana hoto har muka isa inda zamu zauna,,na zauna ina sauke wani ajiyar zuciya tare da satan kollon inda ya A/majeed ke tsaye yana hoto da hannu da dayar kuma yana aljihu.
An soma gabatar da program,ba'a dade ba governor da mutanan sa suka iso, naga ya A/majeed ya futa ashe tare da governorn zasu shigo, har suka zo suka zauna a masaukin su na musamman, Ni'ima ta rankayo kusa da kunni na tana fadin "ashe dai governor din zai zo", nace "dama ance zai zone" tace"ehmana",nace "ok", daga haka ban sake cewa komai ba don hankalina na gun yen gidan mu in basu zoba na shiga goma ba uku ba, munfi minti goma da shigowa kafun na hango Abdul rike da wata baby daba tafi 6month ba sai kuma na hango Nuwairah falaq da aunty jidda sosai naji dadi kaman in mike inyi tsalle, suka samu waje suka zauna Nuwairah na dago mun hannu sai murmushi nake, anyi program kala kala kafun daga karshe aka kirani na futo nai speech Hannat ma tayi sannan muka shiga karban kyaututtuka, na amsa kyauta da dama, sadiya ma an bata, sannan daga bisani school ta fara ansan nata daga wurin mayan mutane, sanda aka kira dad dinmu yai speech don ka'idane da headgirl da assistant dina sai wani nata yayi speech amma wayam bashi, sai dana ji wani iri don nasan in Amal ne dad zai ije komai yaxo mata, aunty jidda ce ta futo tayi speech din kuma ta bada kyautan kudi a matsayin dad ne ya a'iko dashi daganan kuma mahaifin Hannt brr. lamido ya futo yai nashi jawabin,haka dai taro ya watse na mike na nufi gun su Abdul ina mai farin ciki.Ina rungume da yen kanni na Nuwairah da falaq yaran yar mummy aunty jidda, Abdul ya matso yana fadin "sweet sist many congrats"ina murmushi nace"tnx" na amsa khaleesat ina fadin"la Nuwairah ya akayi tai muku wayau tafi ku kyau", falaq ta kwaba fuska zatai kuka wai tafi khaleesat kyau, aunty jidda tace "to yima mutane shiru", Nuwairah na dariya tace"aunty meenal tafa tsani taji ance khaleesat ta fita kyau" sai ga sadiya taxo suka gaisa da aunty jidda tana fadin"mummy bata zoba?"nace"eh" Abdul yace "sun tafi kano ita da dad wai sister Amal tayi accident jiya"na zaro ido ina fadin"accident kuma, amma da sauki ko?" aunty jidda tace"munyi waya da mummy naku tace is just a minor accident, motan ne dai ta samu matsala"Abdul ya tabe baki nida sadiya ne muka hada baki gurin fadin"Allah dada tsarewa",kafun muje inda muka shiga raba kayan suvenier irin su memo da littafi nima aunty jidda ta zo mun da wanda tai mun tun a egypt masu kyau da tsada, sai gashi Hannah lamido har inda nake tabiyoni ta kawo mun nata, Allah sarki mu da muka saba fada kowa naji shi wani ne sai gashi ana kewar juna, muna ta amsan number harda masu kuka, tace"zanyi missing dinki meenal s Gidado ga wasu juniors can kuka suke saboda ke", nace "nima zanyi missing dinku"tace "yanzu zasu wuce gombe ne haka dai aka rabu ana kewar juna".
Motar da aka kawo ya A/majeed tazo futa nabi motan da kallo ina raya wani abu kafun muma muka dau hanyar gida a motan aunty jidda,ina kallon school dinmu ina tunanin na barta kenan na har abada ba maganan resuming holiday na gama kenan, wasu hawaye masu zafi suka zubo min ina tunanin rayuwan kenan.Shagargarin ranan aka dawo da Amal murna take sosai da ganin aunty jidda, daddy ma ya dawo yana gari, rabona da ganinsa kusan 6month kenan amman dana gaishe sa,amsawan azziki ban samu ba bare kuma yace mun ya jiki an kirani baki da lfy l, maybe ma ya manta.
Satin su aunty jidda daya suka shirya zasu wuce kd gun mahaifiyarsu(mummy)wato Hajiya umma babbar aminiyar Hajiya baba mahaifiyar su dad, daga nan zasu koma egypt, muna ta kewarsu muka rakosu har gun mota, dad ne ya futo tafe da P.a dinsa suka nufo parking space inda driver ke tsaye kofan katuwar jeep din daddy yana jiransa, dad na mutunta aunty jidda don haka har gun motar su yaxo sukai sallama tare da bama su Nuwairah kyautan hundred thousand, ya wuce gun motar sa da sauri meenal dake gefen mummy ta kwala masa kira da fadin"dad samaru zaka?",ya juyo yana fadin"yes my daughter" da sauri tai cikin gida tana fadin let me brought my vail inside,zaku kaini hanwa gidan aunty mariya" ta wuce shi kuma ya shige baya p.a da driver suna gaba suka tsaya jiran Amal.
sosai aunty jidda ke mamaki ta kalli mummy tace"wai me yasa kuka cika son Amal ne don Allah kalleta sai kace ba yer twenty four yrs ba duk kunbi kun shagwaba ta", mummy na murmushi tace "ba haka bane aunty kinsan yer fari ce sai da lallashi",aunty tace ba waninan yer fari aka sani da gintse ma fuska musamman ke dana sani da kuwaicin tsiya banyi expecting haka daga gare kiba" mummy dai murmushi take tace"to aunty za kuyi rana a hanya"ta tabe baki tana fadin "kudai gyara na fada muku,kaso naka duniya ta kishine,kuma bana jin dadin yanda take ma en uwanta musamman meenal,",dai dai lokacin da Amal ta futo da saurin ta, har kaya sai data canxa an yafo dan vail din saman gashin daya ji retoching tana musu waving tace bye bye tare da karisawa gun jeep din ta bude baya ta shige sannan driver yaja suka futa,aunty jidda na kada kai ta shiga mota da yaranta suka tafi suma muna kewarsu.Kwance nake bisa gadona ina tunanin nawa na fama,gani nayi wasa wasa watan mu uku da gama school, nai dan juyi ina fadin Allah kasa mu dace, dai dai da lokacin da Amal ta shigo da waya rike a kunninta fuskanan a bace ta nufi barayin gadonta tana zama tare da jan tsaki ta ciro wayan daga kunni ta kuma trying numbern da take kira da alama yana ringing tunda sai ya dade a kunninta sannan ta sauke wayan,can kuma ta kalli wardrobe dinta a bude ta soma mun masifan ni na taba mata kaya niko dana lura da yanayin da take,bance komai ba na taso na rufe mata, don ina iya cewa wani abun ta dokeni mummy ma in taxo ta kara mun da nata, can kuma sai ta jawo pillow ta kwanta tare da yarda wayan gefe daya bisa mattress tana fadin"shi wannan ban san mai ya dauke kanshi ba sai lokacin daya gadaman daga waya kuyi magana yake picking ko kuma yai ra'ayin calling dinka, taja tsaki" dai dai tym din da wayan ke ringing da sauri ta mike tana rarumar wayan sai kuma ta kara jan tsaki daya fi na dazu tana fadin"ashe ma wannan banxanne kai mubash baka yiba shegen rashin zuciya"ta kuma cillar da wayan tana kwanciyarta,haka wayan tai ta ringing bata dauka ba,nidai na zuba ido ina mamakin da wa'inda take rigimanta mai masoya tare da tunanin shi wannan SO ya yake don ban sanshi ba, ban kuma tunanin zan iya yinshi a rayuwata.
Yau tunda nai wanka na soma shirin zuwa samaru, don tun jiya nace ma mummy zani tace sai yau don haka da murna na nake ta shiri cikin atamfa fari da baki na mss dinmu tare da saka hijjab fari sai dan flat shoe dina fari, na futo na nufi side din mummy,mai a'ikinta hajjo ne ke fada mun ta futa,nan ido na ya raina fata don bansan ya zanyiba da transport, can na tuna ina da five hundred tun rogowan kudina na school na dakko na wuce ina jin dadi da niyyar in samu drop don nasan zan samu na dawowa a can.
Tafe nake kan street din gidan mu ina tafiya inda zai kaini babban layin da zanbi inje kan titi gashi sai anyi tafiya mai nisa mu nan wajajan mu ko taxi ba'a samu kowa motarsa yake hawa, niko bani da daman hawa wata mota ma ,yananci motocin daddy ma suna Abuja yazo da abinsa inxai koma ya tafi dashi,mummy ma nata har biyu sai na Amal da za'a mata gyara, inna futa a motar gida sai in tafiya ta kama duka gida, ba ruwan kowa sa tafiyata a abun haya.*so ko wahala?2018*
ina jiran shawarwa rinku plss.✍🏻by meemartjj💕
thanks💕