Chapter 003

2.3K 120 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*dedicated to my dear sister,,,yer mutan katsina Hajaran muhammad yusuf*












*page 003*

――――Mun sami hutu first term muka komo gida,lokacinne na samu mommy da Amal sun futa kasan zuwa egypt inda yar mummy ke aure,aiki ya kai mijinta can(aunty jidda) da yaranta biyu sai na ukun dasu mummy suka je suna,ban damu ba don nasan ko ina nan ba inda za'a tafi dani。
satin su biyu suka dawo fi'ili da kaudi sun karu gun Amal dama yanzu jae take wai ita watace tunda ta fada university ,ni kalan maganan tama ya canza tai bul bul da ita, tana wani shining,ga tamfatsetsan wayar da mummy ta canza mata a can,dad kam musamman ya dawo don tarban yer lelansa ya dauke ta suka zaga boutique kala kala ta zabo kayan da zata koma school dashi banda wanda mummy tayi mata acan。
PaQ(pass question and answer)ne a hannuna zaune bisa dadduma ina karantawa saboda jarabawan dake matsowa na weac .Amal ce kwance bisa gadonta intayi juyi nan ta juya nan lokaci lokaci kuma tana jan tsaki mummy ce ta shigo da sallama ta zauna gefen gadon Amal ta dafa kafadarta tare da kiran sunan ta cikin sanyin murya '' Amal ''fuskan ta kirne ta juyo ta zumbura baki ko amsawa bata yiba,mummy ta nisa tare da fadin''babyn dad ya kamata ace kin koma school tunda kinga tun last two weeks kuka koma,kuma zaki missing wasu lectures din my dear,ki daure ki koma kinji babyn mu''ta yunkura ta mike zaune rike da pillow tana fadin,mummy nifa na riga da nai rantsuwa bazan taba komawa school ba indai ba'a cika mun promise din da dad yayi mun ba,mummy ta dubeta da fadin yanzu Amal sai motarnan taxo zaki resuming school bana ce miki har school din zan zo in kawo miki ba,ta yamutsa fuska tana fadin,ni dai gaskiya mummy sai da new car dina zan koma na gaji da a bani left,dad dina yana senator ,nima nawa nake son na rika hawa,mummy kam wata lokacin taurin kan Amal NA damunta don ita ba'a isa a sata ba kuma ba a isa a hanata ba,abin da take so shi take yie,cikin fushi mummy ta mike tana fadin,ae gwara ki zauna ke baki ga motar baki je anyi karatun dake ba,ta wuce zata futa sai kuma ta juyo ta dan dubeni tare da fadin,ke kuma mekike?cikin sanyi nace mummy karatu nake ta juya tana fadin,in kin gama kizo ina son zan a'ike ki hanwa,nace to sanda ta gama ficewa daga dakin.
kai tsaye samaru na wuce don ya zame mun jiki duk in zanje hanwa saina biya na dauki su zarah don ban fiye son zuwa waje ni daya ba musamman ma da gidan akwai karnuka,sai dai kash tunda ga kofar gidan naci karo da kanninsu suke fada min sunje jamb class amma naki yarda don ganin yau weekend ne, sai dai shima nan na samu tabbacin hakan a gun auntyn su don haka na gaida mutan gidan harda haj.yaya wanda nasha fadan rashin zumunci da ba mayi don tace duk cikin jikokin ta mune kawai bamu damu da ita ba,ni dai na futo bayan na kare bata hakuri na nufi hanwa.
Zaune nake cikin falon aunty mariya wanda yasha gyara da sabbabin cushions,cottons da kayan electronic,kai hatta da fentin gidan a n canza sai kamshi yake kaman na wata amarya,falon yayi matukar kyau kuma ya burgeni,ina tunanin irin kudin da aka kashe banda wa'inda na gani 4month later basu yi tsufan da za'a canza ba nai shiru ina tunani ni daya a falon,Nasira yer a'ikinta ne ta katsemun tunani da fadin sannu tare da ije tray a gabana wanda yake dauke da drinks da cup,nace yauwa,aunty mariya na nan ?tace,eh tana ciki tayi baki ne,amma yanxu zata futo,nace to ,ta wuce ciki,turo kofan da akayi ne yasa ni juyowa wasu yen gayun yen matane suka shigo su uku nan falon suka zauna sun ci uban gayu daya daga ciki tana amsa waya sauke wayar kenan maryam ta futo rike da wata fantsame miyar waya a hannu tana ihu suka rungume juna ga dukkan yanda suke yi friends dinta ne na ABU,nidai kallon su kawai nake magana ma kaman baza suyiba,sannan ina mamakin ko dai biki sukeyi don tun a farfajiyar gidan na lura da yawan motocin dake gurin,ban karisa magana ba sai ga sister kausar yar maryam ne yer aunty mariya ce itama,tare da wasu yen matan tana fadin,momma ina mum?maryam ta juyo da fadin tana side din baki,sis kausar ta juyo tace,ok bara na kir.......dai dai nan aunty mariya suka futo ita da bakinta sis.kausar tai saurin fadin,yauwa mom dad yace in ce miki a kula da kayan can sosai, ta nuna barayin dinning inda aka ije wasu kwalaye da kayaiyaki,tana fadin yace akwai kayan da zasu iya fashewa,mom din ta ya mutsa fuska tana fadin ,to akai can store din baya mana a ije,tace,a'a mom gobe za'ayi amfani dashi fah,ta tabe baki tare da fadin ,to sai a kula da kyau ,cikin bakin aunty mariya ne tace ,wannan kayan dai duk bana preparation din waliman Majeed din bane ,wani yer dariya aunty mariya tayi tana fadin,aiko duk nashi ne a'ikin dad din sune,dayan ma tace lallai wannan da Majeed ya cika da ,dayar kuma ta amshe da fadin sai kace shi daya kuka mallaka,aunty mariya tai saurin fadin,a 'a ba ruwana a'ikin dad din sune don ita nine ba abun da za'ayi,da sauri sis kausar ita da maryam suke fadin,lah mom ai'kom in ya dawo zamu fada mai dad ne kawai ya shirya mishi komai,tsaki taja tana fadin,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now