🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 36~37*
――――Nayi sallama kofan falon, fuskata a rufe ina kasa-kasa da kai sbd faduwar da gabana keyi,inaji a jikina akwai abunda yake faruwa niban saniba, dukkansu su ukun na gani,na gaidasu ina kallon daddy wanda ke daddanna waya ranshi fes, uncle ibrahim ne yafara da fadin"meenal mu iyayenkine, kuma yanda kowa ke yabon halayenki, wanna ya bamu tabbacin bazaki kiyin mana biyayya ba, muna so kizama mai biyayya akoda yaushe, Insha Allah bazaki tabe ba a rayuwa, kuma baza mu taba zaba miki abun da bai dace ba, shiyasa muka daura miki aure ayau dinnan batare da saninki ko shawaran kiba" wani ras!naji a kirjina, gabana ya cigaba da fadi soo fast, na runtse ido ina nazarin wanda aka daura mun aure dashi, tare da gane dalilin daya saka aka daukeni, mukaje wajen masu furnitures a dazu", nashiga uku, anya zan iya rayuwar aure ba tare da wanda nake so ba?wannan shine abunda nake ayyanawa a cikin zuciyana, a hankali na soma furta kalmar Innalillahi wa inna'ilaihir rajiun,uncle lamido ya daura da fadin, wannan haka yake, munsan kin fito daga gidan girma, familyn da muke alfahari dashi,wato Gidado, mijine wanda zakiyi alfahari dashi, wanda ba zakiyi kukan kasance wansa mahaifi ga ye'yenki ba, ba kuma wani bane shi, face d'an uwanki A/majeed, sai da naji gaba daya kunnuwana sun amsa, ina sakin wani irin ajiyar zuciya mai cike da natsuwa,tare da fidda wani numfashi mai cike da iskan rahma, naji ya cigaba da fadin, yanda yayi ma iyayanshi biyayya, kema haka muke son ki mana biyayya, ku zama masu koyi da zaman takewar sagir da zarah, don haka muna sa ran ba zaki bamu kunya ba, mu nason daga ke har d'an uwanki kuyi hakuri da juna, ku kuma zauna lfy, Allah ya baku ikon yin hakuri da juna, yasa ma wannan aure albarka, duk aka amsa da Ameeen, yayin da nake runtse idanuna, wasu hawaye na sauka bisa kuncina, ina kuma mamakin yanda al-amarin ya kasance, wani zuciyar na raya mun, anya A/majeed dina na, kunnina ke jiye mun ya zama mijina, har lokacin na kasa fahimtar komai, uncle ibrahim ya kalli daddy yana fadin, to zafa mu wuce da y'er mu, in kana da abun cewa, sai ka fada yanxu, ya dan tabe baki, yana kallona da fadin, toh nidai ba abin da zance, sai ayi hakurin aure, Allah ya bada zaman lafiya, bana son yawan kawo kara, ayi biyayya da kyau, irin wanda mummyn ku take mun, ni kuma dana kula da ita harta girma, yau gashi har zata bar gidan, ina fatan Allah ya bani ladan, daga haka yayi shiru, uncle lamido ya girgixa kai yana murmushi, da kalaman daddy na karshe, sannan ya kalli mummy yana fadin, toh madam mun baki just 5minutes kiyi ma y'erki hudubar aure na tsakanin y'e da uwa, muna jira daga waje, daga haka suka mike suka bar falon, harda daddy da yabi bayansu,,,,,,,,,,,,
mummy ta mike zata bar falon, yayin da wasu hawaye ke cigaba da bin fuskana, ina ganin abin kaman a mafarki, wai nie meenal, matar A/majeed, to wa Amal ta aura?mubash, shine amsan da zuciyana ta bani, don tabbas na gashi sanda muka dawo wajen furnitures dinnan, shida abokanansa tare da Amal din, itama da kawayenta, suna shan hotuna, amman lokacin saiya shige mun, na kasa ganeshi, sai yanxu fa dana tunano, aunty jidda ta katsemun tunani da fadin, sa'adah ina kuma zaki, inace fada akace ki mata, ko ba kiga barin miki gida za tayi ba, mummy ta dan tabe baki tare da fadin, wani fada kuma, taje kawai Allah ya bada zaman lfy, aunty jidda tace, kinji na rantse sai kinyi ma yariyan nan, fadan da duk uwa ta gari take ma y'erta yayin zuwa gidan aure, don kema kinsan saida umma tayi miki,,,,,,,,,,,,,,,
dole wannan yasa mummy ta koma ta zauna, bisa saman kujeran da nake zaune kasanshi, tana bata rai take fadin, da farko dai ni ba wani abu da zance, sai in fara da fada miki, shi gidan aure abin da yafi yawa a cikinsa hakuri, duk wani tanadi da mutum zaiyi a gidan miji, to dole sai da hakuri, don haka hakuri shine na farko dazan fara fada miki, sai biyayya ga miji, duk wani abu, indai bana sabon Allah bane, yace kiyi, to kiyishi ba bata lokaci, a kula da hakkokin miji da kyau, sai kuma tsafta, baku taso kun ganni da kazanta ba, kunsan ban iyaba, kullum gidana cikin gyara yake, duk da tarin masu a'ikin dake gareni, amman hakanan nakan tashi da kaina, wani lokacin in gyara gidana, sanin kanki ne wannan hakan yake, don haka mutum ya kula da harkan tsafta, girkinki tsafta, suturanki tsafta, muhallinki kullum ya kasance tsaf tsaf, tare da fidda kamshin mai sanyi, a ko wani lokaci, wannan wani babban sirri ne a gidan aure, sai barayin girki, nasan baku da matsala a wannan site din, don lokaci lokaci muna shiga kitchen tare daku, musamman ma ke, dana kanga kin dage a kitchen indan masu a'iki na girki, tom nasan dai ba wata matsala, sai yer wanda ba'a rasa ba, don haka ina mai fada miki wannan, karki sake, karki yadda, kibar gidanki ba abinci, indai da wadatan hakan, to kullum ya kasance food is ready, ina fada miki wannan ne, cos yunwa tana maida mutum mafadaci, komin kirkinsa kuwa, sai last, tarbiyan yara, naji tayi dan shiru,,,,,,,,,,,,