🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to sister Nafeesa muhammad suraj*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 15~16*
――――Dani kike magana, na daga kai ina fadin, eh, ya dan daga wayan yana kare mata kallo, yana tuna irin wannan halin na masa lokacin graduation dimu a school, sannan ya kalleni yana fadin, ya zanyi insan nakine don banga sanda kika yarda wayan ba, nai shiru ina tunanin kalaman sa, wato karya zan mushi kenan, na kuma hada fuska ina fadin, eh a'i nice na yarda wayan, shiyasa nace nawa ne, shima fuska ya hada, yana gyara tsayuwa yace, nasan haka, amma ina son insan inda gaske wayan kine, bana son naba wani ko wata wayar daba nashiba, nayi shiru ina mamakin yanda yake neman maida ni thief din karfi da yaji, na soma tunanin ko dai ya raina kalan dresing din dana yine, na tuna maganan su sameera dasu kace, daga yanayin dresing dinki ma yana iya raina miki wayyo, na dan dukar da kaina ina bin jikina da kallo tare da dagowa,raina yadan baci nake fadin, nawa ne na fada maka,ni ban taba cewa abun wani nawa bane, kuma ma bazan taba in sha Allah, na karisa maganan kaman zan kuka,,,,,,
maimakon ya saki fuska sai naga ya kuma daurewa yana fadin, i don't care, abun dana sani shine sai na tabbatar da mai wayan zan bada, yanxu ki fadamun contact guda 3dake cikin phonebook din wayan, ni kuma na duba naga hakanne, zan baki abinki, if not kuma,yayi wani murmushi yana kuma zuba min ido, na kasa kallonsa don ya kureni, bansan mutum daya na contact dinta ba bare uku, gashi ko nayi ninyar yin tsiwa wannan idanun nasa daya tsareni dasu yakesa nake kasawa,na dukad da kaina ina wasa da yen dogayen yatsun hannuna,,,,,,
shiruna yayi yawa, kawai sai gani nayi ya hada wayar da nashi ya zuba a aljihu tare da dan juyawa baya yana daukan roban swan din daya ije bisa booth din motan, ya nufi inda ya ije tasa black optima da yake son hawa, na bisa da kallo ina mamakin acting dinsa, sanda naga yana kokarin bude motan da sauri na soma tuno irin masifan da kafayat zata mun na koma hostel ba wayanta, basan lokacin da nake fadin, yaya majeed plss don Allah ka bani wayan ba nawa bane, na karisa maganan da idona da sukai rau rau da kwalla,,,,,ya dan saki murmushi yana sakin handle din motan, sannan ya jiyo fuskansa ba yabo ba fallasa, ya iso kusa da inda nake tsaye yana fadin, me kikace, is like u say something, nai danyi ajiyar zuciya da fadin, wayan ba nawa ban.....yai saurin katseni da fadin, no bashi ba ina son ki maimaita the same statement din daki kayi dazun kafun in baki wayan, ya karisa maganan yana ciro wayan a aljuhunsa, nai danyi shiru kafun nace, cewa nayi yaya majeed don Allah ka bani wayan ba nawa bane, na karisa maganan so silent, naga ya saki wani murmushin tare da matsowa gab da inda nake yana kallona, tuni naji wata sabuwar faduwan gaba, kirjina ya rika bugawa sosai, yana wasa da wayan da duka hannunsa naji yana magana cikin wata murya da ban taba jin yai magana da itaba yana fadin, meenal ashe kin sanni, nai saurin dagowa muka hada ido,da sauri na sauke nawa idannun ganin irin kallon da yake mun sun banbanta da wanda yasha mun a baya, na dukad da kaina yayin da zuciyata ta cigaba da bugawa ina runtse ido tare da budesu ina jin wani irin sonsa,nai dauriyan fisage wayar dake hannusa tare da ja da baya saboda tsayuwan nashi bashi da karshe,,,,,
ya dan zaro ido yana fadin, ke nace ki amsa ne, hankalina na mayar kan waya ina kokarin kunnawa, na bude ina ganin hoton wallpaper dake jikin screen din nata, nai murmushin karfin hali da fadin, yaya majeed Allah wayan ne dana yarda, yana murmushi shima yace, na sanie, ya ja hannu riganshi yana kallon wrist watch din dake makele a hannunsa yake fadin,kinga kin bata mun lokaci, a nan kike karatu, nace, eh, yace ina shigowa school din sosai ya bama haduwa?nai shiru ina tunanin amsan dazan bashi kafun nace, kuma a hostel nake zaune, yace,maybe ba kyason zuwa class ne ko?da sauri nace, ni ina shiga class sosai, yace, me kike karanta, nace, micro biology, yace, good, yanxu class zaki ko ina?nace class zanje muna da lecture ne, cike da dan jin dadi yake fadin, good, maza ki tafi ayi karatu da kyau banda wasa, nace, to,har zan tafi sai kuma ya saka hannu a aljihu yana fadin, oh bari na baki na break kisai sweet ko chocolate koh?abun ya bani dariya,bansa lokacin dana fara dariya ba ina fadin, na break kuma?ya rika bina da dan kallo ina dariya, tare da ciro hannunsa empty daga ajihu yake fadin,, hmm irin kin girma yanxu kin wuce na break, to muje mota in baki na handout shine dai dai class dinki a yanxu ko?na daga kai sama alaman eh bayan na tsaya da dariya da nake yie, ina murmushi, yace, to muje, tare muka jera har gurin motan sa,,,,,,,