🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to mum and dad*
*pls don Allah a rika ije karatu lokutan ibada, makaranta, da a'yyuka masu muhimmanci,,,tnx*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 29~30*
――――Hankalinta yayi matukar tashi, lokacin data zo taga halin da nake ciki, gashi bata taba gani wani a irin condition dinnan ba, don haka ko tabani ta kasa yi, ta zaro ido tare da bude baki, tasa hannunta, tana toshe bakinta, ta rika yin baya baya, tunanin tama, bana numfashi kwata kwata, da gudu ta fuce, fuskanta dauke da tashin hankali, ganinta kawai sukayi ta futa hankali tashe, duk kallo ya dawo kanta, daka ganta kasan ba lfy, aunty salma ta tareta tana tambayarta abin dake faruwa, tama kasa magana, sai nuna inda ta futo take da hannu, tana haki, kowa na tambayarta, hawayene suka wanke mata fuska, lokacin da kuka keson kwace mata, bai tsaya jiran tace wani abuba, yayi hanyar inda ta futo, don a idonshi ta shiga, kuma ta futo, yasan dai ba lfy,,,,,,,,,
bai auneba, sai ganinshi yayi a cikin falo, ya karisa har bedroom, shi kanshi ya tsorata, sanda ya ganni kwance ba inda nawa ke motsi, ya duka yana dagoni, tare da tallafo fuskana, yana fadin, meenal!meenal!amman shiru, da sauri ya jawo wani goran ruwa yana shafamun, tare sa juye ruwan duka a jikin, amman ko gezau, ya kuma rudewa da lamarin, daukana yayi cak yana futa dani daga dakin,,,,,,,,,,,
dai sai sanda wasu en uwa ke shigowa, kowa ya saka salati, harda su zarah da hankali ya tashi, yayi dani gurin mota hankali a matukar tashe, su ya sagir ma dake wajen, sai da suka girgiza, don a sume nake gau, ya shimfi deni a bayan mota, ya koma gaba yana shiga, sister kausar ma ta bude dayan barayin ta shiga, yaja motan suka fuce, sanda su mummy suka futo daga sashin haj. ana tafiyan manya mata, ta hangi yaya majeed dauke dani, ana fadin, a'i meenal ce, cikin daga murya da zaro ido take fadin, meenal, aka cemata eh, hankali tashe take tambayar meya faru, aunty mariya na fadin, ta dauki mota kawai ta biyo bayanmu, ta dan dake tana nufa gurin motan nata, sai da aunty salma tace, aunty ga wayanki nan da key din, da kika amsa gun driver, ta dan juyo, cike da waskewa tana fadin, oh, na mantafa, ta miko mata wayan da key, sai ta amsa waya tana juyawa, akace, baki amshi key dinba, ta kuma juyowa da dan tsaki ta amsan key din, ana fadin, zama ta iya driving din kuwa, ina driver ne, aunty salma tace, bari kawai na amshi key din na jamu, aunty mariya na fadin, yawwa hakan yayi, muma yanxu zamu boyo bayanku, aunty salma ta amsa key din, suna biyo bayanmu a motan mummy, haj.kam fadi take, oh ni dije, na bani ban lallace ba, kar inga bakin biki, aka rika tausata da bata hakuri, kafun kuma ta fara zagawa bayi,,,,,,,,,,,,,,
emergency aka wuce dani da sauri, yana rike dani, aka faramun duk abun daya dace, tare da daura ni akan medication, na sosai, har lokacin, ban san inda kaina yake ba, sai dai numfashina ya dawo normal, na ji jiki sosai,,,,,,,,,
yaya majeed kuwa ya kasa tsaye ya kasa zaune, hankalinshi a tashe yake, duk wani bill shi yake biya, su mummy sun iso suna zaune a reception, su da sister kausar dake zaune, tare da rika binshi da kallon mamakin irin tashin hankalin, data gani a tare dashi, tana kallon yanda idanuwansa suka canxa, a duk lokacin da yake cikin wani hali na bacin rai, da tashin hankali, baban likitan ya futo suka jera tare da yaya majeed, a office suka zauna yana mishi bayanin, su kwantar da hankalinsu, nan da yen wau hours ne zan dawo hayyacina, in Allah ya yarda, matsalan da aka samu, ciwon ne, na dade inayi ba'a zo hospital ba, amman zan dawo normal nan bada jimawa ba, don sunyi iya kokarinsu, da wannan ya samu hankalinshi ya dan kwanta, har yazo yai masu mummy bayani, suma hankalinsu ya dan kwanta, mummy na fadan haka nake, inta ciwo, baxan yi magana ba, sai yaxo karshe nabar mutane da wahala da fargaba, haka dai tayi ta yen fadace fadacenta, aunty salma na bata hakuri,,,,,,,,
![](https://img.wattpad.com/cover/169954186-288-k358612.jpg)