Chapter 33

1.6K 111 12
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to mum and dad* 

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 32~33*

――――Da sauri ya futo, jin haushin karen yasan ba lfy, police dog dinshi ne, daya ije anan site dinsa, yayi ta bayan swimming pool din, inda yake cigaba da jiyo haushin karen,,,,,,,,,,,,

A baki swimming pool yaga karen tsugune, yana ganisa ya mike, yana kuma rage sautin haushinsa, hijjab bina ya fara hangowa, dake yawo a saman ruwa, cike da mamaki yayo barayin da hijjab din yake, yana mamakin wanda ya fada ruwan, ya hango bakin gashin dake yawo ta gefen ruwa, da sauri ya tsuguna, yana sa hannunsa ya riko gashina da kyau, na yo sama tare da zubar da ruwan da ya cika mun baki, ina sakin wani ajiyar zuciya, ya jawo hannuna yana taimaka mun sosai, na futo cikin ruwan, ina zaune bakin swimming pool din, yayin da har lokacin kafafuna ke cikin ruwan, kaina a kasa ina faman nishi sama sama, ya tsuguna dafe da hannayensa a saman gwinwansa, ya zuba mun idanuwa, yana mamakin irin wauta ta, da abin daya kawoni ta nan bangaren, nasa hannuna ina kauda gashin daya daya rufe mun ido, ina yin baya da gashin, naji wasu cikin idona, da sauri nasa duka hannuna ina mutsike fuska, tare da son cire gashin cikin idona, har lokacin kaina a duke yake, don ni kaina kunya shirmen da nayi, yasa na kasa hada ido dashi, naji yasa hannunsa yana cire mun gashin tare da maida mun baya, yake fadin sannu ko, na runtse ido sanda naji yayi magana, a hankali kuma na bude idanun ina dagowa muka hada ido, dama nashi idon na kaina, naga ya saki wata yer dariya yana kauda kai tare da juyowa da murmushi a fuskansa yake kuma fadin, sorry fah, na karisa futo da kafafuna daga cikin ruwan, tare da hada fuska saboda dariyan da yake mun, ina matse gashina da ruwa ya jika, shima ya ciro mun hijjab dina, yana fadin, madam meya kawo ki site dina, na dan bata rai ina fadin, mummy ne ta a'iko nee, ya gintse dariyan da yake son yi, shima yana hada fuska yace, ta a'ikoki gun swimming pool din, ko dog din?raina ya kuma baci don nasan tsokanata yakeyi, nace, bafa nan naxo ba, gurin aunty mariya nazo?ya mike yana fadin, to meya kawo kafanki site dina, kaman zan kuka na mike nima, ina dada gyara ribbon din dana kama gashina dashi, ina fadin, to ba dogs din gidan nan nagani ba, shine naji tsoro na biyo tanan, ya dan kauda fuska yana dan dariya, dana dago kai zamu hada ido, sai ya wani kirne, ya miko mun hijjab dina, yana kwaikwayo muryana yake fadin, sai gashi nanma baki tsira ba, na amsa, yana wani bina da kallo, nai sauri kakkabe hijjab din, zansa don dama na takura, saboda kayana da suka jike, sun kamani a jiki, da sauri naji yace, ke meye haka, ba kiga jikin ki a jike yakeba, zaki kara wani, come on muje ki sanja wasu kayan, na zaro ido ina kallonsa, yace, bani zaki kalla ba, hanya zaki kalla, ya karisa maganan yana nuna hanyar wucewa da hannunsa, dole na wuce gaba  ina tafe ina tsayawa, shi kuma yana tafe a bayana, da yaga haka, naji yasa wata yer tsaki yana wucewa gaba abinshi, na bishi a baya, har ta wajen entrance din site dinshi, naga yaja birki ya tsaya, nasan yana nufin inxo in wuce ne, amman sai nayi gaba abuna, ya bini da kallo yana fadin, madam zoki wuce nanne, yanda yai maganan cikin daurewan fuska, yasa na bishi ciki,,,,,,,,,,,,,

A dan madaidacin falon na zauna kan daya daga cikin kujerun dake falon, a darare nake, naga ya shige bedroom, ya barni da tunanin badai anan zan sanja kayan ba, ya futo yana waya tare da fadin, kausar plss kixo mata da wasu kayan kawai ta canxa, yai dan shiru, sai kuma yace, eh ki kawo mata nan, bana son ta shiga cikin jama'a a hakan, daga haka ya sauke wayan, ya samu guri shima ya zauna yana facing dina, ya zuba mun ido, kaman wata tv, duk na kasa sukuni, ga kayan duk sun kamani, dama rigan, dama rigan wuyanshi yai kasa, don haka jikina ya futo sosai, nasa hijjab dina, ina dade rufe jikina da kyau, yana dan basarwa, ya kauda kai, tare kuma da dukad da kai yana danna wayansa, kaman daga sama naji yana fadin, in ban ganiba, wasu sun gani a'i, da sauri na zaro ido ina kalloshi da mamaki, naga ya wani hade rai kaman bai taba dariya ba, ina son in fada mishi, abin da yake tunani a kaina ba haka bane, amman kwarjininsa ya hanani, ina ganin kaman inna fada bazai yardaba, naji zafin kalamansa sosai, don haka a zuciye na mike ina saka hijjabina, tare da nufa hanyar futa daga falon cikin sauri, ya bini da ido kaman yace in dawo, amman wata zuciyar na raya mishi, kan nayi laifi nasan kuma nayi, amman ko sau daya ban taba yin mai maganan ba, tare da nadama akan abin dana a'ikata, don haka yaja tsaki yana maida kanshi, ya cigaba da danna waya ransa bace,,,,,,,,,,,,

garin sauri nayi wata irin tuntube dana kusa fadi dai dai bakin kofan futa, kafana d'aya ya gulle, nai wata kara sanadiyar fadi da naji zanyi, na samu da ker na dafe kofa, yayin da kafan ya rike mun, da sauri ya dago ido, lokacin da yaga ina shirin faduwa, cike da  axama ya mike, yana faman fadin, meenal! yai saurin karisowa inda nake tsaye da fadin, kina hauka ne, zaki rika tafiya yanda ranki yaso, na cije baki sanda nake runtse idanuna, ina daga kafan da ker, yayi dan tsaki, tare da riko hannuna yana fadin, zo mu koma ciki, dai dai sanda sister kausar ta iso wajan da kallon mamakin ganin yanda nake a jike sharkaf take fadin, what's going on, brother meya sameta, yayi dai dai da lokacin da ni kuma na fisge hannuna, tare da dingisawa ina isa inda sister kausar ke tsaye, ya bini da kallon mamaki, wani irin kallo na mishi da idanuna da suka ciko da kwalla ina kauda fuska, sister kausar na fadin, sister meenal meya faru?muje ciki mana, ki canxa kaya, nace, no sister kausar don Allah ki kaini wani wajen, bana feeling comfortable a cikin nan, ta dan kalleni tare da kallonsa shima, wanda ke tsaye har lokacin yana kare mun kallo, tace, brother bari na kaita site din granny ta canxa, ba mutane a can da yawa, kai kawai ya daga mata, zaya juya, sister kausar najan hannuna, muma zamu wuce, na manta da kafan dake mun zafi ina taka kafan sosai, na rufe ido ina kuma dan fadin, ah!da sauri ya kuma juyowa yana zaro ido, tare da kallon kafan dana dafa da hannu, muka hada idanu, sai kuma ya wani waske yana juyawa ya koma ciki, ta gefan ido yake kallon mu har muka futa daga falon, sister kausar na jera mun sannu tare da fadin, keda brother majeed na kasa fahimtar ku, da mamaki nake fadin, fahimta kuma, tace, bar maganan, muka shiga site din da kakansu ke zama in taxo, na sanja kayan, sannan na shiga ciki gun aunty mariya na amshi sakon, tare dasu sister kausar din, dasu maryam, muka koma nan gidan mu, sunzo gun sister in law Amal.







*****
Bai taba yarda aure zaiyiba, sai randa friends dinshi, suka zo kowa na tofa albarkacin bakinsa akan auran, suka gama daganan suka nufi gidansu Amarya, ranan su Amal ba'a zauna ba, kai sai faman rawa yake, ta taro kawayenta da yawa, suka zauna nan babban falo suna fama, kawayen Amal na zayyano event masu yawa da zasuyi, shiko gogan yace ba wanda zaije, baya kuma son wani event, da ker dai ya yarda da crossing, da abokansa suka matsa da sai anyi, kafun dai suka karkare suka tafi, bayan sun cika kawayen amarya da kudi.

Amal tayi wasu nata event din ita da'ya a gida, inda sukai ranan lalle, ranan masu lalle sosai aka kira, akayi ta lalli, hardasu sister kausar duk anan aka musu, akayi ma kowa, sannan akayi ma amarya, nima aunty jidda ta matsa ayimun nace, bana son mai yawa, ta hadamun harda ja yafi yawa, wai zaimun kyau, tunda ni farace, haka akai mun lallin ba wani mai yawa ba, amman ya tsaru, nikaina lallin yaimun kyau sosai, shagargarin ranan ne kuma sukayi arebain night, shima event din ya tsaru ba laifi, sai ranan friday da mummy ta shirya mata wani kayataccan walimah, a nan gidan mu,ranan ne kuma, ta samu daddy a upstairs, tana shirya mishi breakfast.

Da shirin futa ya futo daga bedroom, yasha malum malum, cikin sabbin kaya, mummy ta bishi da kallon mamaki tana fadin, daddyn Amal ina kuma zaka haka, ana hidman biki, ya kalleta da wani murmushi yana fadin, sa'adat kenan, zanta zama a gidane, a'i bikin gida ku ya shafa mata, cike da dan damuwa tace, naga kaman za kayi tafiya ne,yace, eh tafiya zanyi, amma in sha Allah yau zan dawo, ayimun fatan sa'a, kaman wasa tace, to Allah ya tsare ya bada sa'a, a dawo lafiya, yace, Amin, ko breakfast bai tsaya yiba,ya futa sauri sauri, ta rakashi tana mamakin inda ya nufa,,,,,,,,,,,,

ranan ansha walima, lecture na musamman da aka shirya ma Amal din, nima ina wajan waliman tare dasu zarah, don ranan suka zo, zarah da ummee anan zasu kwana, sameera ce zata koma can samaru, zuwa wannan lokacin tafiya kawai nake amman ni kadai nasan halin da nake ciki.

*sorry kudan rage daren da wannan, kyaun alkwari cikawa, tnx, taku har kullum,,,,meemarh*

so ko wahalah?
*2019*
comment&share

meemartjj💕......✍🏻

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now