Chapter 017

1.5K 91 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to late brother Tahir Aminu Aliyu, Allah yaji kanka da gafara*

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 16~17*

――――Na futo wanka na gama shiryawa ina harhada kayana dazan tafi dasu gida wannan weekend din, tun ranan alhamis wannan week din zan tafi don ranan sunday muna da walima yayen dalibai na saukan al-kur'an da za muyi wanda nake zuwa duk weekend inna koma gida, ina ta sauri don yamma ya soma yie,na debo ruwa zan goge takalmana ban sani ba na jika ma kafayat mattress inda take shiga ba nan take futa ma, ni masifan tama duk ya dameni, ta rika abu ita ganin ta girmeni wai sister na,nikam wata lokacin ko hakuri ban bata ta karici masifanta ta gama, haka yau nayi mata na hada kayana tare da daukan jakana na bar mata dakin tana fadin nayi ma ubana banxane(shiru)nidai nai tafiya ta na barta da masifarta.

A bakin gate nayi karo da Abdul ya saka ihu yana fadin oyoyo sweet sist.na, ya kariso yana fadin ABU student, nima nace, Albani student, ya studies naga kayi wani kyau ne harda kiba, yasa dariya yana fadin, duk murnan kare bording ne, nace, bording din daya amshe ka jube kafa kake murnan gamawa,yai murmushi tare da amsan mun jaka yana fadin,ah kowa nason cigaba, na kosa na fara karatun medicine na ganni matsayin doctor, muka karisa ciki ina fadin, lallai amma a'i kuna da sauran lokaci kafun ku zana final exams,yace, six month nefa kawai, nace, ba kawai bane lokacin ni ina 300level ina shirin zana first semester examination, yace, kun kusa fara jaraba kenan, nace, eh nan da 2month ne zamu fara, yace, ah dole inga kin rame, kinsan da anga kinyi rama to exams yaxo, nace, zaka sanine, bari ka fara karatun medicine din naka, zanga kalan raman da zaka yie, da haka muka isa cikin gida muna farin cikin ganin juna.

Na samu mummy ita da masu a'ikinta a kitchen, tana hada ma daddy breakfast, da yike da kanta take shirya mai komai na abinci, na karisa inda take tsaye ina fadin, mummy don Allah kudin waliman dana ce ki tambayan mun daddy in ya dawo, ta kalleni tace, ya baki ten thousand, zan baki 5k a ciki ga flower nan da komai ki diba kisa a miki snacks din da zakiyi amfani dashi, inna sakko saman dad dinku, kixo ki amsa kudin, Abdul na nan yasa mai a mashin dinsa ya kaiki inda zaki, to, kawai na iya cewa ina tunanin son kudi irin na mummy duk kudin da take dashi masu yawa, amma daddy ya bani yer 10k ta hana ni duka gashi hidman kudin da zanyi suna da yawa, bani da zabi daya wuce na amshi 5k din, na samu Abdul ya kara mun 2k, shima wani abokin dad dinmu ne yaje ma dansa visiting shine yaga Abdul din har yai masa kyautan kudi, shine ya kaini wani plaza nan kusa damu nasai yer takami plat, don nawa yawanci duk sun tsufa, sannan nasai yadin hijab din daxa musa, na dai samu na lallaba kudin har na contribution da akace mu biya na bayar,duk da abun dana bada a matsayin gidan mu kwarai yayi kadan,amma ya zanyi abun da aka ban kenan dole na bada,,,,,,

Duk wani abu na snacks masu a'ikine suka mun,,safiyar ranan na kammala komai nawa, sannan na wuce makaranta,,,,,

Anyi walima sosai inda muka sha karatu,naji dadi da naga aunty jidda tazo, duk da bata zo dasu Nuwairah saboda makaranta, amman naji dadi musamman data sa mummy dole tazo taron tare da tilasta mata dole ta bada wani abu da iyayan yara masu hali suke badawa na taimakon makaranta,gab da za'a kammala taron su sameera suka zo don haka dasu aka tashi, bayan sun tayani raba abun walima muka koma gida dasu,,,,,,

munsha hira dasu anan ne suke sanar dani bikinsu saura wata daya amma ankara 2month saboda na sameera da aka sa dana yaya baffajo, na kalli ummee ina fadin, lah duk tare za'a hada bikin, zarah tace, ehh maybe ma harda na ya .....sai kuma tayi shiru tana dukad da kai, nace nawa?ummee na dariya tace, na mutumin ta yaya sagir, nayi murmushi ina kallon sameera nace, ah sameera ke ina zamu kaiki, tayi wani dan murmushin kunya tana kallon su ummee, ummee na fadin, ah weee meenal din kike kunya, nai saurin fadin, kai ummee a'i ita ba irinku bane ba kunya, ummee tace, tana dai jin kunyan ta fada miki zata auri tsoho ne, sameera cikin fada take fadin, niba tsoho zan aura ba, ki daina kiran mun tsoho, naga ummee tasa dariya, zarah na fadin, gaskiya wulakancine irin na ummee, abokin kanin maman tane fa suka hadu a kd bikin wata cousin din sameera shine fa yaxo za'ayi dashi, ummee tace yana fa da mata, zarah tai karaf din fadin, to sai me kema Najib wata rana uku zai karo miki, tace bana ganiba, na kalli zarah nace, kaduna zata kenan, zarah tace, eh a'i ita sameera tayi mana wayau zata garin governor, sameera tace, kuma kunji dadi kuna garin mai zazzau, gashi naku mijin yara ba tsoho ba, na lura ranta yadan baci da kalaman ummee nace, a'i tsohon yafi yaron ma wata lokacin iya rike aure, zarah ta amshe da cewa, balle ma ba tsoho bane sa'an uncle bello nefa, nace, lah ashe ma ba wani babba bane, da haka muka samu sameera ta sakko, ummee na faman koda Najib dinta.


******
――Masifa take sosai ana riketa zata dakeni, saboda yau na mayar mata da bakar maganan data saba gaya mun a kullum, dama mai hakuri aka kureshi ba kyau, don haka nima tana fada ina fada, zata dakeni aka riketa ana bata hakuri, nayi shigewata daki, amma kasan zuciya na cike nake da tsoro, don a duke zata iya mun duka, kodon gabjejen jikin da take gareta,,,,,,

Ta shigo cikin hostel tana taja ta tsaya, sanye take cikin riga da wondo na blue jeans ta daura after dress a samansu ta yafa wani dan siririn gyale, tare da makale wata yer cute bag a hannu, dayan hannun kuma tana janye da trolley, taima kafayat kallon kasa da sama, sannan ta buga tsaki tana fadin, kindai bani da bala'i, haka za'a kare, cikin masifa kafayat ta dawo kanta da fadin,ke kuma banxa mai yawon gantali, sai exams yaxo sannan kike resuming school,saboda kina da masu miki follow up, har tasa kafa zata shigo dakin mu, ta juya sukai kaca kaca da juna, ta kare maganan ta da fadin, kuma daga yau sai dai kiyi masifarki da wata jalilan bani ba, don nie yanxu na cigaba nafi karfin hostel sai dai up k, yau ba gobe ba zan tattara na bar miki dakin, kici tsiyar da zaki ci, daga haka tai shigo wanta dakin,,,,,

sosai jalila tai mamakin ganina a dakin, ashe itace cikon na uku mu, ta rika bani hakuri tare da lallashi akan masifa iri na kafayat, tace, itama dalilin da yasa taki dawowa kenan sai an kama mata up k, saboda masifar kafayat ya isheta, shine sai yanxu ta dawo da aka kammala mata komai, nace, ina miki murna a'i kin huta da tashin hankali, tace, ehmana , kema kixo mu koma tare, don plat ne aka kama mun kuma ni daya ne wajen yaimun girma, nai saurin fadin, a'a haka nan zan cigaba da hakuri, kuma bana so nayi nisa da school, tace, no up k, din bayi da nisa da makaranta nan kusa nefa, ta kara da fadin, inba haka ba Allah sai cikin dare ta tayar da aljanunta ta nemi shakeki, haka take mun duk sanda muka yi fada, har suma na taba yi a hannunta, tsoro ya kamani na kasa cewa komai ina tunanin bin shawaran da jalila ta bani na inbita upk,haka ta rika fada mun mugayen mugunta irin na kafayat, don haka na tsorata sosai, daga baya nabi shawaranta, musamman da naje naga upk din babu nisa don haka muka tattara kayan mu, muka barma kafayat dakin.

*****
Zaune yake dakin haj. bahba bayan ya kammala da cin abinci, yana danna waya, kanshi kasa, kirane ya shigo dayan wayan nashi dake ije gefe daya, ya dauka yana fadin, hello sagir ka shigone?, daga can bangaren ya sagir ya amsa da fadin, eh ina site dina, yaya majeed ya mike da fadin, ok bari naxo na same ka, ya sauke wayan yana futa tare da fadin, haj. nie na wuce, haj. wanda ke daki tana sallah ta dunga fama da fadin, iyy iymmm, shidai ya fuce daga falon,,,,


a dan madaidaicin falon su ya sagir ya sameshi, kishingide jikin kujera, ya samu waje yana zama tare da daukan remote yana sanja channel din da ya sagir yasa yana kallo, ya sagir ne ya kalleshi da fadin, ya?meye labari ?yaya majeed ya dawo da hankalinshi gun ya sagir yana fadin, name fa?ya sagir ya dada gyara zama yace, nasha an samu wani labari ne akan wannan maganan, yaya majeed yai dan tsaki da fadin, kai bari kawai, dad ya matsamun akan wannan maganan, kaman wasa , yanxun ko gaishe shi nayi, sama sama yake asamun, ya sagir yace, a'i kai matsalan ka da sauki, nine kai yanda kuke da tsala tsalan yen mata a familyn dad dinku, can zanje in bincika, amman bazan taba baka shawara cikin family nan namu ba, cos duk yarane ba abun da suka iya sai shirme, yaya majeed ya kalleshi yana fadin, yara kuma?ya sagir yace, of course, they are all kid, kaga haukan da ummee take mana don zata yi aure, ita kuma waccan mara mutuncin bata iya komai ba sai futa hira, common girki inka tsare su, baxa su maka yanda ya kamata ba, yaya majeed yace, wai wakake nufi da mara mutunci?ya sagir na dan tsaki yace, wace banda zarah, duk tasa mutum cikin tunani, da sauri yaya majeed ke fadin, tunani kuma, kaman ya?ya danyi shiru, yana yen kame kame tare da tunanin abun fada, ya nisa yana fadin......

*Afwan readers naso ace page dinan yafi haka amma Allah bai nufa ba, hope zaku cigaba da kasancewa da littafin so ko wahala,,,,,,,inah muku fatan alkhairi*

so ko wahalah?
*2018*
comment&share

meemartjj💕......✍🏻

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now