🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 50~51*
――――Da gudu ta karisa sakkowa daga stairs din, taja ta tsaya tana maida numfashi tare da kara bin gidan da kallo, a hankali kuma ta cigaba da tafiya tana waige waige,hanyar wani corridor tabi inda take jiyo motsi can ciki, ta nufi wajen inda ta tsinci kanta a wani tafkeken falo, idanu ta zuba ma wani standard frame dake ije gefe daya, a hankali take furta kalman,,,
na shiga uku, mummy ina kike, ta zuba ma frame din idanu, hotan tane ita da mubash na wajen dinner da akayi a nan kanon, sunsha kyau harsun gaji suna cikin farin ciki, a zuciya take raya,,,
me yake faruwa dani, mubash kuma a maimakon bro m.... bata karisa ba ta shiga fadin,,,
no no no no, this can't happened, tana girgixa kai, tare dasa hannu tana murza idanuwanta don ta tabbatar da abin da take gani, har lokacin ba abun daya canxa, ita dai da mubash din ne, tayi dan shiru kafun kuma ta rufe idonta, tana kuma wani tunanin,,,
anya ba mafarki take yiba, ta bude idanun tana karisawa inda take jiyo motsi, ta wani corridorn tabi sai gata a wani fadeden kitchen, tsaye wajen gas cooker wata dattijuwan mata ne, daga ganin ta yarene, tasha apron a nata girki, can kuma wajen sink, yer budurwan yarinyane tana ta nata a'ikace a'ikacen, duk sun juya mata baya, a hankali take furta kalman,,,
excuse me, duk suka juyo, saiyi take kaman wata bakuwa, tana tabayar su plss a ina take nan kuma gidan wanene, sanda suke tabbatar mata a kn take, kuma gidan mijinta Alh. mubark d'a ga Alh. basheer, maimaita kalaman ta rika yie, tare da tuna wasu yen abubbuwa da baxa ta rasa tunawa ba, a rayuwan auran nasu, tana kuma tuna last sanda daddynta ke tambayarta ta auri mubash din,,,,
kenan ta yarda ta aureshi, ta bani ta shiga uku, ta gama lalacewa, kawai tana dan dafe saman kai take wani layi, sai a kasa ta zube sumammiya, da gudu ma'aikatan suka yo kanta suna faman kiran, madam madam.
tana farfadowa ta ganta saman kujera inda suka kawota suka ije, suna tsaye a kanta, yanxu sunfi su biyu, kowa na tunanin abin yie, fuskanta sharkaf da ruwa, wanda sukai ta watsa mata, harta farfado,,,
zaraf ta mike zaune kaman wata zararriya, mai a'iken na fadin,,,
madam are yhu oalright, ko kallan inda suke bata yiba, ta mike da gudunta ta koma upstairs, sanye da wata doguwar rigan bacci take, tare da komawa bedroom din, wajen sif ta nufa inda ta yayo wani karamin gyale tana yafawa saman hulan baccin dake kanta, kaman wata mahaukaya take waige waige, saman wani drower ta hanga key din mota da wayanta, ba bata lokaci ta kwasa, sannan tayo kasa sudai kaman walkiya su kaga ta fuce, sanda ta isa wajen packing space, a haukace take bude mota ta shiga tana sakin wani mahaukacin horn, suma gate men din basu tsaya wasa ba, a haukacen suke bude mata gate din gida, ta fuce a tsiyace.
ikon Allah ne kawai ya kawota zaria lfy, ko wace mota ta ganta saita kauce mata, wasu kuma suna hada mata da zagi da tsinuwa, ta rika sakin wani irin horn da dukkan wanda ke cikin gidan sai da yaji, kuma ya girgixa, sabbin security gard din da daddyn ya zuba suke neman sanin wacece ita, a'iko ta futo daga mota tana zuba ruwan bala'i, sauran tsofafin da suka ganta da gudu suke bude mata gate, tai wucewanta cikin gida tana barin motan a waje ko kofan bata rufe ba, tare da shiga haraban gidan tana kwala kiran,,,