Chapter 009

1.9K 109 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕


*dedicated to jj's family*




*page 009*

――――Da sassafe aka tashi da shirye shiryen salla,kasancewar the next day ne salla masu a'ikin mummy ne keta a'ikace a'ikace, Amal kuwa wanka tayi ta shirya tare da daukan mota ta fuce agidan, na shirya tsaf cikin doguwar hijjab dina skye blue na hadda,tare da daukan 1k din da mummy ta bani naje na mata sallama cewa zanje samaru can zamu saloon din dasu zarah ,

tace, a dawo lfy,karki dade, na futa ina raya yanda zanyi da kudin transport don na saloon dinnan da kerma na samu mummy ta bani, nasan tabbas yanxu nai mata wani magana zagi ne kawai za biyo baya, don haka na yanke shawara inna je can in shiga ko gurin haj. in amsa kudin transport din.

Haka kuwa nayi,mai napep din daya dakko ni ya jira ni waje nai saurin shiga ciki don in amso mashi,,,,

Anan farfajiyar gidan na wuce kannin daddy gurin wasu mota suna tsaye, gani harda wasu daban saniba yasa na wuce kaina duke, tunanina baxa su gane niba, ina shiga ciki nayi karo da zarah, nace, yawwa zara kina da chancin 500 zanba driver napep ne, taja hannu na tana fadin, zo muje, gun haj.ta amso mun, kudin muka futa tare don baiwa mai napep kudinsa.

dai dai inda suke tsaye naji an kwala ma zarah kira, ta kalleni tana fadin, jeki kai mishi kudin uncle bello ne ya kiran,na wuce da sauri don bana son na karisa gurinsu saboda yawan da suke dashi,

zarah taje tana fadin,uncle bello gani, yaya sagir dake tsaye jikin mota fuska tamke yake fadin, uncle bello gaki ko?,baku iya gaisuwa ba,sai lokacin ta lura da aboka nansu ne,tare da yaya majeed a gun tayi saurin gaishe su, uncle bello na tambayar, ke wacece wancan yarinyan da bata iya gaida mutane ba, yaya sagir ya amshe da, ku haka kuke kwashe kwashen kawayen da basu san mutuncin mutane ba, uncle idris ya amshe da, shegen rore roren tsiya ne dasu a'i , idon zarah yai rau rau tana fadin,,,,

bafa friend dinmu bane,,,,,ji tayi an karisa mata da fadin,meenal ce ko?, da sauri ta juya kan wanda yayi maganan yaya majeed ne, ta kada kai tana fadin, eh itace, nie bansan bata gaida kuba, uncle bello yace, yarinyan yaya sulaiman ne?uncle idris na fadin, eh kanwan Amal ko?tace eh ita,,,,

dai dai sanda na kariso gurin gabana na wani irin dumm, naji ance,ke zo nan, na juya uncle bello ne ya kiran,na karisa gun ina tafiya cikin sanyi,,,,,

ya zaro mun ido yana fadin,dago ido kie kalleni, kina wani kasa da kai baki iya gaida mutane bane, uncle idris yace,ko baki sanmu bane, tuni ido na suka cika da kwalla murya na rawa nace,dama zan bari inna dawo in gaishe kune,yaya sagir yace, shegen iya bada excuse da yaran nan in ance wannan suce a'i kaza ne, uncle bello yace, to daga yau in kinga mutane ki tsaya ki gaishe su kafun ki shiga ciki, don nan daga uncles dinki sai brothers dinku ne, uncle idris ya soma zuba nashi akan rashin zumuncin da ba muyi kwanaki ma sai daya zazzare ma Amal ido sannan inta ganshi take gaidashi, nidai ina jinsu, wani cikin abokan nasu yace, pls kuyi hakuri a barsu su tafi,yaya sagir ne ke fadin, baka san yaran nan bane sai ana tsawa ta musu, ya kalli zarah yace, karka ji bakan yarinyan nan da shegen bakin rashin kunya, in sun girma ji suke dai dai da kowa,zarah ta zumburo baki tana bata rai, akace mu tafi,nidai naja zarah muka wuce, sai lokacin na lura da yaya majeed din dake jingine jikin mota yana waya kusa da yaya sagir kanshi na kasa, na dan bishi da ido har muka wuce, zarah na fadin, i hate u sagir, i hate u so much.

Dakin haj. muka kule muna hira, na kalli ummee ina tambayar ta, nawa za'a wanke mun kai,,,,,

tace, nawa kike dashi, nace, just 1k nefa tace, karki damu ki ije wannan sai kiyi lalli dashi, za muje gidansu wata friend dinmu ta wanke mana ma, mummyn su ta bude mata saloon din a gida tana yie na business, zata mana kyauta, na zaro ido da fadin, sai kace mu muka bude mata, tai wani far da ido tace, a'i banda haka ma yayanta habibi nane, irin na special dinan kin gane a'i, su zarah suka sa dariya suna tafawa, nai murmushi ina fadin, lallai ashe shi zai biya,tace, eh, naki kawai da nawa zai biya banda na tijararrun nan, sameera tai karaf din fadin,a'i kinsan ko najib bai biya mun ba habiba ba zata ki wanke mun kaiba, zarah ko cewa tayi, ah dadin abinma nima nawa sweet heart din bai tafiba jiya saida ya bada nashi kudin da za'a gyara ni,,,,,,,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now