part 5-6 (Asalin labarin)

1.2K 131 1
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*


*Bismillahi Rahamanir Rahim*

3/January/2019

5-6


Muhammad Na shiga gida ya tadda Sameerah tsaye a compound ta zabga uban tagumi, tana ganin sa ta sauke hannu ta ce,
"Honey M kaga My Adat."

Kallon ta yayi ya ce,
"Bangane naga Our Adat ba, ba anan na bar ta ba."

Hannu ta daura akai ta ce,
"Na shiga uku Honey M wallahi bayan fitar ka da mukai sallah ta ce tafiya zatai ko abinci fa bata ci ba."

"Inna lillahi wainna illahir rajiun."
Hannun ta ya kamo sukai cikin gida.

A falo ya zaunar da ita ya ce,
"Ki zauna bari naje gidan Momy ko can ta koma."

Hannun sa ta rike ya ce,
"Nai miki alkawarin nemar miki Our Adat."

Kiss yai mata a kumatu sannan ya mike ya fita. yana fita ya nemeta ya rasa. Duk layikan unguwar ya duba amman ba mai kama da ko Ja'ada ko mutum daya ma bai gani ba.

Motar ya tsayar ya kifa kan sa yana tina rayuwar da sukai da ja'ada. Shiru yayi a ran sa ya ce, anya kuwa shima ba mafarki yayi da Ja'adatun sa ba kamar yadda ya saba.

Gidan Momy ya nufa yana zuwa ya fada mata kan cewa ko Ja'adatu ta zo

Kallon sa Momy tayi da mamaki ta ce,
"Kamar ya Ja'adatu ta zo bayan can gidan naku ta tafi."

Shiru yyi ya fada mata duk yadda akai cewa
"Na dawo daga massalaci na samu Sameerah ta ce, wai Ja'ada ta fito kafin ta duko waya ta kira ni, dan ta ce, bazata kwana acan ba akwai abinda zatai gobe, amman zata dawo , dan haka ta taho shine  Sameerah ta ce, na biyo ko ta dawo."

"Wai me ke faruwa ne, Ja'ada da mukai sallama da ita kancewa acan zata kwana. Kai kaga da dokin da ta tafi ko abinci fa bata tsaya ci ba. amman kuma ace tazo ta tafi kuma kaga ni Ja'ada bata dawo ba."

Haka Muhammad ya fito daga gidan Momy ya dawo unguwar su aamman sai ya kasa shiga gida saboda shi kan sa bai da nutsuwar da zai rarrashi Sameerah

Kan sa ya kifa akan sitiyarin motar idon sa jajir, ya fara tino da Ranar farko da suka hadu da Ja'adatun sa.

************
Da Yamma ne, sakaliya wajen karfe biyar da arba'in da bakwai, anan unguwar gandun albasa, dake cikin garin Kano. ta taso daga isilamiyya,

Sanye take da uniform Ash kala riga da wando, tana tafe tana dan gudun ta dan yarinya ce da bata wuce shekata tara ba a lokacin.

Amman kalo daya zakai mata kasan yarinyar kyakyawa ce, dan duk da karacin shekarun ta ana gane hakan.

Uniform din ta fes suke kamar lokacin ta saka su. Dai dai kan wani layi ta buge wani saurayi, dake kokarin bude mota. wannan yasa ta tsaya ta dago kai.

Kallon saurayin ta tsaya yi, wanda kyawun sa su suka saka ta tsaya kallon sa.

Saurayin balaraben yaron ne ko ince ba indiye, sanye yake da black kalar wando jeans da farar riga mai dogon hannu. Idon sa sanye da farin glass mai garai garai.

A ido bazai wuce shekara goma sha takwas zuwa sha Tara ba. Daga kallon yaron kasan dan gidan masu kudi ne.ko daga kallon kayan dake jikin sa da kalar fatar sa dake sheki.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now