part 69-70

718 53 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Wednesday
20/February/2019
69-70



"Zazzabi ne sai ciwon kai. Ciwon kan ma yafi damun ta dan yanzu ko tafiya bata iya wa saboda jiri."
"Ya salam!"

Mustapha ya fada yana yin waje da take. jikin ta ya taba yaji zafi rau ya taba kan ta ma haka. Jawad da kishi ya cika shi wai saboda ke xai na taba masa ita ya ce,
"Malam mene na taba jikin ta ne?"

Murmushi Mustapha yayi dan ya gano wani abu a idon Jawad wanda yai mamaki to tayaya zai so kanwar Sameerah sai dai  in ko karya yai masa ba kawar Sameerah bace.

Wayar Jawad ce tai kara ya dauka da sallama. Samerrah. Ta ce,
"Honey M kun karasa aisbitin?"

"Eh gamu yanxu muka shiga."
"Ok Allah ya sauwake"

"Ameen!"
Ya kashe wayar.

BP ta ya auna wanda yai matuwar bashi mamkin ganin yadda ya mugun hawa. Kallon ta yayi ya ce,
"Ba wani abu dake damun ki."

Gefen Kirjin ta ta nuna masa alamar yana mata ciwo. A aran sa ya ce,
"Allah yasa ba abinda nake tunani bane."

Yai mata tambayoyi daga baya ya ce aje ai mata hoto da wasu text text.

Cikin minti bai bi gpma sha biyar ba aka gama komai aka kawo masa. A kan gado Jawad ya kara kwantar da ita.

Idon ta a lumshe. Dr ya amshi sakamakon sannan ya zauna. Yana fara duba file din ya dago da sauri ya kalle ta sannan ya kalli Jawad.

"Ya sunan ta?"
Ya tambaya. Dan bai yi zaton file nata bane.

"Ja'adatu!"
Kallon file din yayi tabbas sunan ta ne ajiki. Ajiyar zuciya ya sauke ya mike ya karasa wajen gadon.

"Ja'adat kina da ciwon zuciya ne daman cam?"
Kai ta girgiza masa.

"Kina zuwa asibiti ganin dr game da wata lallura."
Kai ta gyada masa.

"Akan me kike zuwa ganin Dr?"
"Ni dai ina yawan ciwon kai ne, sai kuma jiri da yawan ci ke damu na. Mun taba zuwa asibiti aka ce min wai jini na ya hau, to tin daga lokacin in na saka damuwa a rrai na har kwanciya jinya nake!"

Saman dakin ya kalla ya ce,
"Kina yawan tunani da zama a cikin damuwa ko?"

Kai ta girgiza yayi murmushi ya ce,
"Kar ki min karya Ja'adatu, tin zuwan ku asibitin nan na nage kina cikin damuwa ki fada min damuwar ki in baki shawara sannan na daura ki akan magani dan ko na baki magani in dai ba za ki cire damuwar ki ba to lallai maganin ba lallai he yai aiki ha."

Shiru tayi. Ya koma ya zauna ya ce,
"Jinin ki yayi mugun hawa, ta yadda komai xai iya faruwa dake daga shanyewar barin jiki. Banyi tunanin xan ganki haka ba a yadda na ga yadda jinin ki ya hau. Bayan nan kuma zuciyar ki tana son kamo da ciwo wanda yanzu haka yana cikin wani hali da dole sai anbi komai a hankali."

Da sauri Jawad ya ce,
"Me?"

Kallon sa Mustapha yayi ya ce,
"Tabbas, abinda na fada haka ne."

"Inna lillaji wainna illahir rajiun."
Tabbas ya tabbata ko Ja'ada bata fada masa ba akan sa take fama da duk wadan nan abubuwa.

Kai ya dafe dole ya ciro Ja'ada daga wannan halin dan ya tabbata shine magani abin.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang