117-118

674 60 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

17/April/2019
Wednesday
117-118



A cikin wata ukun nan da ya gabata abubuwa da dama sun faruwa.

Matan Mustapha da Buhari duk sun zo da su dan ganin wannan Ja'adatun da ta kusa yin ajalin abokin mijin su.

Gaskiya ne da suka ganta sun yadda koma menene namiji zai iya yi akan ta ba dan kawai kyan ta ba har da salon ta dan zuwan su kawai sun ga tarba ta sake dasu. Sannan tana da nutsuwa ita a jinin ta abun yake kome tayi sai ya burge wanda ke tare da ita ko da bai son ta sai dai yayi kyashi ya ki fada.

Sun amshi number ta suka tafi da kewar ta haka ita ma da zasu tafi ta basu turaruka ya'yan su mata ta basu ribom da su alawa.

Jawad ma ya kai su gidan su dan yini sukai yi Momy ta kara yabawa da halin Ja'adatu tai ta godiya da Allah da ya bawa yaron nata mata na gari salihai.

Duk gidajen yayen sa ya kai ta kuma sun nuna mata so da kauna bata da matsalar komai sai ta yadda ta kasa sakewa da mijin nata.

Zaune take a falon tana sanye da dogun jan siket da bakar riga mai ratsin ja kan ta, ta yi rolling da jan mayafi. fuskar ta daga kwalli sai man lebe kawai sai tashin kamshi take.

Ta zuba tagumi tana zaune hawaye na fitowa ta idon ta ita kan ta bata san hawayen take ba.

Sameerah ce ta shigo cikin shigar ta ta bakar doguwar riga Junaid na hannun ta.

Kallon ta tsaya yi sam Ja'ada bata san da shigowar tata ba duk sallamar da takeyi.

Jikin ta ne yayi sanyi ta karasa ta xauna a gefen ta Junaid da suna zama yayo gun ta shi ya dawo da ita daga tunanin da take.

Ta juyo ta dauke shi tana fadin
"My Son afternoon!"

"Kukan me kike?"
Sameerah ta fada tana kallon ta.

"Kuka kuma?"
Ta fada.

Fuskar ta Sameerah ta shafo ta nuna mata. Fuskar ta goge ta yi shiru kawai.

"My Adat!"
Ta kira sunan ta cikin kulawa.

Dagowa tayi ta kalle ta sannan tayi kasa da kai kan ta amsa dda
"Na'am!"

"Mecece ni a gun ki?"
ta tambaye ta.

" *Aminiyya tah* !"
Ja'ada ta bata amsa. Kallon ta tayi ta ce,
"Ni ba *aminiyar* ki bace!"

Da sauri ta dago ta kalle ta ta ce,
"Me kike fadi?"

"Eh saboda baki dauke ni a matsayin aminiyar ki ba. Ki dauke ni a matsayin kishiyar ki ne!"
Kallon ta Ja'ada take,
"Baki dauke ni a matsayin wacce kike so ba, tin da akai case din auren ki da Honey M nake ciki dake Allah ne ya taimake ki baki da lafiya amman wallahi naji ba dadi ace kinsan inda Honey J yake kin rufe ni kin ki fada min kinga baki dauken aminiyar ki ba. Kuma kina ganin yadda Honey J yake shan wahala akan ki amman kika kii fada min. Haba My Adat me kika dauke ne? Me kika dauke? Yadda na dauke ki sam ba haka kika dauken ba. Haba My Adat yanzu kin kyauta kenan. Bayan nan kuma yanxu anyi auren nan nasan kina son Honey J me yasa kika ki bashi soyayyar ki. Me yasa kika ki tallafi shi kinsan irin maraicin ki da yayi kuwa, honey J bai cancanci haka ba sam, dan haka ina fada miki kiyiwa kan ki fada. Ki sauke hakkin mijin ki akan ki baki san gawar fari ba in kika mutu da hakkin sa kar kiyi tunanin wai Honey J zai yafe miki tabbas zai yafe miki amman me yasa ke baza ki gujewa daukar hakki ba My Adat Allah ya sani ina son ki na dauke ki fiye da yadda kika dauke in da kin dauke yadda na dauke ki baza ki na batawa Honey J Rai ba bayan kinsan ni da shi duk muna son farin cikin sa da nutsuwar sa. Dan Allah My Adat ba dan ni ba ki saki duk wata shawarar da zuciyar ki take baki ki ki rumgumi mijin ki dan Allah dan Allah na fada miki!"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now