NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
5/February/2019
39-40A bangarrn Sameerah ta rasa gane kan mijin ta zata iya cewa tin kan ya tafi Jigawa yake fama da zazzabi da ciwon kai ban da kuma abinda ba ta sani ba wanda tana lura da shi akwai damuwa mai yawa tare da shi.
Amman kuma sai ya nuna babu komai duk wata kulawa ya rage bata ba dan komai ba sai bai da kwanciyar hankali da nutuswar hakan.
Ya rame dan sam baya iya cin abinci ko yaje office baya iya yin komai sai kwanciyya da kuka da tunani. Shi damuwa Sameerah damuwa.
Tin da ya dawo daga aiki ya shige dakin sa bata kara jin motsin sa ba wannan yasa tai zaton ko bacci yake.
Can dai ta mike ta nufi dakin nasa, a hankali ta tura kofa ta shiga.
Ganin shii tayi zaune akan gado ya jingina bayan sa da makarin gado, idon ssa biyu ya zubawa waje daya ido daga gani ya lula cikin duniyar tunani.
Matsawa tayi gefen sa ta dan dafa shi a firgice ya juyo yana ganin ita ce, ya kamo ta.
Saurin matsawa tayi tai hanyar fita.
"Kar ki fita Sameerah!"
Ta tsaya bata juya ba kuma bata tafi ba.Mikewa yayi a hankali ya karasa wajen ta ya kamo ta ya dawo da ita gefen gado.
Idon ta yaga ya kawo ruwa,
"Kar kiyi kuka my wife!""Dole nayi kuka Honey M a zato na bacci kake amman ashe idon ka biyu kwana biyu duk ka dauken wuta me nayi maka dan Allah?"
"Wallahi Allah ba abinda kikai min!"
"To me ke damun ka, kana cikin damuwa kar kace min babu."
Ganin bai da amsa yasa yya jawo ta jikin sa ya fara aika mata da sakonnin da ta fiso.Nan da nan ta sake ta bashi kan ta ya cigaba da sarrafa ta, har sai da ya cimma burin sa sannan ya kwale ta.
Da kansa ya daga ta sukai wanka suka shirya sannan ssuka sauko kasa ta dinga bashi abinci a baki har ya koshi,
Amman yasan tana nan cike da tambayar menene damuwar sa shi ne yake kawar da hankalin ta dan kar ta tambaye shi.
Da ta gane haka sai ta sa a ran ta zatai tayi masa addu'a Allah ya yaye masa damuwar sa.
Suna zaune a falo ta dauki wayar ta ta fara kiran layin Ja'ada cikin sa'a kuwa ta shiga ta dauka.
"Assalamu Alaikum!"Ja'asa tayi sallama,
"Wa'alaikum salam my Adat!"Wata faduwar gaba Ja'ada taji tai saurin rufe idon ta sannan ta ce,
"My Samee!"Sameerah dake jikin Honey M ta kara gyara kwanciyya ta ce,
"A da kenan. Dan Allah me nayi miki kika guje ni a lokacin da nake tsaka da bukatar ki."Murmushi Ja'ada tayi ta ce,
"Ba haka bane My Samee wallahi ba abinda kikai min kuma ba gudun ki nake ba.""Bazan yadda ba in har ba ganin ki nayi a tare dani ba. Yaushe zaki zo min?"
Shiru Ja'ada tayi ta ce,
"Zan zo kwanan nan!""Ba wani kwanan nan na kusa haihuwa ki taho ki zauna min!"
Shiru Ja'ada tayi ta ce,
"Kinsa dai ina aiki ko?"
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...