NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
21/2/19...
*Ina tayaka murnar zagayowar ranar haihuwar ka. Ina maka addu'a akan Allah ya kara maka nisan kwana mai albarka, Allah ya jikan Alhaji, ya karawa Hajiya lafiya da nisan kwana. Allah ya biya maka bukatun ka na alheri ya baka mace ta gari da zuri'a mai albarka. Allah ya sa ranar da zaka koma ga Allah ta zama rana mafi Albarka a cikin rayuwar ka. Allah yasa kayi kyakyawan karshe. Ameen Ya Allah*Thursday
21/February/2019
71-72Acan daki kuwa duk suna tsaye akan ta kowa akwai tamabayar da yake aika mata da ita.
Dady ya ce,
"Sannu Ja'ada ya kike jin jikin?"Momy ma ta ce,
"Ya jikin?"Sameerah kuwa cewa tayi
"Sannu My Adat, me ke damun ki yanzu."Murmushi tai musu sannan ta ce,
"Ni ba abinda ke damu na."Momy ce ta kama hannun ta, ta ce,
"Sannu Ja'adatu."Murmushin karfin hali ta saki ta ce,
"Yauwah Momy!""Me kike bukata?"
Dady ya fada yana daga tsaye a wajen kan ta."Bana bukatar komai!"
Ta fada."Dan Allah My Adat me yake damun ki haka har kika shiga cikin wannan yanayin."
Kirjin Ja'ada ne ya buga jin tambayar Sameerah.Shiru tayi sannan ta dago kai ta kalli Sameerah ta ce,
"My Sameee cuta ai ba sai da dalili ba wata kan zo haka kawai.""Ban yadda ba ki fadan damuwar ki dan Allah!"
Murmushi Ja'ada tayi ta kamo hannun Sameerah sannan ta ce,
"Ki yadda da ni."Zatai magana sai kuma tayi shiru ta ce,
"Naji na yadda amman dan Allah ki cire damuwa a xuciyar ki ba zan sso na rasa ki ba dan Allah kinji."
ta karasa maganar idon ta na zubar da hawaye.Murmushi Ja'ada tayi ta ce,
"To menene na kukan? Ki daina in ba so kike nima nayi ba."Da sauri ta goge fuska tayi ta ce,
"Kada kiyi nima na daina."Ta sakar mata murmushi ita ma Ja'adan murmushi ta sakar mata suka rumgume juna.
Momy da Dady suna tsaye suna kallon su cikin so da kauna yaran na burge su yadda suke son juna. Zasu ce basu taba ganin aminai irin su ba sam basa fada sannan damuwar daya ta daya ce halayar su abar so ce ga kowa dan duk kan su suna da hakuri da hankali ga nutsuwa ya ladabi da biyayya ga ilimi.
Dan tsabar aminta har kama suke yi dan dai Ja'ada tafi Sameerah tsayi ne ita kuma Sameerah tafi Ja'ada kiba amman hasken su daya. Kuma dukkan su akwai kyau ga idanu da siraran hanci haka suna da yalwar gashin kai duk da Ja'ada ta fi Sameerat.
"Bari naje naga Dr Mustapha!"
Dady ya fada. Mikewa Momy tayi ta bi bayan sa.A office din Musty kuwa tinda Jawad ya kwantar da kai Mustapha ke kallon sa yana tausayawa dan uwan nasa.
Tabbas inda zai fada masa inda yarinyar nan take da sai yaje ya nemo masa ita amman to ya zasu yi addu'a ita ce kadai magani.
Jawad kuwa yana kwance nan saka yake da warwara ta yadda xai war ware wannan abin har ya auri Ja'adatu.
DU LIEST GERADE
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...