part 73-74

724 60 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Friday
22/February/2019
73-75






Abbah zai magana Dady ya ce,
"Dan Allah muje!"

Wannan yasa suka shiga dakin a lokacin da ta tashi kenan Sameerah ta mika mata ruwa tana sha.

Jin sallanar su Abbah yasa tai saurin dago kan ta. Murmushi ta sakar musu. Mamah ta karaso gare ta tana fadin
"Ah ai jikin da sauki ma!"

"Eh Mamah Alhamdulilah! Yaushe kuka zo?"

"Bamu jima ba."
"Ina yini ya hanya?"

Ta fada tana kallon Mamah.
"Lafiya Alhamdulilah!"

Abbah ta mai da kallon ta ta mika masa hannun ta. Matsowa yayi ya kama hannu ya ce,
"Ja'adatu ya jikin?"

"Da sauki Abbah ya kuke ya hanya?"
"Alhamdulilah!"

"Masha Allah!"
"Ai jikon ma da sauki"
Ya fada yana kallon su Dady.

"Eh Alhamdulilah!"
"To Allah kara sauki."

"Ameen!"
"Bari mu zamu tafi."

Abbah ya fada. Fuska Ja'adatu ta bata dan taso ace su kwana da ita amman wai har zasu tafi.

Gane haka yasa Momy da Dady fita Sameerah ma ta basu waje. Ganin haka yasa Ja'ada ta ce,
"Abbah ba zaku kwana ba!"

Yar dariya yayi ya ce,
"Haba dai Yar Abbah ni fa garin ma muka zo suka ce suna asibiti. Mu kwana muyi me ai sai suga kamar bamu ga kulawar su gare ki ba. Ki kwantar da hankalin ki a koda yaushe muna tare da ke ko bakya tare da mu kinji. Addu'ar mu baza ta taba karewa a gare ki ba. Allah ya baki lafiya yai miki albarka."

"Ameen Abbah nagode!"
Sai ga hawaye.

"Kukan kuma fa?"
"Ba komai!"

"To ki daina!"
"Na daina Abbah!"

Mamah ta ce,
"To Ja'ada Allah baki lafiya mu mun tafi!"

Ta fita a dakin. Abbah ya mai da kallon sa ga Ja'ada ya ce,
"Dr ya fadan abinda ke damun ki. Ja'adatu nasan akan Jawad ne dai. Dan Allah Ja'adatu ki maida komai ga Allah ki dage da addu'a in Allah yayi Jawad mijin kine wallahi sshi xaki auri haka nan in ba mijin ki bane ko yana nan baki auren sa. Ki mika komai ga Allah kinji. Allah yai miki zabi mafi alheri,"

Kai ta gyada korjin ta na bugawa dan yanzu ta daina fatan auren Jawad dan so take son sa ya fita ma a zuciyar ta ko ta huta amman abin kamar dada mata shi ake.

"Nagode Abba!"
"Ki daina damuwa kinji.  Ki rage tunani kowa da irin kadarar sa kiyi tawakali ki samu kici taki kalar kaddarar Allah bazai barki haka ba da izinin Manzon Allah!"

"Allah yasa !"
Ya mike ya ce,
"Mu zamu tafi. Naji kuma ance a cikin satin nan za a kawo kayan lefe ko?"

Kirjin ta ne ya buga dan ita ta manta da wani kayan lefe ma. kai ta gyada masa. Ya ce,
"Allah ya sanya alheri. Allah yasa ayi damu."

"Ameen!"
"Na tafi "

"To Abbah Allah kiyaye hanya ya tsare ya kai ku lafiya."
"Ameen!"

Ya fita a dakin. A falo ya same su suna ta hira ya ce,
"Tashi mu tafi."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now