*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Tuesday
26/February/2019
81-82Har akai la'asar sannan suka tafi masallacin asibitin daga nan wani store suka tafi. Izeedeen ya jido kayan dubiya masu uban yawa dan katon katon din abubiwa ya dinga dauka.
Daga can asibiti suka dawo dai dai dawowar Jawad kenan. Wasu mutane yasa suka taimaka musu suka shiga da kayan. Ana cikin shiga dasu Jawad ya shigo. Da Momy suka gaisa sannan ya ce,
"Momy bari naje gun Mustapha naji ya jikin nata!"Ya fita. A hanya ma sai da suka hadu da Jawad amman shi Jawad bai gane su ba ya shige Su.
Marzuk ne ya kalli Izeedeen ya ce,
"Guy kaga wancan dan girman kan ko?""A'ah ina jin bai gan mu bane!"
"Ba wani bai gan mu ba."Murmushi yayi ya ce,
"Friend menene a ciki mijin aminiyar matata ne fa!""Uhmm ba ka zo min da zancen sa ba akan Ja'ada."
"Eh!"Izeedeen ya fada yana gyada kai.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
"To wallahi ranan na tabbatar da maganar ka. Wannan guy din son Ja'ada yake!""Tayaya ka gane hakan?"
"Baka ga kallon da yake mata ba. Kai magana da nake mata ma baka ga yadda yai hade rai ba.""Yanxu ya xanyi?"
"Kai dai in yarinya na son ka forget about him!"Ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ce,
"Tabbas Ja'ada na da wanda take so. Allah ina rokan ka kasa ba wannan mutunin take so ba. Gwara ta so kowa da taso Jawad!""Muje ko?"
Marzuk ya fada yana kamo hannun sa.Jiki a sabule ya bi Marzuk suka shiga dakin. A falo suka samu Dady da Momy. Nan suka gaisa Dady yake fadan kayan ai sunyi yawa.
Izeedeen dai kan sa a kasa sannan suka cikin dakin. A kan Three sitter suka zauna.
Sameerah ta kalle su ta ce,
"Amman an gode wannan irin kaya haka.""Kai Sameerah dan wannan ai ba komai!"
"To an gode!"Suka zzauna ana hira dasu. Jawad na zuwa yaga Mustapaha baya nan ya dawo dakin.
Da Sallama ya shiga su Dady suka ce ya shiga ciki. Yayi ciki da sallama.
"Assalamu Alaikum!"Yai sallamar cikin dakakiyar muryar sam wacce ta tabo zuciyar Ja'ada da sauri ta dago ta kalli kofar.
Amsa masa sukai gaba dayan su. Yana shigowa yaga su Izeedeen kai ya dauke sai kuma yaga Nusaiba zaune a gefen gadon Ja'ada akan farar kujerar roba.
Fara'a ya saka yayi gun ta tana fadin
"Mum/Daug ashe kin karaso!""Eh wallahi Dad/Son"
Yayi gun Gadon Ja'ada yana kallon ta. Ita ma da ta kafe shi da ido tai saurin dauke ido."Our Adat ya jikin?"
"Da sauki.""Allah kara sauki!"
"Ameen!""Me kike bukata?"
Sameerah ce ta cafe ta ce"Naman jiyan nan taji dadin sa shi zaka kawo mata anjima."
"An gama!"
ESTÁS LEYENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasíaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...