*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Sunday
24/February/2019
77-78Tin asuba da ta tashi bata koma ba gyaran gidan ta hau yi sannan ta shiga kitchen ta hada break din su da na asibiti.
Tana gamawa ta shige ban daki tayi wanka tayi wa Junaid sannan ta shirya.
Dakin Jawad ta shiga ta same shi kwance bai tashi ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta zauna a gefen gadon. Hannun ta ta saka cikin gashin kan sa tana wasa da shi.
Ido daya ya bude yana bin ta da kallo. Agogon dakin ta kalla ta langwasar da kai tayi. Mikewa yayi zaune ya ce,
"Karfe nawa ne?""Takwas saura fa!"
mikewa yayi ya shiga ban daki.Dakin ta fara gyarawa sannan ta xauna jiran sa. Yana fitowa ta fara goge masa ruwan jikin sa. Nan da nan ta shirya shi tsaf sannan suka sauko kasa.
Tea ta hada masa sannan ta tura masa fulas ta ce,
"Bismillah!""Kefa?"
"Sai naje naga My Adat!"Abincin ya fara ci sai da ya gama sannan ya mike ya mikewa Sameerah tayi ta dauko masa jakar sa sukai waje.
A Mota har ta zuba duk abinda zata bukata dan haka motar driver kawai ya tada suka nufi asibiti.
Office din Mustapha, Jawad ya nufa. Ita kuma ta yi dakin Da aka kwantar da Ja'ada.
Momy ta sama akwance akan kujerar dakin, sai Ja'ada dake ta bacci. Basket din hannun ta ta ajiye sannan ta nufi bakin gadon tana kallon Ja'ada.
Ta dan fada kadan, ido ta dauke ta dau tsintsiya ta fara aiki sannan ta share falon ta hade shi da kamshin roomfreshner take dakin ya hau kamshi mai dadi.
Ban daki ta shiga ta wanke sannan. Ta fesa masa kamshi shima mai dadi.
Tana ffitowa Momy ta bude idon ta. Kallon dakin tayi ta kalle ta sannan ta kalli agogon wayar ta.
Mikewa zaune tayi ta ce,
"Ke kuwa tin yaushe kika zo?"Zatai magana kenan sai ga sallamar Jawad nan.
"Assalamu Alaikum!""Wa'alaikun Salam!"
Momy ta fada tana gyara zaman ta.Durkusawa yayi kan sa a kasa ya ce,
"Ina kwana Momy?""Lafiya lou! Kun tashi lafiya?"
"Lafiya kalou!""Ya me jikin?"
"Da sauki!""Allah kara sauki."
ya mike yayi gun gadon. Yana karasawa Ja'ada ta bude idon ta akan Jawad.Ido tai saurin lumshe ta ce,
"Sannu Ja'ada!"Kai ta gyada masa. Sameerah ta ce,
"Ta tashine?"Kai ya gyada mata da sauri tayi gun gadon tana dafata ta ce,
"Sannu My Adat ya jikin?""Da sauki.!"
Ta fada tana kokarin mikewa. Sameerah ce ta taimaka mata ta mike. Ta jingina ta da filo sannan Jawad ya ,
"Ya jikin?"
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasiaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...