NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Monday
7/January/201913-14
"Saboda me kika ce haka?"
"Honey J, kai mai kyau ne, sannan halaiyar ka masu kyau ne, kana da ilimi ga girmama manya ga tausayi ga ibada ga komai da komai fa...... Allah ko dan kyan ka ma zata so ka."Murmushi yayi ya ce,
"Kina son kyau na. Nima ina son kyan ki amman kuma in tambaye ki?"Kai ta gyada masa, ya ce,
"Kina son ki aure miji mai kyau?"Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,
"To gani nan dai. Kasan Allah shi ke zabawa mutum abokin rayuwa bamu ba. Amman ni dai ina so kuma zan iya cewa bana so.""Saboda me kike so?"
"Ai kowa na son me kyau wanda zai ga ni yaji dadi ko?""Haka ne, saboda me bakya son me kyau?"
"Saboda yan mata. Yan mata akwai son mmai kyau in ka auri mai kyau za ana damun ka da kawo maka hari, to in yana tsananin son ka ne zai kauce musu in kuwa son gashi gashi nan ne dai sai kaga ya biye musu. Ni ba zan iya tsayawa fada akan namiji ba duk yadda nake son sa. Shi yasa.""Shikenan!"
Kai ta gyada."Wane irin miji kike so?"
Shiru tayi ta dan lumshe ido sannan ta bude ta kalle shi da shanyayun idanun ta. Wanda kadan ya rage ya saki motar."Ki dainai min irin wannan kallon!"
Ya fada yana gyara zama."Saboda me?"
"Zan fada miki amman ba yanzu ba.!""To menene da kallon?"
"Ki tambayi Sameerah ko ki duba mudubi."Dariya tayi ta ce,
"Kana son kace mutum ya duba madubi kasan akan duba madubi shine na taba makara har kazo kace me yasa na makara. A ranar nasan ya kammanina suke kai ka fara fadan."Dariya yayi ya ce,
"Bani amsa ta?'"Wacce?"
"Wane irin miji kike so ki aura?"Dariya tayi sannan ta ce,
"Kamar Yaya na!""Wanne yayan naki?"
"Honey J man.""Mene da shi Honey J din da har kike son samun miji kamar shi."
Murmushi tayi ta ce
"Yaya kai ma ka sani. Komai da kake da dabi'un ka saukin kan ka, fara'ar ka murmushin ka, ilimin ka duk su nake nufi."Layin gidan su suka shiga. Dariya yayi ya ce,
"Kice dai kina son Yayan naki kawai."Baki da danne da hannu ta ce,
"Ka rufan asiri ni ban iya zama da kishiya bayan nan ma naji kana cewa son ita wacce zai haukata ka ko zai maka illa ai wahala zan sha."Dariya yai sosai dan ya gane itama Ja'ada kamar tana son sa, ga kishi kuma daga gani zatayi shi.
"To in kuma nace kece wannan wacce zata haukatanin fa."
Dariya tayi ta mika hannu ta dauko jakar ta a baya ta ce,
"To ka fada din ma nasan zolaya ce kawai."Ta bude kofar zata fita.
"Ki tsaya!"Ya fada da wani irin sauti. Da sauri ta juyo ta ce,
"Menene?"
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasiaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...