Part 21-22 (Jawad na Ja'adah)

835 68 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*


*Bismillahi Rahamanir Rahim*

'''Juma'at Mubarahk. To all Muslim Ummah. May Allah Accept all our prayers. Ameen'''

Friday.
11/January/2019

21-22

Jawad bai tashi dawowa ba sai bayan karfe biyu. Da kaya nan ma ya shigo gidan,

Akwati ce Babba da mai bi mata sai wasu kayan a hannun sa. a falo ya zube su.

Mamah da Ja'ada ido suka bishi da shi. Ja'ada ya kalla ya ce,
"Zo ki ga kayan ki!"

Matsawa tayi jiki a sanyaye ta zauna. Shi ya bude akwatin shada da atamfofi da material ne da dogayen riguna sosai English wears. Dayan akwatin kuma takalmi da jaka ne kala uku uku sai mayafi da hijab. Da kayan kwalliya su turaruka da mayauka. Har da under wears.

Ledar ya turawa Mamah ya ce
"Ga naku nan Mamah!"

Shadda ce yadi goma goma kala uku sai atampa da leshi da material ita ma.

"Jawad hidimar nan tai yawa!"
"Mamah ina yawan yake. akwai shiyasa kika ga anyi."

"Ni dai duk da haka Jawad."
"Mamah dan Allah ki yi hakuri ki min addu'a kawai."

"To Allah saka da alheri. Allah biya maka bukatun ka."
"Ameen Mamah na "

Mamah ta mike ta fita. Kallon sa ya mai da kan Ja'ada. Ta ce,
"Nagode Honey J Allah kara budi."

Daga yadda take magana mma ya gane akwai abimda ke damun ta. Kallon ta ya kara yi ko zai gane amman ya kasa.

Mamah ce ta kwalawa Ja'ada kira wanna yasa ta mike ta bacewa ganin sa. Ido ya lumshe. A ransa ya ce,
"Naso ina nan za ai saukar ku Ja'adatu nah!"

Sallamar ta ya ji ya bude ido tare da amsawa. Fulas din abinci ne da ruwa da lemo da shi ke kawo musu shi.

Abincin ya bude kamshi ya dake shi. yunwa yake ji amman bazai iya ci ba ba tare da ya ji me ke damun Angel din sa ba.

Mikewa yayi ya koma gaban ta. Hannun ta ya kamo ya ce
"Fadan meke damun ki?"

Kwalla ce ta cika idon ta hannun ta ta zare ta goge sanna ta kara kama hannun sa.

Wasa take da hannayen sa. Ya dago kan ta. Ido ta rufe. Dan murmushi ya saki ya ce,
"In har kina so hankali na ya kwanta ki sanar min da me ke damun ki?"

"Honey Jyyy...."
Sai kuma kuka.

"Ya salam!"
Ya fada yana jan ta jikin sa. Rumgumar da ya sabai mata ita yai mata. Amman yau ko gezau ta kasa yin shiru.

Wannan yasa yasan akwai abun da ke damun Ja'adar ta sa sosai. Sun jima a haka sanna ta samu ta daina kukan.

Wanda shi kan sa Jawad karfin hali yake kawai da tini shima kukan ya fito amman idon sa sosai ya kawo ruwa.
"Honey Jyyy tafiyaa zakai ka ka bar ni..."

Ajiyar zuciya ya sauke. Ya ce,
"Ba barin ki zan ba. Zan tafi ne amman kina nan!"

Ya nuna zuciyar sa. Baza ki taba barin cikin zuciya ta ba sai dai mutuwa nai. Ja'ada ki daina tada hankalin ki kina son na bijirewa su Momy ne. Lallai in har bakya son tafiyar nan wallahi bazan yi ta ba."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon