99-100

745 61 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Thursday
13/March/2019
99-100




Karfe hudu da kwata suka karasa asibitin. Zuwan su komai yai dai dai da zuwan su Dadyn Jawad tare da Momyn sa da kuma yayun sa mata.

Anan suka tsaya matan suka kara gaisa. Momy tayiwa Momyn Jawad introducing din su Mamah da Momyn Izeedeen. Nan suka kara gaisawar

Bayan su Dady suka bi. Dakin Jawad suka kara komawa. A lokacin yana ta bacci sai numfashi da yake fitar wa ta cikin oxygen.

Har ya rame. Sun jima a gun sannan suka tafi dakin Ja'ada. Sameerah na ganin su Mamah ta mike tayi jikin Mamah.

Rumgume ta Mamah tayi tana shafa bayan ta. Tana fadin
"Allah miki albarka."

Nusaiba kuma gun Momyn Jawad tayi. Ja'ada na dai kwance. Dadyn Jawad ne ya ce,
"Wai baccin nan da suke tayi da?"

"An musu allurar bacci ne!"
Sameerah ta fada.

"Ok ina Dr dake duba ta."
"Yana office din shi."

"Bari naje!"
ya juya Dady da Dad suka bi bayan sa.

Su Momyn Jawad suka matsa gefen Ja'ada suna kallon ta. Momy har da yi mata tofi lokaci daya taji yarinyar ta shiga ran ta.

A gun Doctor Dadyn Jawad da ya tambaye shi jikin Ja'ada sai da ya kalle su daya bayan daya yaga ba Abbah sannan yace
"Toh jikin ta Alhamdulilah zance. Sai dai jinin ta da yai mugun hawa wanda kuma ya shafi zuciyar ta, da ta ke da ciwo wanda hawan da jinin ta yayi shine babbar matsala a gaskiya dan sai dai ta tashi zamuga in ba wata matsala dan mostly daga haka zakaga sai ciwom barin jiki. But muyi ta mata addu'a Allah yasa ta tashi lpy.  A bangaren zuciyar ta kam ina zaton sai kun nemi Dr Fauwaz dan shine babban likitan zuciya dake a kasar nan sai dai yanzu haka baya kasar ya tafi wani course a can kasar waje. Ina ganin sai an fita waje da ita taga wannan kwararen likitan akan matsalar dan abun ya ci jikin ta. Sannan kunsa zuciya ba abun wasa bace."

Tin da ya fara magana jikin su Dady yai sanyi. Sosai tausayin ta ya kamasu yarinya karama tana dauke da wannan ciwukan.

Da kyar Dadyn Jawad ya ce,
"To Doctor ya kake ganin za ayi."

"Eh dole, mu bari muga yadda zata tashi kan musan wane treatment xamu fara bata."

Kai Dad ya gyada ya ce,
"Please Doctor ka kula da ita sosai kaji."

"Insha Allahu!"
"Nagode!"

Suka mike suka fita. Jikin Dadyn Jawad ne ya yi sanyi sosai dan bai sani ba ko shima Jawad din irin condition din da yake cike kenan.

Dan haka daga nan office din Mustpha ya nufa. Yana shiga Mustpha ya mike yana kara gaishe shi.

Amsawa yayi ya zauna ya ce,
"Zauna man!"

Zama yayi, Kan sa a kasa. Dady ya ce,
"Mustpha yanzu daga wajen Doctorn da ya duba Ja'adatu nake. Ya fadan komai da yake faruwa. Abin da ya daga min hankali kenan. Shine nace nima bari nazo gun ka naji ya jikin Muhammad din dan nasan a halin da yake ciki."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora