NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Monday
21/January/2019
37-38Washe gari da safe a dining ya samu Dad din sa. Zama yayi bayan ya gaisar da shi ya gaida Mami ta amsa.
Izzedeen ya ce,
"Dad akan zance Ja'adatu ne, Dad ina son asan abinyi tinda naga ta fara kulani."Cup din hannun sa Dad ya ajiye sannan ya kalli Izzedeen ya ce,
"Son gaggawa ba abune mai kyau ba, zanje gurin neman auren ka, amman kana bin komai a hankali kamar yadda nake yawan fada maka.""To Dad yaushe zaka je, kar iyayen ta suga kamar ba da gaske nake ba."
"Zan aika Uncle din ka da Amininah Alhj Lawan!""Dad kai fa?"
Izzedeen ya tambaya murya a shagwabe.Dad ya ce,
"Duk wadan nan mutane da zan wakilta Izzedeen sai naje basu isa ba. In kana son dole sai naje ya na iya dole sai inje din."Mami ta ce,
"Ai ni Izzedewn akan yarinyar nan kamar sun asirce min shi. Gaba daya komai nasa Ja'ada, Ja'ada!, Ja'adar da ba son sa take ba."Jikin sa yaji yai sanyi dan me ma yazo ya fadawa Mami yadda Ja'ada ke behaving masa.
Dad ya ce,
"To ke ina ruwan ki. Ke wace wahala ce ban sha akan ki ba. Ki barsu please hajiya."Murmushi tayi ta kalli dan ta ta ce,
"Dad kai dai!"Izzedeen Dad ya kalla ya ce,
"Ni dai abu daya zan fada maka shine ka dogara ga Allah ka rage son yarinyar nan, duk abinda Allah yayi rabon ka ne zai zo ya same ka kaji ko in abu ba rabon ka bane ba zai same ka ba. Ba a son mutum ya tsananta wa kansa tsananin son wani abu a duniya kaji ko?""Nagode Dad!"
Ya mike yayi dakin sa jjiki a sanyaye.Layin Ja'ada ya fara kira kamar yadda ya zata a kashe. Yana rasa dalilin da yasa Ja'ada ke yawan kashe waya.
Wai shi ina zai sa kan sa da son yarinyar nan. Haka yai ta fama da zuviyar sa har akai sallar magariba ya tafi massalaci.
Bayan isha'i ya kira Ja'ada ya samu ta dauka dan kunna wayar kenan.
"Assalamu Alaiku!"
tai masa sallamar nan tata mai tsinka masa jijijoyin jikin sa."Wa'alaikum salm! Ya kike?"
A hankali ta ce,
"Lafiya lou, yaya mutan gidan?"Cikin jin ddi ta tambayi yan gidan su ya amsa mata cike da zumudi da
"Suna lafiya. Yanzu muka gama magana akan za azo tambayar min auren ki!"Kirjin ta ne ya buga.
"Ki sanar da Abbah yaushe za a zo?""Kasan me?"
Ta katse shi."A'ah!"
"Please ka bari na gama bautar kasar nan tukkun na.""Saboda me?"
"Kawai!""Uhmm daman yanzu Mami ta gama ce ke bakya so na sai wahalar mata da yaro kike!"
Shiru Ja'ada tayi a ranta ta ce,
"Tabbas bana son ka Izzedeen!"A fili kuma shiru kawai tayi.
"Kina ji na?"Ya fada.
"Uhm!"
kawai ta ce.Jikin sa ne ya kara sanyi saboda me zai fada mata Mamin sa ta ce, bata son sa.
KAMU SEDANG MEMBACA
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasiLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...