NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Saturday
9/February/2019
47-48"Ok!"
Ta fada a hankali tabi bayan sa.Hannun ta Jawad ya jawo fizge hannun ta tayi ta ce,
"Look ka kula da abinda kake min."Tayi waje kawai ya bita da kallo. Tana fita ta samu Izeedeen can gefen gidan a cikin mota. Cikin motar ta shiga.
Kallon Ja'ada yayi ya ce,
"Waye wanan?""Mijin Sameerah ne!"
"Mijin Sameerah?"
Ya tambaya cikin mamaki.Kai ta gyada masa, ya ce,
"Me tsakanin ku?""Ba komai!"
"Kin tabbata?""Eh!"
Shiru yayi can ya ce,
"Son ki yake dan in ba so ba ba abinda zai sa yayi haka. My princess kin san yana son ki!"Shiru Ja'ada tayi can ta girgiza kai. Ya ce,
"Ina Sameerah?""Asibiti zamuje kai mata abinci fa kazo!"
"oh tana asibit?"Kai ta gyada masa, ya ce,
"Ok ki mata sannu nan da kwana biyu zan zo, dan yanzu flight na jira na.""Allah nuna mana.!"
Kudi ya dauko bandir din 1k guda biyu ya mika mata."Name ne?"
"Ki rike a hannun ki!""Sun yi yawa!"
"Karki damu!""Nagode!"
Ta bude motar ta fita tana masa addu'a.Sai da ya ga shigar ta gidan sannan ya bar wajen.
Jawad kuwa yana shiga sama ya haye ya shiga toilet ya sakarwa kan sa ruwa.
ya jima sai da yaji kiran wayar sa sannan ya fito ya cire kaya ya daura towel.
Wayar ya dauka yaga Sameerah ce,
"Honey J har yanzu ba ku zo ba!""Yanzu na tashi abacci wanka nayi yanzu zamu taho!"
"Ok sai kunxo!"Ta kashe wayar. Shiryawa yayi cikin sky blue din shadda ya saka hula da takalmi bakake. Barin turare yayi ya sauka kasa.
A falo ya samu Ja'ada ta lumshe idon ta kai ya kauda ya danyi gyaran murya.
Ido ta bude da sauri, kallon sa tayi, Sosai yayi kyau dan ba karamin kada mata zuciya yayi ba. Dan ji tayi soyayya sa na kara daga mata hankali.
"Muje!"
Ya fada yana yin gaba bayan sa tabi tana fita ta tadda shi ya fito da mota,Fitowa yayi ya bude mata gefen sa. Shiga tayi ya rufe sannan ya koma ya tada da motar suka ffice.
Suna cikin tafiya yya dan kalle ta ya ce,
"Kinga yadda muka dace kamar kin zama amarya ta!"Kai ta dauke bata ce kala ba, hannun ta yaja ya fara murzawa cikin salon sa wanda ya fara gaifar mata da wani yanayi a jikin ta.
Da sauri ta janye hannun ta tana zabga masa harara. Murmushi yayi ya ce,
"My Ja'ada kenan kin canja fa, yanzu kin koyi rashin kunya ko, ga tsiwa zan yi maganin su ne."
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...