105-106

715 56 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

*Friday*
12/04/2019

105-106

*Juma'at Kareem to all muslim ummah*

*Alhamdulilah! Alhamdulilah!! Alhamdulilah!!!*

Bacci ne ya kuma dauke ta, har karfe sha daya bata tashi ba. Muryoyin da ta fara ji a saman kan ta su suka sa ta saurin bude idanun ta. Tana ganin Mamah zaune a gefen gadon ta zuba mata ido tai saurin mikewa.

"Mamah!"
Ta fada cikin sanyin murya sai kuma kuka. Rumgume ta Mamah tayi tana dan lallashin ta. Izeedeen ta gani tsaye shi da wasu yan mata biyu zaune a gefen sa.

In ba gizo idon ta ke mata ba kusan kamar su daya da yan mata. Dukkan su mikewa sukai suna fadin
"Sannu Anty Ja'ada ya jikin?"

"Da sauki!"
ta fada tana kallon Izeedeen da ya matso gefen gadon yana fadin
"Princess ya jikin?"

"Alhamdulilah!"
Ta fada tana yin kasa da kanta.

"Mamah ina Abbah?"
"Yana waje yanzu zaki ganshi!"

Sameerah ta kalla ta ce,
"Ina Junaid!"

"Yana gun Abbah!"
Mami ta ce,
"Yau kinga Mamahn ki shine ko ki kallen ko?"

Juyawa tayi gefe tana murmushi ta ce,
"Lah Mami ai banganki ba ne! Ina kwana ina Momy!"

Sallamar Momy ita ta katse musu maganar amsawa sukai ta karaso gun Ja'ada da basket tana fadin
"Ashe kin tashi?"

"Eh!"
Basket din ta bude ta fara zuba mata abinci. Mamah ce ta amsa da kanta ta dinga bata abincin har ta koshi ta bata magani ta sha.

Sosai taji dadin ganin Maman ta, can sai ga sallamar su Abbah nan. Kallon ta, ta mai da kansu yana rike da junaid, murmushi ta sakar masa ya ce,
"A'ah kin tashi ashe!"

"Eh Abbah!"
Ta kalli su Dady ta ce,
"Dady ina kwanan ku?"

"Lafiya lou Alhamdulilah ya jikin?"
"Da sauki!"

Kowa sai da yai mata ya jiki sannan Abbah ya ce
"Ya jikin Ja'adatu!"

"Abbah jiki yai sauki."
"Toh Allah kara sauki!"

"Ameen ya hanya?"
"Alhamdulilah!"
Junaid dake hannun sa ne yake ta miko mata hannu sai ta dauke shi. Amsar shi tayi tana fadin
"Kai my boy haka ka kara nauyi."

Duk kowa na dakin ban da Jawad ta rasa me yasa take son ganin shi bayan in yana gu kasa sakewa take, take kuma ta hau tambayar kan ta shin wai an daura auren ta da Izeedeen ne?"

Ranar yinin asibitin akayi. Ji tayi kamar tabi su da zasu tafi gida amman ba hali ita fa zaman asibitin nan har ya ishe ta.

Tin rana sam bata ga Jawad ba har sai da su Mamah suka tafi gaba daya wajen karfe goma sannan ya shigo dakin dauke da leda a hannunsa. A gaban ta ya ajiye ledar sannan ya wuce ban daki.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant