NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Thursday
10/January/201919-20
"Ameen!"
Ta tada kan ta a kasa."Ya akai jiya a isilamiyya sun tsayar da ranar sauka."
"Eh Nan da sati uku!"Gaban sa ne yaji ya fadi wanda har sai da ya dafe. Ja'ada da take kallon sa ta ce,
"Lafiya?"Kai ya gyada ya ce,
"Lafiya llou!""Anya Honey J!"
"Karki damu. Nawa suke so kukai musu.""Dubu ashirin ashirin har da atamfa da hijab da walima da zamuyi da allo."
"Ok anjima zan kawo sai ki kai ke da Kawar ki.""Kai Honey J bai yawa ba!"
"Bayi ba. Mene a cikin dubu arba'in.""To angode Allah saka da alheri Allah ya kara budi."
"Ameen me kike so na walimar ki. Ki rubuta zuwa ending week din nan mai zuwa.""Da wuri haka."
"Eh!""Allah nuna mana."
"Ameen, na bayar ai miki jaka da littafi da biro da handkerchief sai.me kike so na bugawa!"Kai ta girgiza ta ce,
"Haka ma sun isa.""A'ah in da abinda kkike so ki fada."
"A'ah!""Ok sai kayan snack akwai wata mata a bayan layin ku da takewa Momy in zasuyi biki ko suna zan ka mata komai lokaci nayi kawai sai ki amsa. Sai kayan abincin safe na sauka suma duk cikin sati mai zuwa zan kawo. Sai kayan fita wanne kike so"
"Ido ta zubawa Jawad. Ta ce,
"Honey J ai abubuwan sun yi yawa.""Wa ya fada miki?"
Kai ta girgiza ta ce,
"Honey J ni dai sunyi yawa.""Ba ruwan ki!"
Ya fada cikin hade fuska. Shiru tayi tai kasa da kai.Kan ta ya dago ya kura mata ido. Ya ce,
"Kar kiyi kuka!"Kai ta gyada masa. Bari naje zan dawo anjima. Dan zan sanar da mai kayan date din saukar daga nan Dady na nemana."
Ya mike ya ce,
"Kinsan nan da sati uku tafiyar ku ko?"Baki ta turo. Dariya yayi ya ce,
"Yarinya ko da ckul ko babu dole ne ki daina gani na. Gwara ma ki kasance acan din zai fi miki."Ya fita bata gane me yake fadi ba dai amman kuma haka na nufin ko ina day ne zata daina ganin sa.
Sallama yaiwa su Mamah ya ce,
"Zanje na dawo!""Sai ka dawo.!"
Yana fita gida yaje. A falon bako ya samu Dady shi da wani abokin sa Alhaji Mahmud.Gaisawa sukai Alhaji Mahmud ya ce,
"Muhammad baka zumunci ina jin tin da na dawo kusa da ku baka taba zuwa min ba."Kai Jawad ya sosa ya ce,
"Dady zan zo ne."Dady ya ce,
"Gashi kuma zai tafi karatu ba. Ga Momyn ta sa ta sa sharadi ka cewa in dai ya tafi ba dawowa sai ya gama.""Saboda me?"
Alhj Mahmud ya tambaya.

YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...