119-120

775 66 1
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

18/April/2019
Thursday
119-120


Da suka tashi tafiya kuwa sun sha tsaraba ta nono da kwan zabi da kaji duk haka Abbah ya hada musu. kuma Sun musu nasiha sosai tare da kara musu fada akan su zauna lafiya.

Haka Ja'ada ta tafi da kewar su Mamah. Da suka koma suka baje a falon Sameerah aka kawo musu abinci anan suka ci.

Da zata tafi ne ta kalle Jawad ta ce,
"Honey J ka kwana gun My Samee kaga tafiya zatayi!"

Tana kai wa nan ta fice. Kallo Jawad ya bita dashi haka nan Sameerah ma. Dawo da kallon ta tayi kan sa ta ce,
"Honey M ka tashi ka tafi sai da safe!"

"Baki ji me tace bane?"
"Naji amm...."

Yai saurin katse ta da cewa
"A'ah ba inda zani nima zanyi missing naki dan haka ki bari kawai na kasance da ke!"

Shiru tayi Ja'ada na shiga Bangaren ta tayi wanka ta hau kan gado. Kiran Nusaiba ne ya shigo.

Dauka tayi tana fadin
"My Nusy!"

"Na'am Anty nah ya kike ya gida da Honeyn naki?"
"Lafiya kalou Ya Yaya Izeedeen da su Mami, ina son na shigo Abuja ina zo inyiwa su Mami ya gajiya!"

"Gajiyar me?"
"Biki man!"

Dariya Nusaiba tayi ta ce,
"Anty Ja'ada biki wajen wata hudu kike maganar gajiya."

"Eh man! Wallahi ina son nazo naga Mami."
"Yauwah kedai ce haka amman ba wai zakizo ban gajiya ba. Anty Ja'ada ya zaman naku?"

"Ban sani ba, kaji min 'ya"
Dariya Nusaiab tayi tace,
"Kai daga ji Anty Ja'ada ba kisan komai ba har yanzu. Bari na bar ki in kin zama babba na miki maganar abun a lokacin zaki gane!"

"Lah ni kike cewa in na zama babba?"
"A'ah Anty!"

"Ai shikenan bari na kwanta kije ga mijin ki kinji."
Ta fada tana katse wayar.

A ranta tana cewa tayaya zata janyo ra'ayin Honey J gare ta har ya hakura dan taga shi tinda ta ce kada ya kuma zuwa gun nata ya yi fushi.

Haka tai ta saka da warwara. Har bacci a dauke ta.

A bangaren su Honey kuwa sun sha soyayya kamar ba gobe ta bawa Honey M duk abunda yake bukata, sun kwana idon su biyu.

Washe gari gidan su Momy suka je acan suka yini da zasu dawo gida suka biya ta gidan su Jawad

Abu daya ke tsayawa Ja'ada a rai irin yadda Sameerah ke share ta abun ya ishe ta. Dan haka bayan sun dawo ta bita har daki tana hada kaya ta zauna ta ce,
"My Samee!"

Bata dago ba sai dai ta amsa da na'am daga nan ta cigaba da abunda take yi.

"Kiyi hakuri komai nayi ban yi dan na bata miki ba My Samee nayi ne dan son da nake miki da son saka miki da alheri akan abubuwan da kikai min...."
"Kafin nai miki wani abun alheri wa ya farai miki ni ko Hobey J?"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now