*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Sunday
10/March/2019
89-90Su Sameerah na packing mota. Motar su Buhari na shigowa. Kallo suka bisu da shi.
Sameerah kuma ta ce,
"Kamar motar Buhari!""Nima haka na gani!"
Nusaiba ta fada.A hankali Buhari ya bude kofar motar ya fito Mustapha ma ya fito.
Ido ta zaro tana mamakin me ya faru wata zuciyar kuma ta ce,
"Daurin aure suka zo!"Ajiyar zuciya ta sauke. Ja'ada kuwa bugun zuciyar ta ne ya dadu.
A hankali suka karasa wajen su. Sameerah ta ce,
"Ina kwanan ku?""Lafiya lou!"
Buhari ya amsa Mustapha kuma ya jingina dda motar su Sameerah da suka fito a lokacin"Daman Muhammad ne bashi da lafiya!"
Kirji Ja'ada da Sameerah suka dage. Bakin su a hade suka ce
"Yana ina?""Yana Asibitin Musty!"
Mota Sameerah ta nufa da sauri Ja'ada ta biye mata baya haka ma Nusaiba.Da gudu suka bar gidan su Mustapha suka rufa musu baya.
Izeedeen da suke tafe a mota shi da abokan sa yaga wucewar motar gidan su Sameerah a guje kuma in idon sa bai masa karya ba Ja'ada ya gani a ciki.
Da sauri ya ce,
"Marzuk bi min motar can!"Marzuk ya bi su shima a guje. A mota kuwa Mustapha cewa yayi
"kace kasan inda yarinyar take muje toh!""Kai dai ka tsaya muje man."
"Kar fa a daura auren! Wai kai baka san a irin halin da yake ciki bane. Ya xanyi in na rasa Muhammad ehhe?"Kai ya dauke ya cigaba da tuki dan yaga ne sam Mustapha bai cikin hankalin sa.
Mota uku ne suka zuba a guje har cikin asibitin a cikin motar su Sameerah kuwa kuka take sosai tana tuki.
Ja'ada kuwa zaune take a gefen ta, ta rasa meke mata dadi dan ba komai take ganewa ba.
Haka suka karasa da sauri suka fito daga cikin mota. Gudu gudu sauri sauri suka karasa office din Mustapha.
Su Mustpaha ma da saurin suka rufa musu baya haka nan izeedeen da Marzuk.
Tsaye su kayi ganin likitoci akan Jawad. Mustapha na shigowa yayi kan su yana tambayar su
"ya akayi ne?"Daya daga cikin sune ya dago ya ce,
"Dr a gaskiya abun ba dadi ji ku samar masa abinda yake so in ba haka ba tabbas sai dai wani ikon Allahn amman tabbas zai iya rasa rayuwar sa."Jikin su ne yai sanyi gaba dayan su. Kukan sameerah ya tsanan ta. Haka Nusaiba Hawaye kawai take yi
Ja'ada kuwa kukan yaki ya fito ma ta zuba masa ido yana kwance kawai. Ita kan ta jikin ta wani irin sanyi yayi kirjin ta na dada bugawa.
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
ŞİMDİ OKUDUĞUN
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantastikLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...