111-112

621 50 1
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Sunday
14/4/2019
111-112


A bakin Hall din suka hadu Mami da Jawad da sameerah a gefen ta, sai Jawad da Izeedeen a bayan ta suka shiga nan masu pictures da vedio suka fara daukar su.

Tsayawa sukai kowa yayi gefen matar sa aka dauke su

Mami da kan ta, ta kai su gun zaman su, sannan aka saki kida yan mata da yan uwa suka fara shan rawa.

Ansha shagali anyi hutuna da yan uwa an ci an sha. Haka nan Sameerah sai bajin ta take.

Ja'ada kuwa tana zaune sam bata jin dadin wajen ita gida kawai ta son taje ta huta.

Su Nusaiba da Izeedeen sai hirar su suke amman sam Ja'ada taki ta sake bare suyi hirar.

Da gayya Sameerah tazo ta saka su murmushi sai ka zata wata magana suke. Haka nan ta dauko hannun Ja'ada ta Daura akan hannun Jawad.

Dagowa tayi ta kalli Sameerah.
"Honay M ku na danyin hira mana. Haba Man!"

Baki Ja'ada ta turo,
"Please saboda idon mutane kawai please! Ku tuno da soyayyar ku ta baya man. Ja'adatun ka ce fa! Ke kuma Hobey J din kine. Kusan dukkan ku nasan kuna son junan ku to please feel free, kuma kema My Adat akwai ta mu, but Please yanzu dai ku sake please ku tuna baya!"

Tana gama magana ta bar wajen kallon kallo suka fara yi suna tuno duk rayuwar su ta baya a bar burgewa da sha'awa. Masu yi musu pictures sai dauka suke yi.

"My Ja'adat!"
Ya fada yana kamo hannun ta.

"Na'am!"
Ta iya fadi kawai take kwalla ta taru a idon ta.

Kai ya girgiza mata ya ce,
"Please don't cry!"

Kai ta gyada masa. Mami ce ta karaso ta kamo hannun Ja'ada tayi gefen Nusaiba ma ta kamo hannun ta.

Tsakiyar fili suka fito mai daukar pictures ya dauke su. Mami wayayiya ce dan haka aka sakar musu kida nan ta hau rawa tana juya hannayen su. Nan fili ya kaure ana ta musu liki.

Sai karfe sha daya aka tashi aka debe kowa akai gida dashi. Haka Mami ta kuma dibar amare suka tafi gida abinsu.

Suna komawa akai sallah aka kwanta dan an gaji sosai.

Tin da suka kwanta sai asuba da kyar suka tashi. Shima sallah sukai suka koma bama Ja'adatu da tafi kowa jin ta gaji.

Ba ita ya tashi ba sai.karfe goma duk da ita ba ma abociyar bacci ba ce.

Kowa yai wanka har an fara shirin tafiya kai Nusaiba dake Abuja a jirgi zasu dan haka sai an kai ta za a kai Ja'adatu.

Wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya. A zaune ta samu Nusaiba ta yi kwalliya ta zuba tagumi.

"Ya ne Kanwata?"
Murmushin Karfin Hali Nusaiba tayi ta ce,
"Anty wallahi I will miss u gashi garin ba kusa ba."

Dariya Ja'adatu tayi ta ce,
"Kaji ki ga waya nan. sannan ai ana tare kar ki damu kinji!"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Onde histórias criam vida. Descubra agora