103-104

694 58 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Friday
15/March/2019
103-104



Jawad na ganin haka ya fadi agun da sauri Nurse sukayi kan sa. Aka fita dashi daga dakin.

Su Dady da su Momy kuwa duk hankalin su ne ya tashi Sameerah ma sai kuka take, fitowar Doctor Fauwaz ita ta sa suka yo kan sa gaba daya.

Dad din Izeedeen ya ce,
"Doctor lafiya?"

Kwallar idon sa Fauwaz ya goge dan shima tabbas ya jiwa mutuwar Ja'adatu dan bai taba kallan wata mara lafiya da ta shiga ran sa kamar Ja'adatu ba duk da tinda tazo tana kwance kamar gawa amman yaji ta kwanta masa haka kuma mijin ta yana bashi tausayi tinda ya zo kullum yana kan sallaya ko yana mata karatun al kur'ani.

"Sai dai kuyi hakuri!"
Ya fada yana goge idon sa da gumin dake zubo masa.

A gun Sameerah ta zube ita ma nan yasa aka dauke ta. Su Mami da Momy da su Dady kam kasa magana sukai duk jiki a sanyaye suka bishi da ido da ya fara tafiya.


A can gida Nigeria ma Mamah na kwance bacci ya dauke ta daga kan sallayar da take ta mike a firgice tana yin salati. Can kuma sai da fashe da kuka. Abbah dake zaune a gefen ta ne yayo gun ta yana fadin
"Lafiya?"

"Abbahn Ja'ada ni dai ka kai ni naga Ja'ada dan jikin na yana bani Ja'ada ba tashi zatai ba, ka kai ni naga 'ya ta dan Allah nayi mafarki wai Ja'adatu ta mutu kum...."
kuka ne ya ci karfin ta ta kasa karasa maganar da take yi,

"Haba Mamahn Ja'ada sai kace baki da sani ai mafarki ba gaske bane da mafarki gaske da bayan tashin ko farkawar ka wani ba zaka kara magana bare yin wani abu ba saboda fargabar abinda zaka gani. Dan Allah ki kwantar da hankalin ki kuma Ja'adatu da muna gun ta da bama gun ta ba abinda zamu iya mata dan haka dan Allah ki cigaba da Addu'a ita ce kadai abinda muke damar yi kuma kar mu gajiya iinsha Allahu zata tashi lafiya da izinin manzon Allah (SAW) kinji!"

Kai ta gyada tana goge hawaye tana fadin
"Naji amman dan Allah ka kai ni naga 'ya ta dan Allah!"

"Zan kai ki amman sai kin cire damuwa."
Mamah kamar karamar yarinya take fadin
"Wallahi Abbah na cire kaji ka kai ni."

Dan murmushi yayi ya ce,
"Toh Mamahn Ja'adatu, sai kin aurar da jikan ki na gun Ja'adatu insha Allahu to kinga kuwa ai mutuwar ta ba yanzu ba da izinin Allah!"

"Allah ya yadda."
"Ameen!"

Ta mike ta shiga bandaki ta kara dauro alwala ta hau kan sallaya Abbah dake xaune ya ce,
"Bazaki kwanta ba!"

"Kai ta gyada ta ce bari nakai kuka na ga Rabil samawati wal arda."
Murmushi yayi ya ce,
"Allah ya amsa!"

"Ameen!"



A dai dai wannan lokacin ne naurar dake aiki hade da jikin Ja'ada tayi kara alamar bata mutu ba da numfashi dake fita a jikin ta.

Wata nurse dake tsaye akan ta ta gani da gudu ta fita a dakin tana kwadawa Doctor Fauwaz kira da har zai fita daga asibitin. Juyowa yayi ta ce,
"Sir she is alive!"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin