*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
*Monday*
15/April/2019
113-114Hannu bibbiyu su Momyn Jawad suka amshe ta aka basu amana sannan sukai musu addu'ar zama lafiya. Daga nan kuma akayo gidan ta da ita.
Bangaren ta yana a gyare sai tashin kamshi yake an zuba mata tsadadun kaya masu kyau da tsada dan ko a ido kayan abun kalla ne, sun yi kyau har sun gaji da shi.
A babban Falo Red kujeru aka saka wanda ba karami kara fito da kyau da girman dakin yai ba.
Da yake katon falo ne sai akai mata jere a tsakiya wato aka saka kujerun a tsakiyar falon yadda girma zai rago a ido.
Bed rokm din kasan ma haka aka saka masa red komai har kitchen nata na kasa.
Sai falon sama da aka zzuba mata pink kalar furniture labulaue purher pink. Dakin sosai yai kyau.
Sai bedroom din ta da aka zuba mata pink kalar kaya da labulaye zanin gado center karfet da komai. Dakin sai kamshi yake.
Anan aka ajiye amarya. Dakin Jawad kuma farare mai ratsin Baki aka zuba masa zubin arabi'an kujeru wanda zaka gansu a dab da kasa. Shima dakin sa yai kyau sai dayan dakunan aka sakawa dayan milk kaya dayan kuma pink nd blue kala.
Gida yayi kyau haka nan an kashe dukiya a cikin sa. A gefen gadon ta suka zaunar da ita aka mata bankwana da zazu tafi tai ta kuka.
Anan ma da kyar Mami ta kubuce mata dan cewa tayi sai Mami ta zauna mata. Sai da akai mata wayo sannan ta kyale Mami ta fita.
Sai bayan tafiyar su Mami da Momy sannan Sameerah da kawayen Ja'ada suka shigo su suka dan debe mata kewa. Dan har dare suna tare.
Karfe takwas Jawad ya dawo gidan sa da a yau zasu tare gaba daya da mai gidan wato Ja'ada dan yace nan gidan nata ne ita ce silar fara yin sa ita zata fara shigar sa.
Bangaren Sameerah ya shiga bata nan dan haka dakin sa ya shiga yai wanka bayan ya fito ne ya kira ta a waya. Ce masa tayi gata nan zuwa.
Dan tana garden din ta tana shirya wajen dan ta ce dole tayi nata walimar ta taya Adat din ta samun Honey J din ta.
Tayi kwalliya abun ta daga nan part din Ja'ada ta shiga. Tana zaune akan sallaya kawayen ta na gefen ta.
Ban daki ta shiga kawai ta hada mata ruwa ta fito ta ce,
"Kije kiyi wanka ke muke jira!"Ko kallon ta batai ba.
"Dan Allah!"Ta fada a marairaice mikewa tayi ba tare da ta kalli ta ba ta shiga ban dakin. Ledar da ta shiga da ita tin rana ta dauko ta zube mata kayan da zata saka wata dakakiyar shadda ce pink kala wacce akaiwa aiki da blue kala sosai tayi kyau.
Daya daga cikin kawayane Ja'ada ta ce in ta fito tai mata kwalliya gata nan zuwa.
Fita tayi ta nufi part din ta mai ta tadda shi yana shafawa dan haka ta karasa tana taya sa.
STAI LEGGENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...