NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
61-62
Ido Sameerah ta zuba wa Ja'ada can ta ce,
"Zan takurawa Honey M ya fadan wacce yake sso ko gun iyayen ta ne zan iya zuwa dan na fada musu halin da Yake cikun."Wani yawu Ja'ada ta hadiye sannan ta ce,
"Allah dai ya shige gaba.""Ameen!"
ta koma ta kwanta.A garin jigawa kuwa sai bayan tafiyar Jawad Abbah yake fadawa Mamah abinda ya faru.
Sosai Mamah ta tausayawa yar ta dan ga wanda take zaman jira amman sai yanzu da bakin alkalami ya bushe sannan ya bayyana.
Tabbas ba zata fadawa Ja'ada ba dan zata kara tada hankalin ta ne.
Abbah, Mamah ta kalla ta ce,
"Amman dai Abbahn Ja'ada kar a fadawa Ja'ada abinda ya faru.""Nima haka na gani. Dan dai na amshi kudin sadakin ta ne amman da na fasa dan dai ba dadi ne kawai. Amman nafi so wa Ja'ada auren Jawad!"
"Nima dai wallahi.""To Allah ya zaba abinda yake mafi alheri. Allah daura mata abinda zata iya da mu ma gaba dayan mu."
Sukai shiru can Mamah ta ce,
"Abbahn Ja'ada kasan jiya kuwa mafarkin Yaya nayi."Mikewa Abbah yayi ya ce,
"Uhmm Ke dai Amina da son daukin abinda zai sa min bacin rai kike da damuwa."Mikewa ita ma tayi ta ce,
"Kayi hakuri bazan so bacin ranka ba. Kasan bana so kuma bana ka kawo maka maganar kawai dai mafarkin da nayi ne ya tsayan aa rai amman kayi hakuri.""Ba komai bari na tafi kar na makara!"
"To a dawo lafiya Allah ya bada sa'a Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya.""Ameen!"
Ya fita tana daga masa hannu yana daga mata hannu,A asibiti kuwa Jawad sai kusan goma sha biyu ya farka. Mustapha ne ya taimaka masa ya kai shi ban daki yai wanka sannan ya bashi wasu extra kayan sa dake office din sa.
Sallah yayi sanna Mustapha ya fita yaje gidan sa dake cikin asibitin ya amso masa abinci da ruwan tea.
Tea ya fara hada masa ya sha ssannan ya bashi abinci ya ci, sai da ya gama ya bashi magani ya sha.
"Ya jikin naka?"
Mustapha ya tambaya"Alhamdulilah!"
ya fada yana daukar wayar sa. Gallery ya shiga ya budo pictures din Ja'ada tin lokacin da sukai sallama da zai bar kasar.Ido ya lunshe hawaye na zubo masa. Kallon sa Mustapha yayi ya ce,
"Muhammad meke damun ka haka wai?"Ajiyar zuciya ya sauke ya dago ya kalli Mustapha. Mustapha ya ce,
"Eh kar kace ba abinda ke damun ka dan kana da damuwa."Dan murmushi Yayi tare da cije leben kasa sanna ya ce,
"Haka ne ina da damuwa, sannan damuwa ta tana ban wahala sosai. Ina rokan ka ka sani a addu'a Allah yaya ye min damuwa ta hanyar bani abinda nake ao. Dan samun abun shine kadai cirewar damuwa ta daga zuciya ta. Allah ya sa dani da maganin damuwa ta shine alheri a gare ni!"Sosai Mustapha ya tausayawa abokin nasa. Dan har kwalla ta zubo masa ya dan share ta ya ce,
"Kai dai nasan ba soyayya ce ta saka ka a wannan halin ba ko?"
ESTÁS LEYENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasíaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...