NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Friday
15/February/2019
59-60*Juma'at Kareem*
Tashin hankalin Sameerah daya ne shine kwana su hudu ba waya daga Jawad kuma ya dauke kafar sa. duk ta damu.
Haka suka kara kwana biyu duk jikin su a sanyaye dan ma sun samu baki kanin Dady da baya kasar sun zo har da ya'yan sa kuma ya'yan a gidan suka sauka.
Bayan tafiyar su kuma sai ga Nusaiba nan yar yayar Jawad tazo ita ma mai sunan Momyn su Jawad. Dan Ja'ada tazo dan tin da taga Ja'ada take jin wani abu game da ita kawai taji tana son ta.
Zuwan ta shi ya rage musu damuwar su suka baje ana ta hira. Suna zaune wayar Ja'ada tai kara. Dubawa tayi taga Izedeen dagawa tayi da sallama.
"Asaalamu Alaikum!"Sai da ya sauke aajiyar zuciya sanna ya amsa da
"Wa'alaukm salam my princess.""Ya kake?"
"Lafiya Alhamdulilah kin ganni a kano nazo wani aiki ya yanzu zan juya nace sai nazo naga my princess.""To ka kakaraso ne?"
"A'ah ina hanya!""Sai ka karaso toh!"
Ta kaste wayar tana lumshe Ido."Angln ne?"
Kai ta gyadawa Sameerah. Nusaiba ta ce,
"Wai Anty ke ma auren zakiyi har ina ce a nai wa bro kamu."Dariya Ja'ada tayi Sameeraah ta mike ta shiga zabo mata kayan da zata sa. Kallon ta Ja'ada tayi Sameerah ta ce,
"Ta shi ki shirya maza kan yazo.""Kai My Samee?"
"Allah sai kkin sa."haka ta saka ba dan ta so Ba tayi kyau sosai da ita. Sai kace mai zuwa unguwa sai tashin kamshi take.
Yayo mata waya yana bakin gidan kenan aka kira Nusaiba Driver yazo daukar ta dan haka tare suka fita.Sai da suka gaisa da Nusaiba kasnacewar ta akawai surutu da barkwanci shima haka yasa suka tsaya ana tayi a waje. Sun yi awa daaya sannan tai musu sallamma.
Da suka shiga lemo kawai y iya sha ya ce zai tafi dan yamma zatai masa. Haka ta fito ta raka shi ya tafi.
Sameerah kuwa ganin yau kwana shida kenan rabon ta da Jawad gashi ko wayar sa in ta kira a kashe wannan ya tada hankalin ta.
Cikin tashin hankali ta fadawa Momy abinda ke faruwa. Momy ta ce,
"Kije gida kiga ko lafiya."Haka kuwa akayi ta shirya ita da Ja'ada suka nufi gidan nasa. Duk motocin suna gida abinda ya dagawa Sameerah hankali kenan.
A falo Ja'ada ta zauna, Sameerah kuma tayi sama. Tana shiga dakin sa ta hange sa a cikin bargo sai karkarwa yake yi.
Hankalin ta ne ya tashi lokacin da ta taba jikin sa taji yai zafi zau.
"Honey M baka da lafiya kuma baka fada min ba."Dagowa yayi da kyaar ya ce,
"My wife yaushe kika zo?"Kai daga jin maganar sa kasan yana jin jiki. Bata amsa masa ba sai cewa tayi,
"Honey M baka da lafiya ne tashi mu tafi asibiti a duba ka,"Kai ya girgiza ya ce
"Kar ki damu zazzabi ne kawai"Kuka Sameerah ta sa masa dan tasan halin sa tsab zai ce bai zuwa ganin in har bai yadda ba zata kara masa wani ciwon yasanya ce,
"Daukon kaya na."
ESTÁS LEYENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasíaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...