131-132

886 57 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Tuesday
22/April/2019
131-132




Shi yai mata wanka ya fito da ita ya shafa mata mai. Ya saka mata wani tissue material lemon green and milk. Sannan suka nufi Falo inda Sameerah ta jere musu kayan abincin su.

Kallon sa tayi ta ce,
"Honey ya dai My Samee ce tayi ba."

"Ita ce menene!"
"Da ka bari na tashi nayi ka sata wahala."

"Ke da bakya jin dadi!"
"Ni lafiya ta kalou!"

Hararar ta yayi ya ce,
"Koh?"

Ta gyada kai ya ce,
"Bafa yadda da wayon ki zan ba sai na kai ki asibiti "

Baki ta turo tana make kafada. ya ce,
"Kyayi kya gama!"

Ya hada mata abincin da kasan ya bata taci ta koshi sannan tayi feeding nasa. Sai da suka gama suka nufi part din Sameerah tana ganin su ta ce,
"A'ah me jikin ce? Ai yanzu nake cewa bari nazo naga ko ta tashi!"

Murmushi Ja'ada tayi ta ce,
"Honey J ne fa da abinsa wai daga na dan kwanta da zazzabi fa!"

"Ayyah sannu. Ko dai Za ai wa junaid kani ko kanwa ne?"
"Ke amman ko?"

Ja'ada ta fada. Sameeeah ta ce,
"Ki tausayawa Boy din naki man ya kara kwari ko. Ke dai!"

"Au wai menene bakwa son ku haihun ne. To daga ta sauke wannan tare zaku na diba kuna saukewa after one-one year nake so kuma. So nake nan da five years ya zamo ina da kids sun kai goma!"

Kallon sa suke Ja'ada ta ce,
"Kai Honey J sai kace me?"

Sameerah ta ce,
"Kyalle shi dai so yake mu tsofa!"

"Oh haka kuka ce. Shikenan zan nemo yan mata guda biyu su sai su haifa min!"
ai bai rufe baki ba duk suka yi gun sa suna fadin
"Akan me?"

Kallon su yayi ya dan bata fuska ya ce,
"Akan ina son ya'ya ku kun ce bakwa so. Kunga kwara na samu masu so ko?"

"A'ah muna so!"
Suka fada a tare.

"Da gaske!"
Ya tambaye su. Kai suka gyada masa yai murmushi ya juyar wa da kowa side face nasa tai masa kiss.

Zama sukai Sameerah ta kalle shi ta ce,
"My Oga na fa shirya!!

"Tin yanzu!"
"Eh tafiyar mota nake so nayi. Ina son naga hanya!"

"Ina zaki ki barni!"
"Wai Abuja zata je!"
Jawad ya bata amsa.

"Zamu je dai!"
ta bashi amsa.

"Kin ma isa a bar Honey M din dawa kenan?"
Sameerah ta fada.

"Shi kadai!"
Ja'ada ta bata amsa.

"Ban yadda ba!"
Inji sameerah.

"Kai My Samee please zan biki."
"A'ah fa. Ki zauna ki kular mana da shi next kyaje in ina nan so kike muna barin shi a gida ya karo aure kina dai jin sa ko?"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon