Part 7-8 (Muhammad Jawad)

1K 104 1
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*


*Bismillahi Rahamanir Rahim*

*FRIDAY*
'''Juma'at Mubarak to all muslim. Allah sadamu da. Alheran sa Ameen!'''

4/January/2018.
7-8

Sai da Dady ya lallashi Momy sannan suka sauko suna hira abin su. Jawad na gama break suka mike suka fita shi da Dady.

Kamfanin Dady dake Sharada suka je, suna duba yanayin aikin. Har karfe sha biyu suna can basu da shirin tahowa.

Jawad da yake son ya je taro Ja'ada duk ya kosa ganin Dady na da sauran aiki yasa ya mike ya ce,
"Dady a ban aron key zan je na dawo."

"Ina zaka?"
Kai ya dan sosa ya ce,
"Zan je naga wannan Babyn ko ta dawo ne."

Dariya Dady yayi ya ce
"Jawad kenan kaje ka dawo muyi maganar ta."

"Toh Dad!"
ya dau key din ya fita.

Kofar gate din su ya karasa dai dai karfe daya, lokacin aka tashe su duk sun fito kamar me yawan su kuwa ba za su lissafu ba.

Duk da haka bai sa ya kasa gane Ja'ada a cikin su bba. Dan ta fita da ban tafiyar ta, tsaftar ta, kyan ta, yanayin ta.

Da sauri ya tsallako ya bi bayan ta.
"Baby!"

Ya kira ta. Dan juyowa tayi ta de,
"Lah kai ne?"

Shima ya kwaiwayi muryar ta, ya ce,
"Lah kece?

Sai suka saka dariya. Ya ce,
"Ya makarantar?"

"Lafiya kai fa?"
"Ni bana karatu yanzu. Na gama. Ckul last two year to ina hutawa ne."

"Au wai in an gama makaranta har wani hutawa ake kan a fara wata."
"A'ah ya dangata ga mutum da ra'ayin sa a nawa ra'ayin ina son na dan huta na shekara uku zuwa biyu, tin ina shekara uku fa nake karatu ya kamata a dan huta."

Shiru tayi dan ita ba zata ce ga abinda tta fahimta ba ma. Ya ce,
"Ajin ki nawa ne?"

"Biyar!"
Ta bashi amsa.
"Wow ashe kin kusa shiga JS."

"Eh!"
To kina dai karatun ko?"

Kai ta gyada masa. Har kofar gida suka je, yau ma ta ce,
"Bana fadawa Mamah kazo."

Ta shiga dda sallama. Mamah ta ce,
"Wa'alaikum salam!"

Ta shiga ta ce,
"Mamah barka da gida"

"Yauwah Ja'adatu ya makarantar?"
"Alhamdulilah!  Mamah yau ma tare da Yaya Jawad muke bari nai masa magana ya shigo."

Ta mike ta fita.
"Ka shigo ta fada masa."

Bayan ta yabi suka shiga har Falon Mamah. anan ya zauna suka gaisa da Mamah.

Ja'ada kuma ta shiga dakin Mamah ta cire kaya ta daura zani ta sa hijab ta shiga bandaki tayo wanka.

Dakin Mamah ta koma ta saka wani material dinkin doguwar riga da yai dai dai da jikin ta. Kalbar kan ta guda biyu da Mamah tai mata ta zubo a kafadun ta zuwa bayan ta.

Hijab ta ssaka tai sallah sannan ta nufi Falo, a can ta tadda har Mamah ta kai wa Jawad abinci, shinkafa da wake ne da salad da tumar da gurji da mai da yaji.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon