part 63-64

664 59 2
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Sunday
17/February/2019
63-64



Momy ce zaune a falon sama, tana jiran fitowar Dady. Yana fitowa ya bita da kallo ya karasa gefen ta ya ce,
"Amman fa kinyi kyau kedai benu ce bakya tsofa."

Dariya Momy ta yi ta ce,
"Kai ma haka. Ina tare da kai ai ban tsofa."

Sukai dariya. Ya ce,
"Da magana kenan na ganki zaune anan."

"Eh Daman Muhammad ne ba lafiya, shine nace gwara matar sa ta koma dakin ta ta cigaba da kula da shi."
"Subhanallah, me yake damun sa."

"Sunce dai jiya zazabine a jikin sa a gun Mustapha ma ya kwana shiyasa tin safe na sa ta fara hada kaya ta ajima ta koma dakin ta."
"Hakan na da kyau. Zan je na duba shi kuma Mahaifin nasa bai fada min ba."

"Ba sai sun fada musu ba."
"Allah ya kyauta wa shiriritar yaran nan."

"Ameen!"
Suka sauka kasa.

A falo suka samu su Sameerah da Ja'ada, bayan sun gaisa suka hau dining gaba dayan su aka karya. Sai da suka gama sannan Dady ya ce,
"Sameerah yau zaki koma dakin ki dan ki cigaba da kula da mijin ki."

Kai a kasa ta ce,
"Toh Dady nagode amman dai tare da Ja'ada zamu tafi ko?"

Ja'ada a ranta sam bata son ta bisu amman Kuma tasan su Dady cewa zasu yi ta bita ko dan kula da yaron kuma zata fi sakewa da Sameerah.

Momy ta ce,
"In tana so ai sai ta biki in kuma anan zata zauna shikenan."

"Momy Ja'adatu ma zata so bina, sai dai in ku zaku hana min ita."
"To shikenan yanzu kuje can gidan ku kintsa ajima sai kuje gun sa tinda yana gun abokin nasa."

"To Momy!"
suka mike. Basu dau komai ba suka tafi can gidan Samerrah. nan suka hau gyara duk da gidan bai wani datti ba dan ana gyara shi.

Sai karfe daya suka gama suka daura abinck. Sai da suka gama sannan suka haye sama sukai wanka sukai sallah.

Mikewa Sameerah tayi ta ce,
"Muje muci abinci mu tafi asibitin ko?"

Suka sauka kasa sunci abinci sannan suka dauko mayafai da na Muhammad suka fita.

Driver shi ya tuka su, har asibiti suna zuwa su Muhammad na dawowa daga massalaci.

Da fara'a akan fuskar su suka tarbe su Muhammad ya dauki dan sa yana fadin,
"Boy idon ka biyu!"

Ya kalli Sameerah wacce tayi kyau ta ce,
"Ah Hobey M jiki yai kyau."

Ya ce,
"Wallahi kam Alhamdulilah!"

Ya kalli Ja'ada wacce ba kwalliya tai ba doguwar bakar riga ce a jikin ta ta yafa purple mayafi da takalmi kawai. Ganin sun hada ido yasa taji kirjin ta ya buga da karfi. Cikin sanyin murya ta ce,
"Ya jikin?"

"Alhamdulilah!"
ta kalli Mustapha da ya zuba mata ido ta ce,
"Sannu ina yini?"

"Lafiya mu karasa ciki ko?"
Suka yi ciki kai tsaye office din sa suka nufa, shi kuma ya fice dan zuwa yaga mai ke faruwa a asibitin.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt