*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Monday
22/April/2019
129-130Kan gadon ya karasa da sauri yana dago ta. Tana ganin sa ta fada jikin sa tana kara sakin wani kukan mai tsuma zuciya.
Rumgume ta yayi tsam a jikin sa yana shafa bayan ta a hankali a hankali, ta jima tana kukan ganin ba zata daina kukan ba yasa ya dago fuskar ta bakin su ya hade waje daya.
Tsit kaji ta sai dai idon ta da ya ke zub da ruwa. Sun jima a haka sannan ya zare bakin sa daga nata. Kallon ta yayi ya ce,
"Menene?"Kai ta hau girgizawa. Fuska ya dan bata ya ce,
"Ban gane ba! Menene na tambaye ki kina girgiza min kai."Kuka ta saka masa ya bita da kallo ya ce,
"To baza ki fada min ba!"Kai ta gyada janyo ta jikin sa yayi yana fadin
"Saboda me to?"Nan ma ta girgiza kai.
"kin san dai ina sonki ko?"Kai ta gyada ya ce,
"Son da nake miki bazai taba bari na ganki a wannan halin hankali na ya kwanta ba. Ki fadan wa ya taban ke!"Kai ta make. Ya ce,
"Shikenan ina Sameerahn da ku ka fita tare?"Sai a lokacin, ta tuna ta taho ma ta bar ta acan. Zatai magana kenan aka budo dakin aka shigo.
A yadda ta gansu sai da taji zuciyar ta tadan tabu amman sai ta maze ta karaso dakin. Kai suka dago suna kallon ta.
Ja'ada ce ta fara kokarin barin jikin sa amman yaki sakar ta. Sai ma hawayen da yake goge mata yana fadin
"Me akai mata, ta ki ta fada min sai kuka da ta shigo tana yi!"Kallon Sameerah, Ja'ada take tana girgiza mata kai alamar kar ta fada. Bakin gadon ta samu ta zauna ta ce,
"Wallahi su Sadiya da Farida da Hajara ne daga ganin mu tare suka fara wata magana akan ta. ni kai na sun batan rai!""Menene hurumin su da ita to?"
Ya fada ran sa bace."Ai nayi maganin su. Dan har na taho sun kasa magana. Sai da da xan taho na lura da ashe bata dakin."
"Me suka fada akan ta!""Ni sukeyiwa wai na bari ta auren miji!"
Mikewa yayi ya ce,
"Ki ja musu kunne duk wacce ta kuma saka ta zubar da hawaye wallahi sai na saka an kulle ta. Daman kada in soma ganin kafar su a cikin gida na!"Ya juya ya fita. Ja'ada ta mai da kallon ta ga Sameerah ta ce,
"Meyasa kika fada masa!""To me yasa ki kuka in ban fada masa ba."
Shiru tayi.Sameerah ta ce,
"Kiyi hakuri da na san abinda zzai faru kenan da ba zamu ba ma kinji.""Ba komai My samee. Ni dai tsoro nake kar wata rana ki canja ban san ya zanyi ba."
Dan hararar ta Sameerah tayi ta ce,
"Ba wata canjawa da zan yi ko dan ke kin canja min a baya shine nima sai na canja miki."Kai ta girgiza. Tace,
"To ki sani ba abinda zai sa na canja miki kinji. *Ni da aminiya* wato *Ja'adah da Sameerah* mutu ka raba takalmin kaza."
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...