133-134

797 50 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Wednesday
24/April/2019
133-134



Sau uku cikin daren nan tana farkawa da wani ciwo amman kuma sai ya lafa dan haka kan safiyya har ta dan rame ga bacci. Dan haka tana yin sallar asuba ta koma ta kwanta.

Da ya dawo yaga ta koma yai wanka ya shirya ya jima zaune ko zata tashi dan yasan ita ba ma'abociyar baccin safe bace. Ganin ba tashi zatai ba yasa ya sauka ya karya sannan ya dawo yadauki wayoyin sa da jakarsa. Zama yayi yai kissing forehead nata sannan ya mike ya fita yana jin kamar kar ya tafi. ba ita ta tashi ba sai karfe goma.

Wanka tayi ta sauko kasa. A falo ta samu Sameerah. Zama tayi da kyar tana rige da kugu. Junaid yayo gun ta yana fadin
"Mimah!"

Yadda yake kiran ta dan yana jin Sameerah na cewa Momah zaka na ce mata.

Daukar sa tayi ta ce,
"Dan gidan Mimah ka tashi lafiya? Ya Momahn ta ke?"

Ta kalli Sameerah ta ce,
"My Samee kin tashi lafiya?"

"Lafiya lou ya jiki jikin?"
"Alhamdulillah!"

Sallamar nurse suka jiyo suka amsa ta shigo bayan sun gaisa take cewa
"Ya jikin?"

"Alhamdulilah!"
"Ba abinda kike ji?"

"Eh!"
"To masha Allah zan wuce asibiti ne sai na dawo!"

"A dawo lafiya!"
Ta fita.

"Na miki masar na kawo miki?"
"Wow eh kawon, har naji yunwa ta kamani. Honey J ya tafi aikin ne?"

"Eh yace ai sai bacci kike!"
"Wallahi!"

Ta mike ta nufi kitchen ta kawo mata ai fa nan ta zauna tana ci tana bawa Junaid yana ci. Sai da suka ci suka koshi sannan suka zauna kallo.

Wayar ta ce tayi kara tana dubawa taga Jawad ne. Dagawa tayi tana fadin
"Honey J ka tashi lafiya? Ya aikin?"

"Alhamdulilah ya jikin?"
"Alhamdulilah!"

"Masha Allah ai nace bari na kira naji ko kin tashi."
"Na tashi har naci masar da My Samee tayi,"

"Ina sameerahn?"
Wayar ta mika suka waya ta bawa Junaid yana ta kiran sa da
"Abbi Abbi!"

Daga nan ya kashe waya. Sallar Azahar da akayi yasa ta mike ta hau sama. Alwala tai tayi sallah.

Tin da tai sallah ta kasa tashi a gun sai ciwo ya tayar mata. In tana daga zaune har ta kwanta tana mai zubar da gumi abin tausayi ita kadai da ciwon ya tsanta sai hawaye ko magana ta kasa bare ta iya mikewa ta kira Sameerah.

Sameerah dake daki taji zaman Ja'ada yai yawa sai ta mike ta nufi dakin nata duk da tana tunanin ko bacci ne ya dauke ta. A yadda ta ganta ba karamin ruduwa tayi ba da gudu ta kara sa gun ta can ta mike ta sauka kasa ta sa driver ya fitar da mota. Ta kira masu mata aiki aka kamo Ja'ada suka tafi asibiti.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora