*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Saturday
20/April/2019
123-124Daukar wayar yayi Mustapha ya ce,
"Gani nazo!""Ok ka shigo part din Ja'adatu gani nan!"
Ya kalle Ja'adatu ya ce,
"Mustapha yazo ya duba ki!""Me yake damu nah?"
Ta tambaya.Kallon ta yayi ya daura hannun sa ajikin ta ya ce,
"Zazzabi sannan kuma naga bakya iya tafiya ko? Sai kuma me?""Jiki na ke ciwo kawai."
"Kai wannan Honey J din duk shi ya janyo miki ko? Allah sai na zane shi.""A'ah!"
"Au kar na zane shi?"Kai ta gyada ya mike ya dauko mata hijab sannan ya dauke ta kamar Baby suka sauka kasa da ita.
A kan kujera ya ajiye ta ya kalli Mustapha ya ce,
"Sannu da zuwa!""Yauwah!"
"Ina Kwana?"Ja'ada ta fada kan ta a kasa.
"Lafiya lou Madam ya jikin?"Ya kafe ta da ido dan ganin me ke damun ta. Ta ce,
"Da sauki!"A kallon da yake mata ya gane a gajiye take, kuma jikin ta is so weak. Jawad ya kalla ya ce,
"Me yake damun ta ne?""Wallahi zazzabi ne fa, sai tafiya da takasa yi, sai ciwon jiki!"
"Dukka ita kadai?""Wallahi kadai bari."
Yanayin ta ya kalla ya ce,
"Daman bakya kya jin dadi ne?"Jawad ta kalla ta marairaice masa fuska dan ita bata san me zata ce ba. Shi kuma Jawad bai san ana jin haka ba dan bazai manta ba Sameerah bata yi duk haka ba duk da a budurwa ya sameta.
Kallon su yayi sun zubawa junan su ido dan ma Ja'ada nata da kunya a ciki da kuma marairaicewa.
Mustapha ya ce,
"Ah dole Muhammad ya mace akan Ja'ada ya gane ita macece mai shagwaba sannan kuma mai cika mutun da salon ta dan ita ba dole ne ma tasan tana wani abun ba kai da kake tare da ita kai zaka gane haka.Ji fa duk ya manta da wani shi a gun ma dan haka ya mike ya ce,
"Bari naje Muhammad zo muje ka karbo mata magani!"Maganar da yayi ita ta dawo da Jawad hankalin sa. Ya mike yabi bayan sa. Bayan ya mata kiss a goshi.
Mustapha ya ce,
"Madam Allah kara sauki kinji."Ta amsa da
"Ameen!"A waje suka tsaya Mustapha ya ce,
"Nifa ban gane me ke damun ta ba.""Wallahi Wai daga na je gun ta ne fa shine duk wadan nan abubuwan daman ana samun irin haka?"
"Kasan jiki-jiki ne wani aikin da zakai wani sai yaji shi bazai iya ba. And also ina jin baka bi da ita a hankali ba kayi zaton Sameerah ce wacce ta saba wannan kuwa kaga bata saba ba da yadda ya kamata ka tafiyar da ita."
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...