*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Wednesday
13/March/2019
97-98Suna zuwa gida a falo duk suka same su. Zama sukai duk sukai musu sannu da zuwa.
Momy ta fito daga daki tana kallon Dady.
Zama tayi suka gaisa da Abban Nusiaba sannan ta kalli Dady ta. Ce,
"Sannu da Zuwa Dadyn Jawad!""Yauwah ya gidan?"
"Alhamdulilah, sai dai duk muna cikin tsoro na kiran da kayiwa yara ina fatan ba wata matsala dai ko?""Ba wata matsala daman akan Muhammad ne!"
"Me ya samu Jawad din!"Ta tambaya hannun ta daure akan kirjin ta. Dady ne ya ce,
"Zaki iya tina shekaru bakwai zuwa tara baya ""Eh me ya faru?"
"Ki kwantar da hankalin ki.""Bazan iya ba Dady sai naji mai ya samu Jawad din!"
"Bafa abinda ya same shi.""Toh ina ji."
"Yauwah kin tina Time Din da sam bai son zaman guda da cin abincin gida in ki yi magana yace yaci a gidan wata yarinya har ki ta fada nace menene dan yaci kice kar su cutar da shi nace ai shima ba da cutarwa yaje musu ba dan haka baza su taba cutar dashi ba.""Eh Na tina Dady "
"Yauwah kin tina tafiyar sa kararu ""Na tina.!"
"Kin tina kwana ki da yazo mana da maganar yana son wata yarinya taki yadda dashi."Kai ta gyada. Abba ya basu labari tin hadiwar su da Ja'adatu da taimakon da yake mata da kuma tafiya karatu da tashin su Ja'ada da dawowar sa halin da ya shiga da wahalar da yake sha akan rashin ta har Yau din nan da yadda aka daura auren a yanzu kuma aka bada auren jikar sa ga Izeedeen.
Sosai suka tausayawa Sameerah da suka ji yadda ta tsaya tsayin daka. Sai dai suna mata addu'a Allah basu xaman lafiya, abu na biyu ku da yasa hankalin su ya dan kwanta akan sanin Ja'ada da sukai tin a haihuwar da Sameerah tayi sun lura da Ja'ada na da hankali nutsuwa da tarbiyya.
A take Mami taji Ja'ada ta shiga ran ta da yadda ta iya boye duk wannan abun dan samuwar farin cikin Kawar ta. Da wata kawar ce da duk hanyar da tasan zata bi dan ya sota ya aure ta zatayi bama da shi ma din yana son ta amman ta boye kuma shima ta hane sa da bayyanawa ya boye din.
Lallai Ja'ada kawar kirki ce wacce kowa zai so ta zamo kawar yar sa.
Ba abinda Zata ce sai addu'a Allah basu zaman lafiya da zuri'a daiyaba Allah ya hade kan su.Abinda ya kara mata dadi shine yadda Jawad ya amshi auren Sameerah bai nuna yana da wata yarinyar ba sai dan kawai ya faran ta ran iyayen sa. Hakika ya faran ta ransu kuma sun ji dadi shima Allah ya cigaba da faranta masa da bashi masu faranta masa. Allah ya hade kan ya'yan nasu.
Sameerah kuma ta cika ya ta gari mace mai albarka mai son farin cikin mijin ta lallai da wata macen ce ta gwammace ya mutu da ya kara mata aure. Auren ma da kawarta aminiyar ta.
Sosai kowa ya dinga juya abin a cikin ran sa. Nan dai kowa yasa albarka bama Mami.
Haka yayun Jawad ma duk addu'a suke. Take kuma Mami ta fara shirye shirye dan tace dole ko yar walima ce a hada bayan Jawad ya ji sauki.

ESTÁS LEYENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasíaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...