part 43-44

784 70 1
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Thursday
7/February/2019
43-44




*Bayan sati daya*

Duk wata addu'a Sameerah tayi kan Allah ya taimake ta akan abinda take son cikawa dan farin cikin mijin ta.

Dan yanzu addu'ar ta daga Allah ya daura mata dangana sai kuma Allah ya sa yarinyar ta yadda ko sa samu kwanciyar hankalin mijin ta.

A bangaren Ja'ada kuwa duk takurar da Jawad ke mata ta ishe ta. Ga Izzedeen har yanzu bata iya sakewa da shi dan sam zuciyar ta ba ta wani son sa.

Komai a cakude yake mata, abinda yake dada tada mata hankali shine taji ance, yau sauran kwana kaza bikin ta.

Duk yadda take so tayi aure ko ta gujewa Jawad kuma bata son auren.

Muhammad kuwa duk ya rame ya rasa nutsuwar sa da walwalar sa. Komai nasa sai a hhankali.

Addu'a ba wacce bayayi amman son Ja'ada kamar dada masa akeyi.


Kwance Ja'ada take a falo kan cinyar Mamah ta ji karar wayar ta.
dubawa tayi taga Sameerah ce.

Kirjin ta taji ya buga ta gyara kwanciyya sannan ta dauka,
"Assalamu Alaiku!"
"Wa'alaikum salam!"

"My Samee kina Lafiya?"
"Lafiya lou My Adat yasu Mamah da Abbah?"

"Kowa lafiya yasu Momy da Dad da Ur husband?"
"Duk lafiya Alhamdulilah!"

Sukai shiru can Sameerah ta ce,
"Kina kusa da Mamah ne?"

Kai ta gyada ta ce,
"Eh!"

"Ok Please give her the phone!"
Mika mata wayar Ja'ada tayi ta mike tayi daki.

Gaisawa sukai da Mamah sosai. Mamah na tambayar ta ya jiki jiki ta ce, Alhamdulilah.

Sai da suka gama gaishe gaishen sannan Sameerah ta ce,
"Mamah dan Allah alfarma nake nema!"

"Alfarmar me fa Sameerah!"
"Mamah dan Allah ina son My Adat tazo ta zauna min har na haihu!"

Murmushi Mamah tayi ta ce,
"Allah sameerah na zata waji abu ne, ba komai ai zan fadawa Abbah in ya dawo!"

"Nagode Mamah!"
"Ba komai!"

Dai dai karasowar Ja'ada wayar ta amsa tayi cikin daki. Sameerah ta ce,
"My Adat gidana nake so kizo ki zauna min har na haihu!"

A razane Ja'ada ta ce,
"Me?"

"Eh ai nasan kinji!"
Shiru Ja'ada tayi. Sameetah ta ce,
"Naji kinyu shiru ko bazaki zo bane?"

"Ba haka bane, kinga ina aiki ga shi biki na ya kusa."
"My Adat ko kina da aiki baki iya zuwa guna. Bayan nasan dis week zakuyi hutu bayan haka kuma aure ai ba ddaurawa akai ba tinda har yanzu kin karkashin iyayen ki ne. Ni nasan My Adat ta daina so na. Amman na riga na fadawa Mamah kuma ta ce zata fadawa Abbah kar na damu dan haka ki fara shiri."

Tana ggama fadar haka ta kashe wayar ta. Kwanciyya tayi tana fadin.
'Lahaula wala kuwta illa billahil aliyul azim!"

Ji take kirjin ta kamar zai rabe tayaya zata iya zaman gidan Sameerah ga Honey J a gidan.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now