93-94

577 42 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*


Monday
11/March/2019
93-94

Ta dawo lafiya kuma ta kwada ramar ta saka mata tumatur albasa da kuli a ido ma sai ta baka sha'awa bama mai ciki.

Da dare bayan magariba ta aikawa da Maman mu Kwadan Ramar nan. Ajiyewa tayi dan ta san Baban mu da son kwadan Rama. Haka yana dawowa ta mike masa duk da tana son taci amman ta ce taci rage masa tayi.

Sanin in dai bata ce haka ba to ba ci zai ba dan haka ta ce rage masa tayi.

Haka ya zauna yaci ya koshi. Sai da ya gama sannan yace
"Bilkisu a ina kika samu Rama?"

"Baba Rama ce ta bani!"
"Me?"

"Eh wallahi ta aikon da ita daxu!"
"Ya salam!"

"Menene?"
"Bilkisu kada ki kara cin abin hannun Baba Rama!"

"Saboda me?"
"Ni dai na fada miki."

Ya mike yayi dakin kakan mu. dan duba shi.

Maman mu kuma ta rasa dalilin meyasa ya ce, ta daina cin abinda ta bata.

Mikewa ita tayi ta bi bayan sa, a can ta tayashi suka gyarawa kakan mu kwanciyya sannan suka tafi dakin su.

Wanda duk dare sai Baban mu yaje gun Kakan mu ya duba shi fin sau uku dan ko zai bukaci abu.

Baba Rama kuwa tai ta zuba ido taji bayani amman, haka washe gari har da zuwa dakin Babar mu anan ta same ta tana ta aikin ta.

Haka ta juya da bacin rai, tin daga lokacin duk abinda Baba Rama ta bawa Babar mu sai ta ki ci.

Sai Baba Rama ta zata ko aikin beyi amman a haka sai kiyaya ta kara shiga tsakanin su, tsakanin ta kuwa da Kakan mu sai dai in Baban mu ya fito dashi da kakan mu sha iska ta ganshi ko kallo kuwa bai isar ta.

Haka sauran ya'yan ma in sun zo in sun ganshi a waje su gaishe shi dan ganin idon sa.  Amman in yana daki basa ko kallon dakin da yake.

A haka Baban mu da Babar mu suka cigaba da zama cikin rufin asiri da kaunar juna da taimakon juna sai dai in Baba Rama ta damesu da masifar su.

A haka har Babar mu ta haife ni. Mahaifin mu yaji dadi in da ya saka min suna baban kakar mu Dahir.

Tin ina jariri nake shan wahakar Baba Rama dan tana zaune dani zata aiki Babar mu ita kuma tai tayi min izaya ta duka sai dai Babar mu in taxo min wanka tai ta gani tabo a jikin na.

Bata tashi sanin me Baba Rama ke min ba sai lokacin da ina da wata biyar ta aiki Babar mu makwabta tin daga waje take jin ihun na wannan yasa ta shiga gidan da gudu dan ganin nake wa kuka.

Anan ta samu Baba Rama tana ta duka na ba tsoron Allah kome yaro dan wata biyar yai mata.

Tana ganin babar mu sai ta ce,
"Kinga yaro sai barna ke min ko?"

Daukar yaron tayi ta ce,
"Amman Baba Rama ai yaro ne!"

Tayi daki dani tana lallashi na. Kakan mu yana daki bai da bakin magana da ciwon barin jiki ya kama shi.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora