Part 25-26 (Haduwar Jawad da Sameerah)

846 87 3
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Sunday
13/January/2019
25-26

Haka yai ta rayuwa har ya shekara daya. A haka ya samu Lokacin Abokin sa Mustapha ya koma gida Nigeria.

Shi yaiwa kwatancen gidan su Ja'ada ya ce yaje ya kai mata waya sannan ya bada number sa.

Duk da haka Jawad duk ending month sai yai mata transfer kudi ta account din Ja'ada wanda ita sam bata daukar kudi ma.

Dan Atm din yana a ajiye a gida tana can boarding kuma aa harkar kasuwan cin Abbah ya bukasa. Ko ba haka ba Gidan su Sameerah *aminyar* ta su ke mata duk abinda zasu tafi ckul dashi.


A bangaren Ja'ada sai da tai ciwo sosai Saukar su ce ma da Sameerah suka sa ta dan karfafa jikin ta.

Anyi shagalin saukar su inda mai photo da vedio yazo ya musu wanda Jawad ya aiko mata.

A ranar sukai walimar makaranta wannan yasa ta ce sai washe gari zatai walimar ta.

Sosai mutane suka je mata har da yan gayar sodi dan anji kayan da take rabawa da kuma shigar da akace tayi suka je.

Ita da Sameerah sukai a gidan su Sameerah wanda Jawad ya bawa mai musu snack duk tayi komai kuma komai yayi cikin yaddar Allah.

Sosai Ja'ada ta samu kyaututuka a makaranta. sannan aka dauke su zasu na koyar wa a wasu ajikin. Asabar da lahadi da safe kuma zasu karasa haddar su wacce yanzu sukai izu arbain da wani abu.

Wasu yan ajin da za ai auren su ne yasa suka matsa akai sauka ba tare da an hada da ta yan hadda ba.

Sati Daya da sauka Dadyn Sameerah yai.musu duk abinda ya kamata na makaranta sannan suka tafi.

Ko a makaranta Ja'ada bata da magana sai akan Jawad. Honey J kaza Honey J kaza.

A makaranta sun hade kansu kamar yan biyi dan wasu twins suke ce musu ma.

Bame jin kan su basa fada dan Ja'ada akwai hakuri haka ma Samee.

Tasu ta zo daya sosai. Komai nasu daya. Baka gane cewa ba gidan su daya ba sai a suna.

Haka nan suna da kokari a cikin su sai ka rasa wa yafi wani kokari.

Wankin su kuwa Sameerah ita ke musu. Kullun suna tare basu da matsalar komai sai ta kewar gida.

Ita kuma Ja'ada sai ta kewar sahibin ta Honey J. Wanda ta sawa Sameerah son sa.

Dan in kaga Ja'ada na hira sosai to labarin Honey J din ta take bayar wa.

In kuwa son ya motsa mata sai tai ta kuka dan ita kadai tasan me take ji. Ji take kamar tai tsuntsuwa taje gun sa.

In Sameerah ta same ta tana kuka har taya ta take. Sameerah bata san so ba amman ta dalilin kawar ta *aminyar* ta yasa ta san yadda yake dan tasan Ja'ada da kawai ci akan abu abinda yasa ta kuka kuwa babba ne.

A haka suka cinye term daya suka dawo gida. Kowa na murna har da Ja'ada amman in ta tuna ba Honey J sai hankalin ta ya tashi.

A haka suka gama hutu aminci sosai ya kullu tsakanin Ja'ada da Samee. Ita ta ce,
"My Adat. "

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Onde histórias criam vida. Descubra agora