*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Friday
19/April/2019
121-122Karba tayi ta daga rigar don taga yaya girman rigar take, sai ta ganta bata fi ta tsaya a iya cinyar ta ba. Gata transparent komai na jikin mutun sai an gani pink kala ce. ji tayi gaban ta ya fadi saboda a gaskiya tana jin nauyi da kunyar Honey J yaya za ayi ta iya sa wannan 'yar rigar agabansa.
Tana son Honey J matukar amma bata jin zata iya gashi duk taga ya canja mata a yanzu yanzun nan.
Tunani ta zauna yi ta rasa ta yaya zata saka rigar shi ya ce
"Tashi ki saka ko inzo in taya ne?"Da sauri ta ce,
"A'a!"Ta mike ta tafi can lungun gado ta fara cire doguwar rigar sai ta tjna da Honey J da ke zaune akan kujerar dake dakin.
Idon sa na tsaye a kanta kem, ta juyo ta dubeshi taga ita yake kallo sai ta dauki rigar baccin ta nufi bandaki.Honey J yace,
"ina zaki kuma?"Cikin kunya kanta a kasa tace
"bandaki zanje in canja."Ya bude baki zaiyi magana tai saurin fadawa bandakin.
Tana shiga wanka tayi ta wanke bakin ta sannan ta tsane jikin ta ta sako rigar baccin nata.Ta yafa mayafin jikin ta ta fito ba kowa a dakin wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya. Ta zauna ta dan yi shafe shafen ta sannan ta jika jikin ta da turaruka masu dadin kamshi.
Tana zaune taji bude kofar sa ya shigo, ta tsorata taja da baya.
Yana tsaye a bakin kofa hannun sa dauke da wasu manyan ledoji guda biyu, ya kura mata ido yana yi mata murmushi ya tura kofar dakin ya nufo inda take zaune a hankali ya Mikar da ita.
Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce,
"Taho kici kazar amarcin ki da kowa ke ci a ranar auren sa."Kai ta girgiza ta ce,
"Na koshi.""Ba wani nan."
Ya bude gashin kajin da suka ji hadi da dankali da su albasa da kayan kamshi sai kamshi ke tashi.Da kansa ya dinga bata kadan taci ta ce ta koshi. wani jug ya dauko ya bude ya zuba mata a cikin kofi ya kai bakin ta. Amsa tayi ta kurba ta ji ashe fruits ne aka markada aka zuba masa madara. Wannan tasha da yawa sannan ta kau da kai.
Zama yayi ya ci bayan ya fita mayar da kayan ta shiga bandaki ta wanke bakin ta. Shima dakin sa yaje ya wanke bakinsa sannan ya dawo dakin nata. A tsaye ya ganta zata dauki mayafin ta ya shigo dakin wannan yasa ta kasa karasa ga mayafin tayi tsaye kawai. Kallon ta ya ke yi cikin so da kauna da sha'awa a hankali ya karasa in da take a tsaye.
Hannu Biyu yasa ya jawota kan kirjinsa ya rungume ta tsam yayin da dukkan su. zuciyoyin su suka hau bugawa a lokaci daya kowannen su yana jin yadda ta dan uwansa take bugawa don tsananin farin cikin da suka tsinci kansu a wannan lokacin.Ko wannen su kwakwalwarsa na kokarin tatantance masa shin da gaske ne ko kuwa mafarki sukeyi. Ja'ada ta dago da kanta a hankali ta kalli Honey J don ta tabbatar shi din ne kuwan ko mafarkin da ta saba ne. Ai kam dai dai lokacin shima ya dago yana kallonta don shima ya tantance gaske ne ko mafarki yake irin wanda ya saba
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...