part 49-50

797 70 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Sunday
10/February/2019
49-50


Yana kwance yake magana shi kadai,
"Dole akan Sameerah ba zan rasa My Ja'adatu ba dole na rushe baikon da akai mata dole na wanke kai na dan ta cire zargin yaudarar ta nake dole na tabbatar mata da son da nake mata. Amman duk wannan wa zai taimaka min?"

Ya dan yi shiru zuwa can ya ce,
"My wife kdai zata taimaka min dan haka dole na sanar da. my wife abinda yake akwai."

Ranar da bai bacci ba haka ya kwana surutai daga baya ya mike ya shiga toilet yai alwala yazo ya kai kukan sa ga Allah maji rokan bayin da.

Sameerah ma batai bacci ba damuwa biyu ta hadar mata dan ta tabbata akawai abinda Ja'ada ke boye mata, amman dai zata kara gwada ta ta gani.

Sai kuma damuwar mijin ta haka ta kwana juyi ga jego ba abin ta tashi tai sallah takai kukan ta ga Allah ba. Amman duk da haka tana kwance sai addu'a take a cikin ranta.

Ja'ada kuwa ganin ba baccin zatai ba ya sa ta mike ta dauro alwalan ta hau kan sallayar ta nan tai ta sallah tana kai kukan ta ga Allah.

Har asuba tana kan sallaya sai da aka kira sannan ta mike tai sallah ta kuma fita gyaran gidan.

Kan karfe bakwai ta gama gyara gidan gaba daya sai tashin kamshin turaren wuta yake haka nan Dakin me jego sai kamshin turaren wuta yake da kamshin jego gadon nan ta shimfida masa zanin gado mai kyau.

Samerrah tana can ana mata wanka Momy na wa Baby. Ta gama ta shirya shi tsaf sannan ta kwantar da shi dan har yai wanka.

Ja'ada kuwa tana can kitchen tana ta hada hadar hada abincin ssafe.

Bayan sameerah ta fito ta shafa mai ta gyara jikin ta ta saka wata atamfa mai ruwan ganye da yellow da ja ba karamin kyau tayi ba.

Nan ta bade jikin ta da kamshin turare. Tana zaune Momy ta kawo mata kunun gyada da Ja'ada ta damo mata, da farfesun kayan ciki.

Fulas din dankali da kwai da na ruwan tea ta dauka a babban fulas dan kai wa mai jego dakin ta.

Tana direwa ta kalli Sameerah da tai ci ado sai kace amarya ta ce,
"Kaga uwar gida amarya kuma a gidan Honey M!"

Dariya Sameerah tayi ta ce,
"A'ah ce dai uwar gidan ni da na kusa amsar kanwa."

'Ke ba wata kanwa Honey M naki ne ke kadai!"
"Da hakan zai faru zan ji dadi, amman yanzu ma alhamdulilah tin da har nasan ina da matsayi gun hobey M kuma Allah yasa raya sunna zzai yi da ace an kamashi wajen wata fa. Ai gwara ya kawon uku har da kwarkwara."

Dariya Ja'ada tayi ta ce,
"Allah ya kara gyara zuciyar ki!"

"Ameen kema!"
"Ameen amman kin dai san ni da kishi ai!"

Tayi kofa zata fita taji kamshin turaren wannan yasa ta dan koma ciki da zumar abu zata dauka.

Yana tsaye a bakin kofa yana jin su yaso Ja'ada ta fito ya fara ganin ta amman kuma bata fito ba wannan yasa ya shigo.

Idon sa akan ta ya fara tozali duk da tin wankan asuba da tayi kuma ko mai bata shafa ba tana sanye dda bakar doguwar riga tayi rolling kanta da bakin mayafi.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now