part 57-58

747 56 3
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Thursday
14/February/2019
57-58



Tin ranar Jawad bai kara zuwa gidan ba. A bangaren Ja'ada taji dadi bata ji dadi ba. Dan ko ba komai tana son ganin sa ta samu sanyi a zuciyar ta. Jin dadin ta kuma na ta samu bai zo ba bare ya tadawa aminiyar tata hankali. Duk da taga kawar tata bata ji dadi na dauke musu kafa da yayi ba.

Ga Anty Rukayya ta ce a tambayo musu sunan yarinya da yake so zata je gun malamin nata. Ga ba Jawad ba alamun sa.

Yau Izeedeen zai zo Sameerah da ba gun ta zai zo ba ma tafi dauki da shirye shiryen zuwan sa. Dan duk ta raba ai musu kayan tarbar sa.

Haka nan a cikin kayan da Honey M ya kawo wa Ja'ada ta dauki wani less ta bayar an dinko mata, ta tana hada mata duk abinda take bukata.

Karfe hudu dai dai ta fito daga wanka mai ta shafa ta zira dinkin da akai mata na doguwar riga mai A shape tai mata kyau ta zauna a jikin ta kasancewar ta fara kayan sun amshe ta dan baki da adon pink kala ne.

Hoda kawai ta shafa ta mike dai dai lokacin Sameerah ta shigo. Kallon ta tayi ta ce,
"Kai amman kinyi kyau Allah sai nai miki kwalliya.

Fuska ta bata ta ce,
"Kiyi ma kuka amman sai na miki."

Nan ta zauna tta fara mata kwalliya. Suna gama kwalliyar dan simple tai mata za ta farai mata dauri kenan sai ga sallamar Jawad nan.

Gashin Ja'ada dake kwance a gadon bayan ta ta nade mata tana amsa sallamar sa.

Kallon su ya tsaya yi ba karamin burge shi sukai ba. bai kara sakin baki ba sai da ta gamai wa Ja'ada dauri ta dago dan adukar wayar ta da take ta kara.

Izeedeen ne.
"Hello"

"Ok gani nan!"
Ta fada. Mayafi Sameerah ta miko mata sannan tadauki turare ta farai mata barin sa.

Jawad da ya kasa motsi daga inda yake zaune ya ce,
"Ina zuwa ne?"

Samereah ce ta ce,
"Angon ta ne yazo!"

Dam yaji kirjin sa ya buga na jin abinda Sameerah ta fada. Murmushi Ja'ada tayi ta ce,
"Bari naje!"

tayi waje. sai da ta fita sannan sameerah ta kalle shi ta Zauna.
"My samee fushi kike dani?"

"Akan me zanyi fushi da kai me kayi min!"
Murmushi yayi ya ce,

"Kiyi hakuri to gani ai. Ki daina bata ran ki."
"Ai kai kullum burin ka rai na ya baci. To menene na ban hakuri. Kai zan bawa hakuri da nake son saka damuwar ka a cikin rayuwa ta bayan ni baka damu dani ba."

Mikewa yayi ya karaso gun ta ce,
"Ki daina fadin haka zaki ssa na kara shiga wani halin."

Zama yayi a kusa da ita ya janyo ta jikin sa. Ta langwabe ajikin sa. Ya ce,
"Ke matace ta gari ce kuma na yadda dake na kuma aminta da ke shiyasa bana iya boye miki komai ki godewa Allah da kuma da bana boye miki, da na boye miki nake baki san halin da nake ciki ba da ki ji yaya kenan."

"Haka ne, nima ina godiya da Allah da ya bani kai mijina mai fadan sirrin sa nagode."
"Allah miki albarka."

"Ameen!"
Can sai ta dago ta ce,
"Ya suna ta ne?"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora